page 2

4 1 0
                                    

*MUGUN NUFI*
     _(Baya kashe ɗan_ _barewa)_

PAID BOOK

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى*  *ASSɷ* 📚✍*
  _{Onward Together}_

_STORY AND WRITTEN_
                  _BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
//////////////////////////////////////////////////

FREE PAGE

🅿️2️⃣

*Kindly Make ur payment through my bank account 👉* *0034847179*
*Fiddausi sani*
*Stanbic bank*
*And send ur evidence* *Via my* *Watsap number 08039228702*
*Is 300 only*

Haka Suhaima ta kasance zaune ita kaɗai a falon, sai da lokacin sallah ya yi tukunna ta koma bedroom ɗin, ganin numfashin Meemerh ya koma normal sai ta gyara mata kwanciya ita kuma ta shiga toilet dan ta yi alwala.

Tana cikin sallah ne ta ji motsin Meemerh alamar ta tashi kenan, toilet ɗin ta shiga ta yi wanka kafin ta yi alwala ta fito ita ma. Lokacin Suhaima har ta idar da Sallah tana bakin gado zaune tana danna wayarta da alama chat ta ke yi, haɗa ido suka yi se suka sakarwa juna murmushi "Ya jikin naki?"
Suhaima ta tambaya tana ajiye wayarta kan bed side drower, kai Meemerh ta ɗaga mata alamun da sauƙi, bata damu ba, saboda ta saba dama can Meemerh ba me yawan surutu bace, idan ka ga ta yi doguwar magana to da Abie ne ko kuma ita Suhaiman. Ta shi ta yi ta shimfiɗa mata pray mat, tana kallon ta sai da ta gama shirinta tsaf kamar babu abinda ya faru kafin ta kabbarta sallah.

Tana cikin sallah ne Abie ya shigo ɗakin.

Ajiyar zuciya ya sauke ganinta cikin ƙoshin lafiya, maida hankali sa ya yi wurin Suhaima da ke masa sannu da shigowa, cikin sakin fuska ya ce "Sannu da ƙoƙari Suhaima na ji daɗin ganin Meemerh cikin natsuwarta, ban yi tunanin zan sameta a haka ba."

Dariya ta yi, ta ce, "Abie yanzu fa ƴar budurwarka ta fara zama jaruma, ai ta girma."  Meemerh da idar da Sallahn ta kenan ta juyo tana watsa mata hararar wasa."

"Dama jaruma ce ni Malama ko Abie?"

"Ƙwarai kuwa."  Ya faɗa cikin farin ciki, "Ina fatan dai babu abinda ya ke damun ki a yanzu?"

  "Babu komai Abie ina lafiya, na ji daɗin ganin ka haka kaima, ka yi haƙuri Abie ina jin tsanar kaina, kasantuwa ta ƴa ɗaya tilo da Ubangiji ya baka, kuma na kasa sama maka farin ciki, a kaina kullum ake faɗa maka baƙaƙen magana, na yi maka alƙawari insha Allah wannan shi ne karo na ƙarshe da hakan zai sake faruwa, ba zan sake kula ko wanne namiji ba bare  har daga ƙarshe akai sukana akan abinda wata bare ta aikata tun ban san menene duniya ba. Abie ka yi min komai na rayuwa, abu ɗaya da ka kasa yi wa rayuwa shi ne auren macen da bata da ce ba me yasa na fito ta tsatson ta, kullum se na yi wa kaina wannan tambayar, bana sonta kamar yadda na san cewar ita ma bata sona, na tsaneta, ko a lahira ina rokon Allah kar ya nunamin azzalumar fuskar ta!"

Share hawayen da suka zubo masa ya yi,  ya tsuguna tare da kama hannun Meemerh. "Mahaifiyarki bata cancanci wannan kalaman naki ba Meemerh, tana sonki, ni na san cewar tana sonki kuma har abada ba za ta dena son ki ba, daga yanzu idan ba Alkhairi za ki faɗa akan matata ba kar ki sake aibata ta a gabana, kina da damar faɗar abunda ki ka faɗa saboda hakan aka dasa a zuciyarki, sai dai yau ina so na faɗa miki cewar idan cuta ne ni ne na cuceta ba ita ta cuceni ba kamar yadda su ke faɗa, mu ci gaba da addu'a insha Allah wata rana komai ze zama labari"

"Abie kullum fa haka ka ke faɗar komai ze zama labari shin se yaushe ne zan bayar da wannan labarin, se yaushe ne ƙaddarar matarka zai dena bibiyana, wani lokacin laifin ka nake gani, ina ganin kamar da gangan ne ka ƙi zaɓa min uwar da ta dace, duk da ina kwaɓar zuciyata duba da halaccin ka a gareni, ka maye min gurbin uwa da uba ina ma a ce kai ne uwata kuma kai ne uban, kana da nagartar da babu wanda ya isa ya aibata ka, da yanzu ina cikin farin ciki babu wani tabo a rayuwata, amma babu komai akwai Allah shi zai saka min." Kife kanta ta yi a jikin Abie tana sakin wani marayan kuka wanda ke bayyana ainahin ciwon da ke damun zuciyarta, Abie be sake magana ba se shafar bayanta da ya ke yi alamar rarrashi, ita kanta Suhaima kukan ta ke yi.
Ta rasa wane irin sirri ne wannan wanda ba za'a faɗa ba, duk da a zuciyarta tana zargin koma menene silar barin Mahaifiyar Meemerh a gidan Abie to ba zai wuce kitimurmurar ƴan'uwansa da matan sa ba ne.

MUGUN NUFI Where stories live. Discover now