5

1 0 0
                                    

*MUGUN NUFI*
     _(Baya kashe ɗan_ _barewa)_

PAID BOOK

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى*  *ASSɷ* 📚✍*
  _{Onward Together}_

_STORY AND WRITTEN_
                  _BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////

FREE PAGE

🅿️:5️⃣

*Kindly Make ur payment through my bank account 👉* *0034847179*
*Fiddausi sani*
*Stanbic bank*
*And send ur evidence* *Via my* *Watsap number 08036879073*
*Is ₦300 only*


Misalin ƙarfe tara 9 na dare Meemerh ta yi shirin kwanciyar ta, har ta kwanta se kuma ta ji tana son kunna wayarta da ta ke a kashe tsawon wasu kwanaki, neman wayar ta fara yi dan bata da tabbacin inda ta ajiyeta, cikin sa'a ta ganta cikin bedside drower, ɗaukowa ta yi ta dawo kan gadon ta ta kwanta, kamar jira ake ta kunna wayar saƙwanni suka fara shigowa, duk da bata riga da ta duba ba ta san ba zai wuce Mujahid ba, saboda haka bata ma bi ta kansu ba kawai sai ta kunna data, a nan ma dai zancen ɗaya ne domin messages ne birjik ke shigowa musamman na groups ɗin school, privet message guda huɗu 4 ne kawai, ɗaya Mujahid ne da akwatin sakonnin ya nuna mata adadin messages din da ya turo har guda ashirin da biyar 25, sai sauran na ƙawayenta guda biyu, sai ɗaya na Mudassir (yaron Baba Musa).

Ganin yana online ne ya sa sai ta buɗe saƙon shi, murmushi kawai ta yi a yayin da ta ga abun da ya rubuto mata, ganin bata da abun ce masa sai kawai ta tura masa sticker ta fito,  har zata kashe data sai ga saƙo ya shigo mata da baƙuwar numbern, tana buɗewa sai taga an ce,
"Hey Wifey da wa ki ke chat a wannan lokacin bayan kin san yanzu ke matar aure ce?"
Cike da mamakin sakon ta ke sake karanta shi, bata gama mamaki ba ya sake turo mata da wani.
"Ban taɓa jin labari me daɗi ba kamar na samun ki da na yi a matsayin matar aurena, da ma na faɗa miki cewar ke rabona ce, kar ki damu da tunanin ya aka yi ki ka zo duniya na san dai tsoron da ki ke yi kenan, to ki sani ni ke ɗin dai nake so, ki fito gani a falo ina jiranki."

Tunda ta ji wannan kalaman ta gane cewar Bashir ne, duba agogon wayarta ta yi ta ga kusan ƙarfe 10 ake magana, dan haka bata ce dashi komai ba ta kashe data, ta yi kwanciyar ta.

Bashir da ke zaune a falo ya ci gayu sosai cikin ƙananan kaya, dan shima ba'a baya ba Indai ta fannin gayu ne, duk da kasancewar shi baƙin mutum ga shi ba wani kyau ne da shi ba, domin shi kana ganin sa za ka san cewar familyn DURUMBU ne, kasancewar zuri'ar idan har kaga wani jika nasu da hasken fata, to tabbas se idan daga uwarsa ya gado, duka iyayen su maza baƙake ne masu ɗan hasken cikin su ma su ne Abie da kuma Baba Auwalu su ne su ke ɗan da kyau a cikin su.
Shi kuma Bashir photo copy ne na kakansu, shi ya sa kusan ya fi kowa baki a familyn. Time to time yake duba wristwatch ɗinsa ganin lokaci na tafiya amma bai ga alamun Meemerh za ta fito ba, da ya ji motsi sai ya kalli ƙofa amma shiru, har ƙarfe goma sha ɗaya 11:10 ta yi yana nan zaune, jin kamar motsin tafiya ne yasa ya sake gyara zama a tunanin sa ko Meemerh ce, sai dai ya yi rashin sa'ar ganin Abie cikin farar jalabiya hannun sa riƙe da carbi.

Kallon Mamaki Abie yake yi masa, kafin ya ce,
"Bashir me ka ke yi anan kusan ƙarfe sha ɗaya 11 na dare? Na fito ne in rufe ƙofar falo fa."

Sosa kai ya fara, kamar mutumin kirki ya ce,
"Baba wallahi ban san lokaci ya tafi ba haka, tun ɗazu nake jiran Meemerh amma bata fito ba."

"Ta san da zuwanka?"
Abie ya jefa masa tambaya.

"Ehhhh na sanar da ita." ya bashi amsa a taƙaice.

"To ka ga yanzu haka ba mamaki ta manta shirmen Mamana kenan, kuma yanzu na san ta yi bacci, ka tafi gobe sai ka dawo ka ji?"

Ba dan ya so ba dole ya amsa da
"To Baba, sai da safe."

MUGUN NUFI Where stories live. Discover now