Part 1

6 2 0
                                    


Bismillahi rahmani rahim

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, wanda ya bani karfi da tunani har na rubuta wannan littafin me suna Ummu salma.     

The book is dedicated to my lovely mom, Hajiya khadijat Umar ...

This book is a paid book, and I want you guys, da kuyi supporting ɗina gurun siyan wannan novel ɗin... 


    

    Thirteen year old salma has been through a lot in the past, from losing her parent, to then having an aunt that wasn't too fond of her. Beat after beat and punishments, after the next, she still pulls through. 

    .

Free page

#1

Zaune take a kan tabarma, a tsakar gidan, dafafiyar shikafa da miya takeci, cikin nutsuwa kamar wata babba... Yarinya ce da bazata haura shekaru goma sha uku ba. Wata matace da bazata haura shekaru talatin da biyar ba. Tashigo gidan buja buja da ita kamar wata sabuwar mahaukaciya. Kallon kyakyawan yarinyar dak'e zaune Tana cin abincinta Bata masan da shigowan tab'a matar tayi. Hankali atashe matan ta ke kallon yarinyar, atsawace tace " Salma.. agidan ubanwa kika samu abincin dakikeci? Juyowa yarinyar data Kira da Salma tayi bayan ta ad'iye sauran abincin dake bakinta tace "gwaggo yaushe kika dawo? Crossing Hannayenta wacce aka Kira da goggo tayi atsawace tace "uwarki kike tambaya baniba.. Dan uwarki bakin amsamin tambayar danake makiba, ko sai na tatakaki?.. ajiye spoon din dake hanunta yarinyar tayi, gabanta na faduwa cikin siririyar muryarta tace "yunwa nakeji, shiyasa na dauka". A tsawace matan tace " kambatan ubba, abincin Dana ajiye wa hafsah taci in tadawo, kika dauka?.....wayyo Allah, yau saikin yaba wa ayya zakk'i. Da sauri tashiga dakinta, tafito da dorinan data sayo musan man dan punishing na Salma . Zumbur Salma tamike Tana zaro manyan idanunta tace " wlh gwoggo karki dukeni da wanan abun, it hot so much" takarasa fad'a Tana matso kwalla.... Wani dariyan mugunta gwoggo ta ketce dashi Tana fad'in"Dan uwarki, ya'u ko mutuwa zakiyi,Banga abin dazai hanani bugun ki dawanan dorinan ba"" da Dan gudu ta karaso gurin Salma dake baya baya, jikinta na rawa, d'aga bulalan tayi, tasauke mata ajikinta babu ko Imani...wani irin ihu Salma tayi Tana kuka, Dan in akwai abin da Salma ta tsana a duniyan nan shine bulala, ganin irin ihun data keyi kamar wacce za'a yanka, yaba gwoggo haushi tafara jibgarta Kamar wata animal......sai datayi mata likis, kamin tabarta a yashe a kasa Tana fad'in"shegiya, gobe idan na'ajiye abu, kyadauka kici, dukda nasan abanza, Dan kina warkewa zaki Kara aikata wani laifin"ta karashe Tana dungurinta a goshi, sanan tashige dakinta, Tana tub'e hijabin dake jikinta data dawo daga unguwa dashi.... ahankali Salma tamike zaune,still Tana sauke ajiyan zuciya, akai akai Dan tsaban yanda taci kuka...mikewa tayi walking slowly tashiga toilet Dan yin fitsari....atsakar gidan Salma tacigaba dazama batare data shiga cikin dak'i ba...wata yarinyace tashigo cikin gidan sanye da uniform black trouzer and white riga dayakai har gwiwanta,kanta sanye da karamin hijabi shima fari.... Yarinyace daba zata haura shekara sha biyar da haihuwa ba, fuskar Nan nata a daure, Kamar Wanda akayima albishir da mutuwa....Koh kallon Salma dake yi mata sannu da dawowa batayiba ta shige cikin dakin su dake kusa dana gwaggo....., canza uniform dake jikinta tayi da wani kod'ad'an atamfa riga da skirt, bak'in fuskarnan nata a daure tafito daga cikin dakin su, ta shige cikin na gwaggo......kwance tasami gwaggo akan tabarma tawani baje Tana kwasan bacci, sai munshari takeyi, hankali kwance.....kallonta hafsa dake ta hura gajeran hacinta tayi, da karfi tace"gwaggo, gwaggo" Koh motsi gwago batayiba Dan yanda baccin yayi mata dad'i.....da Dan sauri ta dauko wani kwanun samiran data gani yashe a dakin, sannan ta dawo Nan inda gwaggon ke bacci.....da iya karfinta ta sake kwanun yafado kasa, yabada Kara timmmm......a zabure gwaggo ta Mike zaune Tana zaro idanu, har daure kirjin datayi na niman kwancewa, tabe Baki hafsah tayi sannan tace"abincina nake son kiban.....kallon direction din data ji magana tayi a Dan tsawace tace"yanzu fisa bililahi kin min adalci kenan hafsa"wani mugun kallo hafsa ta mata Tana murgud'a Baki tace"Ni dai kawai kibani abinci na, inyaso sai ki koma baccin ki" ta karashe maganan in i don't care tone........ Baki sake gwaggo ke kallon diyar tata sanan tace" ya'u kam saidai ki dau na anabawa, kisha garin kwaki, dan yar iskar yarinyar can, ta dauke abincin dana ajiye maki ta cinye" hankali a tashe hafsa tace" but how inna? Taya zaki yarda ta dauke min abinci taci yanzu kuma ace nasha garin kwaki, bayan ke kanki kinsan yarda da tsani shan kwaki"hamma gwaggo tayi tana mitsi mitsi da ido tace" wlh daga zuwa gidan suna ingaya maki, sai na dawo naa tarar tana cin shinkafar dana ajiye maki" wani irin tsalle hafsa tayi tana fad'in"lalai ya'u sai na ci uban..... Katseta gwaggo tayi atsawace tace" arniyar uwarta dai kinci, badai yaya na dake kwance a kabarinsa ba" tana gama fad'in haka ta kwanta, murya kasa kasa tace" ki duba cikin dogon kullan nan zaki ga suger da soyayan gyad'an mallam daya bani ajiya, ki dauka ki sha garin dashi"..... Bud'e lumsasun idanunta tayi tana kallon hafsan tace" koh sai nagaya maki inda garin yake ne? Girgiza mata kai hafsa tayi tana hura dan guntun hancinta, tafice daga dakin...... Nufar salma tayi dake zaune har yanzu tana huci kamar zaki tace"ya'u sai na nuna maki shayi ruwa ne" tuni salma ta mike tsaye tana kallon hafsa tace"have i done anything wrong ne kuma? Harararta hafsa tayi tace" idan naci uwarki ai zaki san you've done something wrong ai" takarasa maganan tana cakumo salman tana wani zazaro idanu..... Kallonta salma keyi babu ko kiftawa, zuciyanta na tafarfasa tace"kar ki sake ki kara zakin uwata data ciki grave dinta hankali kwance" dariyan rainin wayoo hafsa tayi sanan tace"ashe kafurai ma na kwanciya hankali kwance" haushi ne ya kara cika salma, hakan ya sanyata tunkud'e hafsan da dukkan karfinta.... Baya hafsa tayi ta fad'i kasa timmm....... Mikewa tayi daga kasan sanan tayi hanyar d'akin gwaggo dan shan garri, saboda in tabiye ma zuciya ba abin da zai jawo mata sai raini gurin yarinyar nan.....


Washegari da tsamin jiki salma ta tashi, Hakan Kuma Bai Sanya gwaggo taji tausayinta ba..... She kept doing the house chores, tun daga kan wanke wanke, shara har zuwa diban ruwa ita tayi shi....... Kwance take Akan tabarma a tsakar gidan nasu sai rolling takeyi tana kama cikinta, saboda yunwan Dake cinta, Dan tun kunun safe da gwaggo ta Bata Tasha tayi breakfast dashi, ita Kuma tace Bata iya Shaba.... Shine har yanzu kusan karfe uku na Rana Bata Sanya komai a bak'in tana..... Mikewa tsaye tayi jikinta a sake ba energy ta shiga takawa a tsanyaye zuwa dak'in gwaggo...... Zaune ta sameta ta barbaje kund'in da tayi ciniki kayan matan data siyar jiya Sunna, murmushi kwance a fuskarta take k'irga kud'in feeling so happy...... Dan turo Baki gaba salma Dake kallonta a bak'in kofa tayi sannan ta qaraso cikin dak'in, tana kallon gwaggo a hankali tace"gwaggo yunwa nakeji" a zabure gwaggo ta Tatara kud'ad'an ta boye so under tabarmar da take Kai...... Duban salma tayi tace"toh sai akayi Yaya, Dan kinajin yunwa sai kizo ki tsaya min a tsaye, Koh ni nace kar Kisha kokon Dana Baki da safe, ko Kuma ni kike son ki cinye d'anya.... Shagiya dangin arna" kallonta salma takeyi babu ko blinking idanunta na cukowa da hawaye, Amma Bata yarda ya zubo bah.... Cikin Dan cracking tace"gwaggo... Toh .. ki bani .. kunun insha yanzu" Baki Bud'e gwaggo ke kallonta kamin ta kece da dariya San tace"yarinya ai kin Riga da kinyi asara tunda har kikace bazaki Sha ba... Sai dai kijira a gama sanwan dare kici" Dan marairaicewa salma tayi tana hade Hannayenta waje daya tace "Dan Allah kiyi hakuri, yunwa nakeji" tsaki gwaggo taja sannan tace"sai fa kiyi.... Ai tunda ki ka k'irkiro ma kanki rashin Shan kunu, yau sai kin yini Baki ci komai ba.....


Pay via Account number: 1003958995 salamatu zakariyau heritage bank then you send your evidence of payment through 08068780599, ko kuma pin ɗin recharge card na MTN 


Forgive the typos 

UmmusalmaWhere stories live. Discover now