page 9

0 0 0
                                    

*MUGUN NUFI*
     _(Baya kashe ɗan_ _barewa)_

PAID BOOK

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى*  *ASSɷ* 📚✍*
  _{Onward Together}_

_STORY AND WRITTEN_
                  _BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////

FREE PAGE

🅿️:9️⃣

*Kindly Make ur payment through my bank account 👉* *0034847179*
*Fiddausi sani*
*Stanbic bank*
*And send ur evidence via* *my Watsap number*
     *08039228702*

Har dare Abdul khabeer yana da kon kiran ta, ko wani nata amma shiru, duk se ya bi ya damu domin yana da bukatar sake jin sanyayyiyar muryarta, ajima kaɗan ze duba wayar duk da ba'a sillent ta ke ba, zuwa can dai dubarar cire layin wayar ya zo masa, da sauri ya dauko wata ƙaramar waya a cikin cobbord din sa ya cire layin wayar Meemerh se ya saka a wayar, contact ya shiga to his own surprise lambobin da ke ciki basu fi guda 10 ba, mamaki ne ya kamashi, se kuma yayi tunanin maybe to tana da main line da take using ne shiyasa ba ta damu da wannan ba.

Fara duba wa yayi, numbrn farko yaga an rubuta Durling sis, se wata an rubuta C, mudassir, Sauran kuma babu suna kawai dai anyi saving ne akan wayar a karshe ya ci karo da wacce akayi saving amma da Arabic word ne ƙura wa lambar ido yayi , Ƙurratu-ain, aka rubuta tare da heart emoji, dum!! Yaji gaban sa ya fadi tabbas ko be tambaya ba ya san numbrn saurayin ta ne, samun kansa yayi da danna delete, ya goge numbern tare da jan tsaki, yana ajiye wayar.

" Yaya lafiya ka ke faman tsaki kai ɗaya? Cewar Hassana da shigowar ta kenan dan isar masa da saƙon Aunty, harara ya jefa mata" to tambai aike bazaki taɓa canja shegen halin nan na ki ba, ace yarinya sam bata da self respect abunda be shafeki ba se kinyi magana, shiyasa Usaina ta fiki hankali ai, wai ma me ya shigo da ke nan? Turo baki ta yi saboda a duniya babu abinda ta tsana kamar a gwasaleta " Aunty ce fa ta ce ka fito zamuyi dinner tun dazu bata ga ka fito ba" ta faɗa tana raurau da ido alamar zatayi kuka. Sai kuma ta bashi tausayi domin haushin Meemerh ne da ta yi saving numbern gardi da wannan sunan ya bashi haushi, ka mo hannunta yayi ya zaunar da ita bakin gado

" Sorry lilina ke ma kinsan bama haka ai, ke fa Yanzu big lady ce kidena saurin kukan nan, dan nan kusa aure xanyi miki " cikin shagwaɓa ta ce " to yaya ba kai bane, kaima yanzu zaka fara biyewa Aunty komai se kuriƙa cewa Usaina ta fini hankali yanzu daga na tambayeka shikenan se masifa" to kiyi hakuri na dena baxan sake ba, yanzu ki tafi kicewa Aunty ina zuwa ".

Bata sake magana ba ta fita daga ɗakin.

#Meemerh

A gidan su Suhaima ta wuni, se dare ba yan sunyi sallahr isha'i tukuna tayi shirin komawa gida, babu yadda Suhaima batayi da ita akan ta kwana ba, amma fir taƙi amince wa, dukan wasa Suhaima tayi mata ta ce, " da ma na san ai bazaki kwana ba, tunda cinye ki zamuyi" gwalo Meemerh tayi mata ita ma cikin raha ta maida mata magana da fadar, " ke kam na fi so na ganni kusa da tsoho, awa nawa ban ganshi ba, kinsan idan har ba baya gari bane to bana zama nesa dashi ba" kyaji da shi kuma, nide mu tafi in raka ki Malama" haka suka fito, se da ta shiga ɗakin Maman Suhaima tayi mata sallama tukuna suka fice. koda ta ko ma gida, ɗakin Abie kawai ta tafi ta gaishe shi tare da sheda ma sa dawowarta, daga haka ta dawo dakinta, saboda a gajiya take barci ne a idon ta.

Har ta yi shirin barci, ba ta kula da wayarta bata tare da ita ba, dan haka tanayin addu'ar bacci tayi kwanciya abinta.

#Abdul-khabeer

Sam ya ka sa sakin jikinsa ya ci abinci, sosai Aunty ta ke kula da yanayin damuwar da yake ciki, ba ta dai yi magana ba, har se da kowa ya gama cin abincin sa, ta shi yayi ze fita, ki ran sunan sa da ta yi ne ya saka shi dakatawa tare da juyowa ya dawo, mikewa ta yi tana nufar dakin ta kafin ta ce " ka sameni a ɗaki"

Be Musa mata ba, ya bi bayanta, a bakin gadon ta ta zauna shi kam tsaye yayi, stool din da ke gefen gado ta nuna masa " ka zauna mana" anan ma dai zaman yayi, cikin hikima ta fara yi masa magana " Abdul-khabeer menene damuwar da ka zabi barinta a zuciyarka ta cutar min dake fiye da ka sanar dani, ita damuwa tana illa ne a lokacin da mutum ya barta cikin cikinsa, ko da ace babu me iya share maka hawaye se nake gani kamar bayyanar da ita ze rage mata karsashi acikin zuciyarka, shin ko dai maganar da Papi yayi ce take damun ka, idan har wannan ne ka sani ko da yaushe ina bayanka bazan taɓa bari ayi maka abun da ba ka so ba, nide dan Allah ko baxaka iya sanar dani damuwar ka ba, to ina so kayi ƙoƙarin ya ki ce ta daga zuciyarka, dan bana so ya cutar da kai"

Duƙar da kan sa yayi ƙasa yana nazarin kalmomin da zasu fito daga bakin sa, gaskiya ne duk duniya bayada majinginar damuwar sa kamar Aunty domin tana yi masa son da be da misali,  ɗago kansa yayi ya dubeta, se ta langwabe kanta alamar roko.

" Aunty Kinsha fadar cewar kima so kiga ranar da zan kawo miki mace da sunan wacce na ke so, tabbas na haɗu da yarinyar da ban taɓa jin abinda nake ji akan ta kan ko wa ba, ba wai saboda kyau ko wai abu ba, natsuwar yarinyar ita ce abu na farko da ya fara taba zuciyata..... Labarin komai ya bata,tun da ga karo da suka ta shi yi da mota har tsawar da yayi mata da haukrin da ta bashi, ya karasa da daɗin, " Aunty a yadda yaran yanzu basu da kunya kina ganin idan da wata ce zata yarda bata maida min magana ba daka ƙarshe ma ta bani haƙuri?

Dogon nunfashi Aunty ta ja kafin ta ce, " to ai ni jira nake naji dalilin damuwar ta ka, na ga dai ba kaje kaji ta bakin ta ba to Miye na damuwar? Aunty ai na faɗa miki tabar wayarta a hannuna ko shine fa ina duba wa na ci karo da wata number.." se kuma yayi shiru " ina jinka me ya faru da kaga numbrn? Aunty sunan da ta yi sarving ne na ga kamar na saurayin ta" murmushi aunty tayi tare tambayar " wane suna ne wannan ya saka likitan ɗana fargaba? Aunty ni na manta ma sunan amma dai irin suna ne da ke nuna kana matuƙar ƙaunar wanda ka rubutawa shi " Abdul-khabeer" ta kira sunan shi

Ɗago kai yayi ya kalketa, " Me ka rubuta a nunbrna? World best" ya bata amsa " to yanzu idan wani yaga wannan sunan a wayarka se ya ce ni budurwar ka ce? A'a Aunty" yawwa to ze iya yiyuwa ita ma numbrn Babanta ne ko kuma yayanta ba lale se saurayinta ba, ka ga ban san ka da karaya ba, ko da ma ace saurayinta ne idan har ba baiko akayi musu ba kana da damar shiga sahun manema ai, kuma idan rabonka ce se ka ga ka sameta, ka kore shi wanda ka isko, saboda haka kar kayi nauyin baki, ka isa gareta, ka kuma yi addu'a idan Alkahiri ce, domin da zafi zafi akan dake karfe, so nake ka tabbatar da idan zaka iya samunta saboda mu dakatar da Papi daga zaɓin da yake shirin yi maka, kafin maganar tayi nisa, ka san dai tsab pharm goyon bayansa xeyi ko?

Ajiyar zuciya Ya sauke, domin kalaman Auntynsa sun bashi ƙwarin gwiwa, to shi me yasa tun farko ma beyi wannan tunanin ba?.........

Comments and share pls

Kar ku manta ku biya kudin ku
Jiya nace wannan ne last free page, to zan kara daya sakamakon alfarma da wasu suka nema, daga shi bazan sake ba idan kuna so ku biya kudin ku

#Real@Bazamfari💋

MUGUN NUFI Where stories live. Discover now