*MUGUN NUFI*
_(Baya kashe ɗan_ _barewa)_PAID BOOK
*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى* *ASSɷ* 📚✍*
_{Onward Together}__STORY AND WRITTEN_
_BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////FREE PAGE
🅿️:7️⃣
Hankali kwance Meemerh ta ci macaroni jallof dinta, ta na gamawa ta sauya kayan jikin ta, ta fito don tafiya gidan su Suhaima, dama a rayuwar ta gida biyu ta sani idan har baka sameta a gidansu ba to fa ba za ta wuce gidan su Suhaima ba, dangin Abie babu inda ta ke zuwa duk da matar Baba Yahuza batada matsala kuma tana kokarin janta a jikin ta, ita ce dai bata da sakewa domin duk duniya daga Abie se Suhaima ne ta yarda bazasu taba cin zarafin ta ba.
A falo ta samu Abie tare da Dada, ganin yanayin zaman su kawai seda ya haddasa mata faduwar gaba, dan jikin ta yana bata ba maganar arziki ne Dada ta fadawa Abie ba ganin damuwa shinfide a fuskarsa, ita kuma fuskarnan a murtuke sam babu alamar daria, wurin Abie ta isa ta dan rage tsawon ta kadan ta re da fadin, " Abie zan je gidan su Suhaima" kai kawai ya ɗaga mata alamun se ta dawo, ba ta ko kalli inda Daada ta ke ba ta nufi hanyar ficewa. Da Karfi Dada ta janyo gyalen rigarta, wanda ba dan Allah ya tsare ba da babu abuna ze hanata faduwa, dan dai ta yi saurin dafa kujera ne, juyowa ta yi rai a bace tana yi mata wani irin kallo me wuyar fassara kai tsaye ba zaka ce hararanta take ba, haka kuma ba kallon arziki bane, hakan yana da alaka da rashin bayyanar da fushi irin na Meemerh Kuma wannan halayyar na ta ke kara hassala su Baba Musa, domin so tari xasuyi abu dan ranta ya ɓaci amma sam bata basu ,damar fahimtar hakan .
" Ke ko uwarki ta yi kaɗan ta raɓani ta wuce ba tare da gaisuwa ba bare ke, ƴar banza gadon marasa mutumci da tarbiyya, a duk jikokiña ke ce kika fita Zakka kamar yadda uwarki ta fita Zakka a matan ƴaƴana" Runtse ido Meemerh ta yi don sosai yau kam zuciyarta ke ta fasa da kalaman Dada, wacce a kullum burinta, ta ga ta tozartar da ita, idan ba haka ba ina hadin kifi da kaska, miye ta ke alakanta ta da matar da ba ƙaunarta takeyi ba.
Tabbas yau ba dan ganin idon Abie ba da ta yi maganin jarababbiyar matar nan, saidai ko an raina ɗan tsun tsu baxe ciyu da gashi ba, zata ƙyaleta saboda Abie, idan kifi da zabo na yawo dole watarana za'a haɗu, buɗe idon ta tayi ta sanya su cikin na Dada, da sauri kuwa ta saki mayafin da ta rike a hannunta, don ganin mugun jan da ke cikin idon, kakkaɓe gyalen Meemerh tayi bata ce komai ba ta ficewarta.
Aikam se tijarar Dada ya dawo kan Abie " yanzu Ahmadu a gaban idon ka wannan yarinyar ta wulkantani amma ka kasa cimin uwarta, ko a jikin ka ma, kamar abun daɗi yayi maka tunda ga ka a zaune kana kallon mu ko tari ka kasayi, anya uwar yarinyar nan a haka ta bar min kai kuwa, ko dai tayi maka wani surƙullen ne shiyasa baka ganin kowa se ƴarta, ita kan ta ba ka so a tayar da labarin ta, kuma abinda ka san baze yiyu bane dan wallahi se mun faɗa, da ma ance idan mutum ya mutu abun da ake faɗa a kan sa shi ne ze bisa to na fi son ayita wa Adizatou azaba dai dai gwargwadon cin amanar da tayi mana..." Haba Dada be kamata kina irin wannan maganar ba ki sani ita rahamar Ubangiji idan ya so ka da ita to komai girman abun da ka aikata se ta shafeshi, ko da tana raye ko kuma ta mutu, ina roka mata rahamar Ubangiji, domin nine mijinta kuma na fi kowa sanin wacece ita, na yi mata hukuncine kawai a bisa umurnin ki, amma sam bata ci amanata ba, kuma bazan gushe ina rokon Allah ya bayyanar da gaskiya ba" rike baki Dada ta yi tsabar mamakin yau Abie ne da kan sa ke maida mata magana wanda ko cikin yan uwansa ƙarya ne su faɗa ya faɗa ,fashe wa tayi da kuka, wai Abie ya ci mutuncin ta, sosai hankalin sa ya ta shi don ya san hawayenta bala'i ne a gareshi, rarrashin ta ya hau yi, da ƙyar ta hakura ya rakata har sashen ta.Ga damuwa ga ɓacin rai haka abubuwa suka taru sukayiwa Meemerh yawa, driving kawai ta keyi amma sam zuciyarta babu daɗi, a dai dai wani junction motar ta ta kufce saura kaɗan ta bugi wata mota da ta zo da gudu ita zata shiga shikuma ze fito, da sauri ta samu ta ci burki fito wa ta yi dan ganin me motar ya yi parking rai a bace ya nufo ta " ke wace irin mara hankali ce zakizo kina driving din ganganci idan koyon driving kikeyi me yasa zaki zo babbar hanya a cikin unguwa ya kamata ki koya, wallahi da kinyi min asara da se kin biyani dan bazan ɗauka ba, sakarya kawai,Mtssswww" ya yi tsaki ta re da juyawa ze tafi " kayi hakuri dan Allah wallahi ba koyo nakeyi ba, kawai dai tsautsayi ne, ka san yau da gobe kuma Alhamdulillah tun da Allah ya tsare ma babu abunda ya faru" juyowa yayi dan ganin wace yarinya ce wannan, duk rashin mutuncin nan da ya shuka mata amma take bashi hakuri cikin sanyi murya, idon ta a kasa tana sharar hawaye, duk da be wani ga fuskanta ta sosai ba amma jikin sa yayi sanyi se ya ga duk be kyauta ba, tunda shima da lefinsa gudun da yake yi ya zarta hankali, sosai yarinyar ta ba shi tausayi, matsowa yayi kusa da inda take ya dauki wayar ta da ta suɓuce a hannunta lokacin da yayi mata tsawa mika mata yayi, cikin sanyi murya sabanin ɗazu yace " kiyi hakuri dan Allah ba ina nufin yi miki faɗa bane, raina ne a bace"
Jin maganar sa ta sauya se ta ɗago kai ta kalleshi, watabarakallahu fili ahsanul khalikin, abinda ya furta kenan cikin zuciyarsa domin kyan yarinyar ya buge zuciyarsa, ga dararan idanunta da hawaye suka kwanta a ciki, se ya karawa idon haske da ƙyalli, girgiza masa kai tayi tare da fadar " ka yawaita istigifari a duk lokacin da ka kasance cikin ɓacin rai, domin fushi ma kulli ne na sharri, ka ga yanzu ma shine ya rinjayi zuciyarki, ni ma ba'a son raina nayi ba motar ne ta ƙwace min, kayi hakuri pls".
Sam baya fahimtar yarenta se ƴan laɓbanta da ya tsurawa ido, wanda idan ba ya na kusa da ita sosai ba ya tabbatar bazeji abun da take faɗa ba, yanayin da take motsa laɓbanta sam bazakace magana take yi ba, tashin motar ta ne ya dawo da shi daga duniyar saƙaƙurai da ya tafi na wuccen gadi, hannun sa ya kalla yaga wayar da yake miƙa mata ashe bata karba ba da alama ita ma ta manta ne, da sauri ya kalli hanyar se dai wayam babu alamun ƙurar motar ta ma, da sauri ya shiga motar sa , reverse ya yi ya bi bayanta ko ze ganta domin ya bata wayar se dai ko alamun ta be gani ba, dan haka ya hakura tunda ya san dole zata nemi wayarta idan ta kira se ya sameta gidan su ya kai mata........
To fa wa kuke tunani wannan gayen?
Ku biya kudin ku domin Kusha shagali ku💃
₦300 only
Comment and share pls
#Real@Bazamfaria💋ention a user
YOU ARE READING
MUGUN NUFI
Mystery / ThrillerSoyayyar uwa soyayya ce da ake haifar ƴaƴa da ita, musamman ma ƴaƴa mata, sedai wannan ya sha banban da rayuwar Meemerh, a duniya babu wacce ta tsana kamar mahaifiyarta, bata tashi tare da ita ba amma ko yaushe addu'ar ta da fatan ta ko a mafalki ka...