Part 9

1 0 0
                                    


💝💝 Ummusalma 💝💝


Free page


#9


 with high speed aunty husna ke gudu akan titi, sai datayi Nisa, sannan ta tuna bata tambaye shi inda ya ajiyata bah.. gangarawa tayi gefe ta parker motan sannan ta dauki wayanta dake ajiye akusa da ita tayi calling number Umar din.. har ya kusa katsewa ya dauka, Koh sallaman dayayi mata bata amsa bah tace" a daidai ina ka sauke ta?.. tacikin wayan yace"na ibawa road".. katse wayan tayi after hearing that, sannan tacigaba da tuk'inta, hankalinta atashe.. tana kaiwa na ibawa road din tafara dube dube a hanyar bayan ta rage speed din motan, adu'a takeyi acikin zuciyanta, Allah Ubangiji ya bayyanar mata da Salma .. tsoro ne taji yakamata, ganin garin ya fara duhu gashi har yanxu bata hangi Salma bah.. parking tayi agefen titi, ta had'a kanta da steering motan tana mai sauke ajiyar xuciya.. kamar ance ta D'ago kai, idanuntane suka sauka akan wata yarinya dake tsugune a kasa ta had'a kanta da gwiwanta.. bata iya hango yarinyar sosai saboda duhun da gari yayi.. a hankali ta buɗe door din side dinta sannan ta sauka ta mayar ta rufe, cikin sauri ta tsallake titi sannan ta qarasa inda yarinyar take, batare da tsoro bah .. tana isa tace"Salma"..

 a firgice Salma ta mik'e tsaye tana xaxare ido saboda tsoron daya mugun kamata sanadiyan muryan mutum dataji akanta.. hasken wani mota dayake wucewa ne yayi reflecting fuskan aunty husna, hakan ya sanya Salma ganin fuskarta, murmushi ta sake sannan tayi maza ta rungume aunty husnan, hawayen farin ciki na xubowa ta cikin idanunta.. a hankali aunty husna tashiga patting bayanta tana lalashinta da kalamai masu ratsa xuciya.. sake juna sukayi tana kallon Salman tace"hope ba abun daya sameki? Kyaɗa mata kai Salma tayi, kamin su tsalake titin atare xuwa inda tayi parking mota... Ba wanda ya kuma cewa komai har suka isa gida..

   xaunar da ita tayi akan sofa sannan tashiga kitchen ta ɗibo mata abinci acikin plate ta bata.. carmly Salma ta amsa abincin sannan tashiga ci tana mai sauke ajiyar xuciya saboda kukan dataci.. maida plate din kitchen tayi, sannan ta dawwo ta xauna a inda ta tashi fuskarnan nata ya koma ja, ga idanunta dasuka kumbura.. kallonta Aunty husna tayi cikin kulawa tace"mai ya haɗaki da shi har ya sauke ki Salma? Tana wasa da fingers dinta tace" walahi ban masa komai bah, kawai daga cewa ya rage kudun motan am feeling scared shine yace in sauka masa a cikin mota". Ajiyar xuciya aunty husna ta sauke tana mai jin haushin abun da Umar yayi har cikin ranta, cikin sanyi tace"kiyi hakuri kinji, but you could have beg him, Bai kamata ace kin biye mashi ba kema, da baki sauka a motan bah" share hawayen Dake fuskanta Salma tayi sannan tace" I was scared, naga yayi fushi ne a lokacin". Murmushi aunty husna tayi dan Koh ita tasan yanda Umar ke canxawa in har yyi fushi carmly tace"tashi kije kiyi sallah, nasa su ummu su kai maki kayan dakuka siyo ɗakinku.. gyaɗa kanta tayi sannan ta miƙe xuwa ɗakin nasu...

Da safe tana wanke wanke a kitchen ta sinkayo muryan Umar a parlor Yana yima su ummu lesson. Kasancewa ya'u ranan weekend ne.. tsaye tayi a kitchen din Jin muryansa har yanxu acikin parlon, Dan harga Allah tsoron haɗuwanta dashi takeyi she don't know why tsoron datake masa yakara nunkuwa fiya da na da".. buɗe kofan kitchen din akayi aunty husna tashigo ciki tana kallon Salma dake tsaye tana facing kofan tace''lafiya na ganki tsaye, kinƙi fitowa parlor".. girgixa Kai Salma tayi cikin i'ina tace"uhmmm daman...inason fitowa..yanxu ne".. girgixa Kai kawai aunty husna tayi sannan ta qarasa ta dauki container gishiri sannan ta fice daga kitchen din batare data kuma cewa komai bah... Ajiyar xuciya Salma ta sauke bayan ta wuce, tana dafe k'irjinta ta qaraso door din kitchen din tana gathering courage, duk da yanxu ta daina jin muryansa acikin parlon.. hannun tasa a handle din kofan sannan ta buɗe, clashing sukayi dashi abakin kofan kitchen din. ... . xaro manyan idanunta tayi, xuciyanta na bugawa, kallonsa takeyi kamar yanda shima din ita yake kallo babu Koh blinking.. ita tafara dauke kanta, tayi baya kaɗan saboda kusancin nasu da yayi yawa.. yunkurin bin gefensa tayi ta wuce, Amma ya tare gurun da arm dinsa, hakan ya sanyata ɗago manyan idanunta ta axa a oily eyes dinsa Dake cike da kaifi dakuma kwarjini... Kamar xaiyi magana sai kuma yayi Shuru ya matsa gefe, hakan ya sanyata wucewa har tana tuntuɓe, Straight ɗakinsu ta nufa..

UmmusalmaWhere stories live. Discover now