Part 8

1 0 0
                                    


💝💝 Ummusalma 💝💝

Free page


#8


Ya'u kwana uku kenan, da xuwan Salma gidansu Umar, ba abun da tanima ta rasa a gidan, Dan aran da taxo gidan da yamma.. aunty husna ta fita tayo mata siyayan abubuwan dabaxa'a rasa bah, tun daga kan kayayaki, takalma, dakuma cream din shafawa, brush da dai sauransu. Har yaran aunty husnan sun Saba da ita yanxu.... 

Xaune take a parlor tana kallon tv, ita kadaice acikin gidan Dan aunty husna ta tafi gurun aiki sannan Kuma yaranta are in school... Sanye take da abaya Bak'i daya mugun haskata, fuskarnan nata fayau sai Wani glowing takeyi..... Kamshin tularansa ne ya bug'i hancinta, a hankali tajuyo ta kallesa... Staye yake a bakin kofan parlon ya rungume Hannayensa, fuskarnan nasa a daure kaman Koda yaushe... Dauke kanta tayi batare datace dashi kala bah .. cikin tafiyansa ya qaraso ya xauna akan sofan Dake facing nata..... Sai taji Wani iri saboda xaman dayayi acikin parlon... Idanunsa na kan tv carmly yace "ba abinci agidan ne?? Dan kallonsa tayi, to make sure kunuwanta ba karya suke gaya mata bah... Tab'e Baki tayi ganin bama ita yake kallo bah, Hakan ya sanyata tunanin maybe her ears was wrong, ahankali ta Maida idanunta kan tv Dake aiki..

.juyowa Umar yayi staring straight into her with so much surprised ganin tak'i tanka masa, carmly yace "so you've now turn to boss lady of this house right?? 

Juyowa Salma tayi takallesa, tana Mai auna maganan daya fad'a... Cikin Dan D'aga murya yace''na lura Baki da kunya ko na second" jinjina Kai yayi cikin zuciyansa yake fad'in ''xan gyara maki xama yarinya".. idanunta na kasa cikin sanyayan muryanta tace"ban Gane Mai kake fad'a bah??.. ko kallon inda take beyi bah ya mik'e ya fice a dak'in cikin tafiyansa Mai cike da takama... rolling idanunta tayi tana Mai dafe kanta, ajiyar zuciya ta sauke tana Mai gode ma Allah da Bai maketa bah...tana ta xaune a parlon cikin fargaban ko xai Kuma dawowa. Ganin har an dau lokaci Bai dawo bah ya sanyata Jin relief acikin zuciyanta.... Karfe uku daidai aunty husna ta dawo da yaranta hud'u dukkansu mata, daga makaranta acikin motan ta... Cikin murna Salma tafito daga parlon ta nufesu fuskanta a sake, sannu da dawowa tayima aunty husna da yaran nata, cikin girmamawa ta Sanya hanunta ta amshi mini bag din aunty husnan, tashigo mata d'aki dashi... Cikin sauri ta juye ma aunty husnan ruwan xafi ta a bucket sannan ta Kai mata toilet Dake cikin dak'in ta, kallonta aunty husna Dake xaune a kan gadonta tayi carmly tace''salma ke dai bakya gajiya da aiki ne"... Itadai Salma kanta na akasa tana wasa da fingers dinta tace"axubo maki abinci akawo Nan ne? ko Kuma kinfito kici a dining ne? Tana kallonta tace"jeki kawai, in nagama can fito inci,but make sure ke kika zuba ma yaran Nan, kada suje sud'ibi abincin dayafi karfinsu su kasa ci"... Gyad'a mata Kai Salma tayi tana fad'in "inshallahu" tana gama fad'in haka ta fice daga d'akin Dan xuba ma yaran abinci Dan tasan halinsu, Suna cire uniform suke fitowa dining... Kamar yanda tayi tunani kuwa Hakan ya kasance Dan tsaye ta Sami Babar cikinsu da baxata haura shekaru goma Sha biyu bah, tana yunkurin d'iban abincin a warmers dake kan dinning table... cikin nutsuwa ta dubi yarinyar bayan ta qaraso dining table ɗin tace"Ummu let me serve you".. plate ta dauka tashiga d'iban mata rice and stew with pepper soup data girka masu, Dan Jin wacce ta kira da Ummu tayi kamin ta koma ta xauna akan kujera, without uttering a word... Haka tayita serving dinsu daya bayan daya, tana gamawa ta koma parlor tacigaba da kallonta...

Har suka gama suka dawo parlor suka xauna aunty husna Bata sauko bah... Can sai ga aunty husnan ta fito ta nufi dining ta xauna, da kanta tayi serving kanta acikin plate, tana gama d'iba ta shiga cin abincinta cikin nutsuwa.... Sallaman da'akayi, ya Sanya dukkansu jujowa suka kalli kofan bakinsu na amsa sallaman da'akayi.. lokaci d'aya Salma ta dauke kanta bayan sunyi Ido hud'u dashi... Tare da Sadiq suka qaraso cikin parlon suka xauna.. cikin fara'a su Ummu suka shiga gaishe su bayan sun xa xauna.. cikin Sakin fuska Sadiq ya amsa masu while shi Kuma Umar ya amsa idanunsa na kan wayansa dayake latsawa.. kallon Sadiq Salma tayi tace"Ina yini".. Dan d'ago Kai Umar yayi ya kalleta, sannan ya Maida kan wayansa.. Sadiq yace" lafiya qalau Salma, ya kewan gida? Tana wasa da gefen mayafinta tace"lafiya qalau, Alhamdulilah".. qarasowa cikin parlon aunty husna tayi tana kallon su tace"sanunku".. kallonta Sadiq yayi sannan ya shiga gaisheta with so much respect.. ta amsa tana fad'in"Salma je ki kawo masu abinci suci''. Har Salma ta mik'e tsaye, Sadiq yace"a'a Salma Yi xamanki daga Wani get together ma muke".. cikin sanyi aunty husna tace"har yanzu dai Baku hakura da xuwa party's bah Koh? Shafa Kansa yayi idanunsa na kasa yace"aunty ai Daman a hankali hankali xa'a barxuwa inshallah".. tab'e Baki tayi Bata kara cewa komai bah.. kallon Umar Ummu tayi a hankali tace "uncle Umar, I have an assignment that will be submitted tomorrow morning, Kuma ni ban iya bah".. batare daya d'ago Kansa ba yace"and so".. Dan marairaice murya tayi tace"in kawo Maka, to assist me with it?.. d'ago Kansa yayi cikin sanyi yace"ok". Cikin murna ta mik'e tayi hanyar d'akinsu Dan dauko book dinta... Ko second d'aya Ummu batayi bah tafito rik'e da exercise book a hanunta ta nufi Umar. Xama tayi a kasa sannan ta Mika masa takardan.. amsan takardan yayi sannan ya shiga Yi mata assignment din cike da kwarewa.. kallonsa Sadiq yayi yace"toh Umar sai ka fito" Yana gama fad'in haka ya mik'e tsaye, gyad'a masa Kai Umar yayi idanunsa na kan takardan assignment dayake solving. sallama yayi ma aunty husna da su Salma sannan ya fice daga gidan ..

UmmusalmaWhere stories live. Discover now