page 3

1 0 0
                                    

*MUGUN NUFI*
     _(Baya kashe ɗan_ _barewa)_

PAID BOOK

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى*  *ASSɷ* 📚✍*
  _{Onward Together}_

_STORY AND WRITTEN_
                  _BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////

FREE PAGE

🅿️:3️⃣

*Kindly Make ur payment through my bank account 👉* *0034847179*
*Fiddausi sani*
*Stanbic bank*
*And send ur evidence* *Via my* *Watsap number 08039228702*
*Is 300 only*

Da daddare suna zaune suna hira, duk da dai kusan hirar tsakanin Suhaima da Meena ne, ita dai Meemerh nata sauraren su ne kawai, dan tun abun da ya faru da ita a asibitin nan ya ƙi barin zuciyar ta, ta rasa me ne ne ya haddasa mata wannan faɗuwar gaban.
"Am Suhaima ko za ki rakani gida ne? Ina so na ga Abie Kin ga duka mun bar wayoyin mu a can na tabbata hankalin sa na can a tashe, zai yi ta kiran wayarki."

"Meemerh yanzu fa zancen ƙarfe goma ake yi ina za mu tafi yanzu? Dady ma ba zai bari mu fita ba, kawai dai ki amsa wayar Meena ki kira shi, kuma ma ai na san Bahba za ta faɗa masa cewar kina lafiya."

Kallon Suhaima ta yi kamar za ta yi magana sai kuma ta kalli Meena, fahimtar akwai maganar da ta ke so su yi ne ya sa Suhaima ta umurci Meena da ta tafi ta kwanta dare ya yi, sai da safe ta yi mu su tare da yi wa Meemerh fatan samun lafiya, ta fice.

"Ina jin ki to." Suhaima ta faɗa tana murmushi.

Sai da Meemerh ta sauke ajiyar zuciya kafin ta fara kora mata bayani. "Suhaima bana baƙin ciki da barina da Mujahid ya yi, kin sani tun farko alfarmarki ya sa na fara kula shi, sam bai yi min ba, na yi ƙoƙarin ganin na nuna masa soyayya kamar yadda ki ke buƙata, har manya su ka shiga lamarin sai ga shi rana tsaka ya watsa mi ki ƙasa a ido, Suhaima a yanzu bana tunanin akwai wani namiji da ya yi saura a duniyar nan da zan iya kalla da sunan so, tambayar ki zan yi, shin me ya sa mutane ba sa uzuri a rayuwar su, me ya sa laifin wani zai shafi wani, shin meyasa duk ƙoƙarin kare Mutuncina da na ke yi ba ya tasiri? kawai saboda wata matar da da ace an bani zaɓi ba zan zaɓe ta a matsayin wacce zan zauna a duhun cikin ta ba. Suhaima me wannan matar ta aikata ne da har munin sa ya kasa shafewa a zukatan mutane? Abun nan fa tun bayan zuwana duniya ne, ba kya ganin ya kamata ace zuwa yanzu an manta da shi ba?

Girgiza mata kai Suhaima ta yi, cike da tausayin Aminiyar ta ta, ta ce,
"Meemerh shin ba ki ji me Abie ya faɗa ba? Mahaifiyar ki mutuniyar kirki ce, abin da ki ka kasa ganewa shi ne duk masu zuwa neman auren ki zuwa ake ana hanasu neman ki, idan an zo kora mi ki bayani sai a yi amfani da tsanar da ki ke yi wa Mahaifiyar ki wanda duk wanda zai raɓeki zai san cewar ba ki ƙaunarta, shi ne sai su ke nuna mi ki cewar laifin da ta aikata ne ya ke sa ana gudun ki. Meemerh ke ba yarinya ba ce ya kamata ki yi tunani, shin me ya sa ake auren ƴaƴan shegu ma kuma an tabbatar cewar ba su da Iyaye? Saboda babu wanda ya isa ya dakatar da abinda Allah ya ƙulla, ko da ma ace laifin me ta aikata ba zai zama dalilin rusa auren ki ba Meemerh, ba kuma zai zamo dalilin tsanar da ki ke yi mata ba, iya rayuwar gidan ku idan ki ka kalla za ki san kitimurmurar da ke cikinsa, sanin sa ne dai sai Allah, Allah zai iya jarabtar ki da hakan ko dan ƙiyayyar da ki ke yi wa wacce ta sha wahalar haihuwar ki.

Dakata Suhaima! Wace uwa ce za ta yi watsi da rayuwar ƴarta tun ba ta gama sanin me ne ne duniya ba, wace uwa ce za ta juyawa rayuwar ƴarta baya tsawon shekaru Ashirin da biyu kuma bata waiwayeta ba? me ya sa ta aikata abin da ta aikata wanda shi ne ya zame mini tabo a rayuwata? Tabbas abinda ta aikata ya yi muni Suhaima tunda har Abie ya iya yi wa matansa barazanar barin gidan sa ga duk wacce ta yi ƙoƙarin sanar da ni, tunda har girmansa ya hana su Baba Musa sanar da ni duk da tarin tsanar da su ke yi min, tunda har illar sa ta hana Dada ambatamin shi sai dai takan ambaceni da ba jinin ta ba, Suhaima, zuciyata ta yi rauni na fara yarda da maganar Dada na cewar ni ɗin ba jinin ta ba ce, ina tunanin ƙazantar da ta aikata kenan Abie ya kasa zama da ita, ni alfarma ɗaya nake so su yi mini su faɗa min wane kwarton ne ya yi mata cikina har ta haifa, wane tsinannne ne ya yi sanadin zuwana ba ta hanyar da ta dace ba, suhaima ina ji kamar na kashe kaina na huta na gaji da baƙin cikin wannan rayuwar! Kuka ta ke yi bilhakki da gaskiya ta fita hayyacin ta se surutai ta ke yi, da kyar Suhaima ta yi nasarar rufe mata baki tana girgiza mata kai alamun ta daina, domin ita kanta ba za ta iya cewa komai akan hakan ba, ta fara yarda da maganar Meemerh na cewar laifin da mahaifiyarta ta aikata kenan, sai dai a matsayin ta na wacce ke rarrashin ta be kamata ta nuna karaya ba, da ƙyar ta haɗa kalmomin da zata faɗa mata.

MUGUN NUFI Where stories live. Discover now