page 10

7 0 0
                                    

*MUGUN NUFI*
     _(Baya kashe ɗan_ _barewa)_

PAID BOOK

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى*  *ASSɷ* 📚✍*
  _{Onward Together}_

_STORY AND WRITTEN_
                  _BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////

LAST FREE PAGE

🅿️:1️⃣0️⃣

*Kindly Make ur payment through my bank account 👉* *0034847179*
*Fiddausi sani*
*Stanbic bank*
*And send ur evidence via* *my Watsap number*
     *08039228702*

Washegari tun da safe ya dauko wayar, tunanin wace number ya kamata ya kira yake, se ya tuna da Durling sis wannan ya bashi tabbacin ƴar'uwarta ce, dan haka kawai ya dannan kira, sedai har ta ƙarashi ringing ba'a daga ba, se da yayi 3missed call a jere duk ba'a daga ba, ajiye wayar yayi ya shiga wanka.

Har ya gama shirin sa, domin Monday ce ta ze ta fi wurin aiki, ya na shirin fita daga ɗakin se ga wayar ta yi kara, da sauri ya dawo, numbern da ya kira ba'a daga bane ta ke kira yanzu, se da ta kusa katsewa tukuna ya daga, handsfree ya dannan wayar ba tare da yayi magana ba, da ga can muryarta ta bayyana me cike da bacci da alama ta shin ta kenan " Ke wannan uban missed call na lafiya ne, ko mafalkina kikayi yau? " Shiru beyi magana ba," Hello, Hello, Meemerh ko ba ki jina ne?".

"Meemerh" ya maimaita sunan a kan laɓbansa " ke ba na son iskanci idan kinsan ciwon ƙyaluwarki ne ya motsa miye na kira na to" tsaki tayi zata kashe wayarta, cikin inda inda yace " Am ba ita nace" cike da mamakin jin muryar na miji ya daga wayar Meemerh, Suhaima ta ce, " to waye? Am kin gane jiya ne muka dan so samun accident to Allah dai ya kiyaye shine ta tafi ta bar wayar ta a wurin, na yi tunanin zata kira don cigiya amma shiru shine nayi amfani da layin dan kiran wani nata saboda na maida mata da wayar" fashewa da daria Suhaima tayi ta ce , " kace kai ne wanda ya firgita ta a jiyan nan, idan dai Meemerh ce ze iya yiyuwa ba ta ma san ta bar wayar anan ba tunda kaga ba ta nemeta ba " Allah sarki ai na ga kamar ita sha'anin wayar baya gabanta, yanzu dai idan babu damuwa dan Allah ina zan iya samunta se na kai mata wayar?

" Kai kana ina ne yanzu? Ehhh to yanzu dai zan tafi wurin aiki ne, shine nake so if possible, ki bani address na ku se na zo na kawo mata idan na taso da ga wurin aikin" ok to idan ka ta so daga aikin ka kirani se na yi maka kwanatancen gidan, mun gode fa " daga haka suka katse kiran.

#Meemerh

Fitowar ta da ga wanka kenan ta na zaune ta na shirya jikinta, sai ga Bahba ta shigo bayan sun gaisa ta ke sanar da ita sakon Abie, " dama Alh ne ya ce na kira ki saboda yana ta kiran wayar ki ba'a dagawa" juye juyen neman inda ta ajiye wayar ta ke, dan ita sam se yanzu ne ma ta tuna da wata waya, ganin bata ganta ba se ta ce, " Kinga Bahba ban san ma ina na ajiye wayar ba ina tunanin a sillent ta ke, ki sanar da shi ina zuwa" ganin irin kallon da Bahba keyi mata ne ya saka ta tambayar, " Bahba lafiya dai ko akwai wani abun ne? Cikin sanyin murya ta ba ga amsa da fadin," Babu komai sedai kawai in ƙara baki hakuri ki yi haƙuri da duk wasu kalubalen da ke faruwa a gidan nan, insha'Allah komai ze wuce" tana gama faɗar hakan ta juya ta tafi, mamakin kalamanta su ka bawa Meemerh" something fishy" ta faɗa tana zura doguwar rigar da ta fitar da sauri, dan zuwa ta ji me ya faru kuma, me ta sake aikatawa.

Tun daga stairs din take jiyo hanyiyar su Bahba Musa, addu'a ɗauke a bakin ta ta karasa saukowa cikin mutuwar jiki, dan ta san zuwan su gidan ba alkhairi bane, daga ne da dasu kadan ta tsuguna kanta a kasa ta gaishe su, Abie ne kawai ya amsa ta tare da fadin" Mamana kin san shi aure fa lokaci ne kuma wani ba ya auren matar wani, ki sani duk duniyar nan babu wanda ya isa yayi miki abun da ba ya cikin kaddararki, ki ɗauka hakan Allah ne ya tsara miki kuma insha'Allah ze zame miki Alkhairi"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 16, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MUGUN NUFI Where stories live. Discover now