page 4

1 0 0
                                    

*MUGUN NUFI*
     _(Baya kashe ɗan_ _barewa)_

PAID BOOK

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى*  *ASSɷ* 📚✍*
  _{Onward Together}_

_STORY AND WRITTEN_
                  _BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////

FREE PAGE

🅿️:4️⃣

*Kindly Make ur payment through my bank account 👉* *0034847179*
*Fiddausi sani*
*Stanbic bank*
*And send ur evidence* *Via my* *Watsap number 08039228702*
*Is 300 only*

_________Abdul khabeer
Ɗa ne a wurin pharm Abas, su uku ne Ubangiji ya wadata iyayen sa da haihuwa, shi da ya ke da shekara talatin da ɗaya 31 a duniya se ƙannensa guda biyu ƴan mata waƴan da su ka kasance tagwaye ne Hassana da Usaina, suna da shekaru goma sha biyar 15 da haihuwa, akwai tazara sosai a tsakanin su da yayan na su. Mahaifinsu pharmacist ne yayin da ita kuma mahaifiyar su ta kasance nurse duk da bata fita aiki domin mahaifin su bai amince ba, a cewar sa yana da rufin asirin da zai iya riƙe iyalansa to babu dalilin da zai sa matarsa tana yawon titi a matsayin ma'aikaciya.

Abdul khabeer ya kasance ɗa mafi soyuwa a zuciyar Auntyn sa yadda ta ke tattalin sa ko su Hassana ba ta yi wa haka, shi kuma Medical doctor ne a India ya samu shaidar karatun sa, a Kano iyayen na sa su ke zaune domin shi pharm Abas acan ya ke aiki, sai dai shi yana zaune ne a Kaduna, kasancewar kakannin sa acan su ke da zama. Sai kuma Allah ya yi acan ne zai samu aiki. Ya kan daɗe bai leƙa gidan kakannin na sa ba, kasancewar sun taso shi a gaba da zancen aure, yadda suka damu da ya yi aure ko iyayen sa ma ba su damu haka ba.
Taslim cousin sister ɗinsa ce wato ƴar ƙanwar Mahaifin sa, sa'ar ƙannin sa ce twins, duk da dai ma su ne a gabanta dan sun bata watanni da haihuwa, girman jikin da ta ke da shi ne ake yi mata kallon wata cikakkiyar budurwa ba kamar su Hassana ba, kyakkyawar yarinya ce ta gaske, kuma tun da ta buɗe idon ta Allah ya jarabceta da son Doctor Abdul khabeer, sai dai shi ne ya ke basarwa dan ba ya so yarinyar ta kawo masa raini tunda dai ya san ko shi ba zai iya auren ƙaramar yarinya kamarta ba, saboda ita ne ma ya sa ya daina zuwa gaishe da goggon ta sa.

Tunda Pharm Abas ya sanar da shi cewar za su shigo Kaduna jikinsa ya ba shi cewar buƙatar kakansa ne kuma ya san ba zai wuce zancen cewa ya yi aure ba ne, kullum faɗar su ke wai har ya fara tsufa a gida, shi dai sai dai ya bi su da murmushi kawai domin ya san cewar matar da ya ke so tana nan zuwa gareshi.

Wannan kenen.

DURUNBU fam#

Lokacin da Meemerh ta fita daga falon sai tattaunawar ya dawo a tsakanin mutum huɗu 4, wato su Baba Musa, shi dai Abie ido ne kawai na shi, yana sauraren musun da suke yi a tsakanin su akan auren Meemerh duk da yana jin ciwo da zafin aibata Meemerh da suke yi sai dai ba zai iya furta komai ba, domin su ne gaba da shi idan ka cire Baba Auwalu shi ne kawai ƙaninsa a cikin su, kuma shi ne wanda be goyi bayan hukuncin su ba.

"Ahmad kana jin abun da muka
Yanke ko bai yi maka ba ne shiyasa ka yi shiru ba ka ce komai ba? Girgiza kai Abie ya yi cikin sanyin jiki ya ce, "Yaya me zan ce a hukuncin da iyaye suka zartar kan yaransu, tunda kuna ganin haɗa ta da Bashir ɗin ya dace ai shikenan, nawa kawai fatan Alkhairi ne."

Cike da jin takaicin haushin kawaici irin na Abie ga mutanen da basu cancanta ba, Baba Auwalu ya ce,
"Yaya shin idan kai ka Amince ita Meemerh ta yarda ne? me ya sa za'a haɗa ta aure da Bashir bayan kun san cewar akwai cutarwa a ciki, yarinya da hankali da natsuwar ta za'a baiwa wannan malalacin ita, wallahi ba zai yiwu ba, kuma ni ba zan goyi bayan hakan ba!"

"Lallai Auwalu ban san cewar baka da mutunci ba sai yau, yanzu a gaban Yaya Musa ka ke kiran ɗansa da malalaci?"

Cewar Baba Isah.

MUGUN NUFI Where stories live. Discover now