page 6

0 0 0
                                    

*MUGUN NUFI*
     _(Baya kashe ɗan_ _barewa)_

PAID BOOK

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى*  *ASSɷ* 📚✍*
  _{Onward Together}_

_STORY AND WRITTEN_
                  _BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////

FREE PAGE

🅿️:6️⃣

*Kindly Make ur payment through my bank account 👉* *0034847179*
*Fiddausi sani*
*Stanbic bank*
*And send ur evidence via* *my Watsap number*
     *08039228702*

Sosai Hajiya Hadiza ta sha jinin jikin ta dan ba ƙaramar nadamar shiga sabgar Meemerh tayi ba, sauƙin ta ma ba'a gaban Hajia A'isha bane ta san da abun ya fi muni.

#Bashir

Tun da safe da ya fe sa uban wankan sa abun ka da ɗan gaye ko breakfast be jira ba ya doshi gidan su Meemerh domin zuwa kamun kafa wurin Hajiya Dada. A falon ta ya sameta ta na zaune tana karyawa, domin ita al'adarta tunda safe take cin abinci a cewar ta yafi saka lafiya. Jin shigowar mutum ya sakata ɗaga ido dan ganin ko waye, da mamaki ta ce, " kai ne da uwar safiyar nan se ko na ci maka ba shi ne?".

Sosa kan sa ya yi yana murmushi tare da fadin, " ai dai kya bari mu gaisa kafin ki fara tambayoyin nan da ba sa ƙarewa, to miye ma dan ka zo ka duba lafiyar matar ka har se an wani tuhumeka? Ya faɗa da sigar wasa.

Hararan sa ta yi ta ce, se yau ne ka zo duba ni ina har zazzaɓi na yi kwanakin nan amma ba ka zo ba" Kinga yanzu ai shiyasa na zo dan na goge lefina" ko dai wani abun ya kawo ka ba" dariya yayi dan ganin ta harbo jirgin sa.

"Yanzu dai Dada ki ga ma karyawa a tsanake wata magana na ke so zamuyi" ganin babu alamun wasa a fuskan shi se ta tattara karin kumullon ta aje a gefe maida hankalinta ta yi wurin sa " to ina jin ka Basiru" cikin sanyi murya kamar wani kamilalle ya fara kora mata bayani cike da magiya ya ce, " Dada na san a lokacin baya nayi shiririta amma a yanzu Allah ya shiryeni shiyasa ma na yanke shawarar zanyi aure, kin san shi aure yana ƙarawa mutum kamala.." ba ta ko bari ya ƙarasa ba ta washe baki " Masha'Allah Alhamdulillah, Lallai kam ka shiryu Basiru tunda har tunanin aure ya zo kanka, to wace yarinyar ka sa mo mana Allah ya sa dai yar gidan su masu tarbiyya ce, dan an shani sau ɗaya bazan yarda ayi na biyu ba".

Murmushi Bashir ya yi ya ce, "Dada wannan ban da matsala dan ba kowa ba ce fa ce ƴar'uwata, Kinga za'ayi tuwona maina kenan baki da fargabar tarbiyyar ta" ƙara washe baki ta yi tana gyara zama " to ina jin ka Bashir Nusaiba ko yasira?

" A'a Hajia Dada waƴannan yaran ai basa da kunya kuma ma yaushe suka isa aure? To nide su kaɗai na sani matan da suke ɗan da girma a dangin nan ana wacce kake magana? To mutuniyar ki na ke so Meemerh..." Meemerh kai kam me ya ja ka zuwa ga wannan yarinyar ko ɗan jan fatan da take da shi da ƙwalakwalan ido kamar ƴar Mayu shine ya ruɗeka? Haɗe fuska Bashir yayi " nide Hajiya Dada bana so a haka ba ganta kuma na ke son auren ta idan kuma bazaki bani ita bane in sani"

" Haba Bashir ko da kake gantalelle ai babu wanda ze hanaka wannan jihadin, kana ganin kowa yaki auren ta, tunda har kai ka ji ka kuma gani ai shikenan Allah ya zaunar da ku lafiya" washe baki Bashir yayi jin ya samu goyon bayan Dada " amma Dada wani hanzari ba gudu ba, ina ga Baba Ahmad din kamar baya sona da yarinyar, dan jiya ma na zo gunta amma wallahi ya hanani ganin ta" Cike da Mamaki Dada ta ce, " shi Amadun ne yayi maka haka? Ina lefin wanda ya nuna yana son ƴarsa, wacce waje taki ɗauka, to ka barni da shi jeka ka fara shirin aure ni na baka ita kuma aure za'ayi babu fashi dan bansan uwar me zata ci gaba da yi a gidan nan ba tunda kai har kaji zakayi jihadi. " Laluben wayarta ta fara miƙa wa Bashir tayi " kira min lambar Amadu"

Sanin ba ya da gaskiya da sauri ya ce, " a'a Dada kar ya ce na kawo ƙaran shi ne, ina ga kawai ki kirashi daga baya se ki sanar da shi kin yanke hukuncin haɗani da Meemerh kinga shikenan babu wanda ze zargeni" jin abinda ya faɗa sai ta mai da wayar ta ajiye.

#Meemerh

Ko da ta koma ɗakinta, ta faɗa kan gado tana sauke ajiyar zuciya, ta san ba ƙaramin dakiya ta yi wurin maidawa Hajiya Hadiza da magana ba, tabbas Suhaima ta yi gaskiya ta sha faɗa ma ta cewar shirun da ta keyi ne ya saka sukeyi mata cin kashi, kuma ta tabbatar a yau ɗin nan duba da yadda Hajiya Hadiza sarkin taƙama ta daburce, duk da ba ta so abinda ta yi mata ba ko ba komai ita matar Abie ce ya kamata ta girmamata.

Tana nan a kwance har Baba ta gama girkin ta kawo mata, sannu da aiki tayi mata tukuna ta tashi ta zauna ta fara cin abincinta.

#Abdul-Khabeer
Kamar yadda ya yi zaton dalilin zuwan iyayensa Kd hakan ne ya tabbata kuwa, domin dirar safe sukayiwa gidan Kanka su Papi, bisa ta kurawar Auntynsa, domin ba dan ita ba da ba zuwa xeyi ba, tun da suka shiga gidan ya ɗaure fuska, duk wasar da Hajjo (kakarsa) keyi masa be saki fuska ba.

Bayan gaishe gaishe Papi yayi gyaran murya " kamar yadda kuka sani na sha baku lokacin akan ku saka ɗanku yayi aure amma kukayi biris da maganata, saboda ɗan so ne shi se abinda yace kukeyi, Khadijah duk nafi ɗora wannan lefin akan ki domin kece kike ɗaure masa gindi ace kamar Abdul-khabeer Sa'anninsa nawa ne ke da yara amma shi ko maganar auren ma ba ya so idan lafiya ne bayada se ya faɗa mana mu nema masa magani"
    Duƙar da kai Aunty tayi cikeda biyayya tace " Allah ya huci zuciyar Papi, ba wai ina ɗaure masa bane na yi masa uzuri ne saboda na san aure lokaci ne idan lokaci yayi komai rashin son sa dole xeyi..." Dakatar da ita Papi ya yi ta hanyar fadar, " aiko ga lokacin nan Ubangiji ya kawo mu don kuwa ina me tabbatar miki da na gama maganar auren sa na nema masa matar aure da kaina don na fahimci shi tsoron matan yakeyi ko kuma tashi auren ne beyi ba".

Kamar saukar aradu haka ya ji maganar Papi a kunnen sa tabbas idan Papi ya ce Ehhh to ta tabbata babu fashi tsohon yana da kafiya akan abu, to ya kenan da gaske ya sama masa matar auren wace iri ce zubinta da tsarin ta na irin wacce ya ke so ne ko kuwa, sosai hankalin sa yayi tashin gauron zabbi, gefen Aunty ya kalla cikin sa'a suka haɗa ido, alamun rarrashi tayi masa da ido kawar da kansa yayi gefe dan ba ma ze iya furta komai ba.

" Ya na ji duk kunyi wani shiru ko hukuncina be yi muku bane, ko kuma saboda na taɓa ɗan so ne? Haba Papi da mu da Abdul-khabeer ai duk mallakin ka ne komu ba mu wuce kayi mana zabi ba bare kuma shi, Allah Ubangiji ya tabbatar da Alkhairi " Phrm Abas ya faɗa cikin ladabi
     " Ameen Ameen, dama dalilin neman da nakeyi muki kenan ko da kun kwana biyu ma baku shigo Kd ba, ban san me yasa baku son zama garin nan ba" jin ze ɓallo wani zancen se Phrm Abas yayi saurin kawar da maganar ta hanyar janyo wani labarin, Aunty dai hankalin ta na kan danta, don ita ka ɗai ce zata fahimci halin da yake ciki domin ita ta san wanene khabeer ta san irin macen da yake da burin aura tsoron ta ɗaya kar macen da Papi ya zaɓa masa ya kasance ba batayi masa ba, ita ma dai cikin zuciyar ta alkhairin Ubangiji ta roka akan wannan al'amari.

Comment and share pls

#Real@Bazamfaria💞

MUGUN NUFI Where stories live. Discover now