💝💝 Ummusalma 💝💝
Free page
#11
Umar
Direct cell ɗin gidan daddy ya umarce sojojin dasukaishi su rufe.. sai dasukayi da gaske kamin su iya shigar dashi cikin cell ɗin, suka fito sannan suka rufe da key. Lumshe idanunsa yayi, yana mai riƙe kansa dake barazanar tarwatse masa. Bin cell ɗin da kallo yayi, yana mai jinjina kansa. Dan idan bai manta bah, kusan shekara biyu kenan rabonsa da wannan ɗakin... Zaune yayi a ɗakin yayi Shuru, duk abun duniya ya ishesa, cos ba abun dayake tunawa sai club ɗin da yayi ma Sadiq alkawarin zuwa ya'u, he even promise to pay their bill, yanxu ya xasuyi. Ya tambayi kanshi. Lumshe idanunsa yayi, zuciyansa na xafi, gashi duk jikinsa yayi tsami, saboda dukansa da Sojojin sukayi... Ana kiraye kirayan sallan magariba daddy ya buɗe cell ɗin ya shigo, alokacin Umar was taking a nap Dan Bai Masan da tsayuwan mutum a gurin bah, Saida yaji karan buɗe kofa. A firgice ya buɗe lumsasun idanunsa, staring straight into his dad. Qarasowa ciki daddy yayi, sannan ya ajiye kettle daya shigo dashi. Carmly yace" ga buta nan, ka tashi kayi alwala, sannan kayi sallah, amma karkasa ran za'a kawo maka abinci, cos acikin punishment ɗinka, there is no food for you today, saidai gobe" sauke idanunsa dasuka janxa kala daga kallon uban nasa yayi. Cikin sanyi ya dauki butan ya fita nan bakin kofa yayi alwala, batare dayayi yunkurin guduwa bah, dan inma yayi gigin barin nan, jikinsa ne kawai zai gaya masa, dan gidan zagaye yake da sojojin da sukafi na jiya yawa , and gashi yanxu sun daina jin tsoron sa. Yana iddarwa ya shigo ciki, ya nimi gefen dake da ɗan dama dama yafara gabatar da sallansa. A hankali daddy ya mike tsaye ya fita daga cikin ɗakin sannan ya mayar ya rufe kofan da key, kamin ya fice...
Washegari da asuba daddy ya shigo cikin cell ɗin, riƙe yake da touch light, saboda duhun da ɗakin yayi Dan d'akin baida boob.. Qarasawa inda Umar ke zaune yayi, sannan ya tsuguna yana kallon Umar da idanunsa ke lumshe kamar yana bacci, while by ba baccin yakeyi bah, cos kwata kwata kasa runtsawa yayi da dadare, he couldn't sleep because of yanda sauro keta cixonsa. Hakan ya sanya jikinsa yayi week, cos ga cizon sauro ga kuma dukan daya sha jiya.. kallon fuskarsa daya koma ja abunka da farin mutum, baban nasa keyi, yana mai girgiza kansa.. cikin taushi ya kira sunansa. Hakan ya sanya Umar ya buɗe idanunsa, Amma lokaci ɗaya ya maida ya rufe saboda hasken touch light Dake reflecting idanunsa .. hakan ya sanya daddy juyar da kan tocin ya zamana yana kallon wani gefen.. cikin kamewa daddy yace " ka tashi, ka koma ɗakinka, inkayi wanka ka gyara jikinka sai ka fito masallaci"
xaro oily eyes dinsa yayi jin abun da daddy yace, cikin sanyi yace " thank you so much daddy" tab'e Baki daddy yayi sannan yace " but karkayi tunanin escaping, dan walahi bazan dubi kai ɗana bane, I will just allow them to shout you if you try excaping" shi dai Umar Shuru yayi yana kallon uban nasa, shidai ba abin dayake da bukata irin ya sakar ma kansa shower Koh yasamu sauƙin tsamin da jikinsa yayi masa ..... Ficewa daga cell ɗin daddy yayi sannan ya bar kofan a buɗe....
Da kyar Umar ya iya miƙewa tsaye let's talk about yanda yaketa jan kafansa zuwa main entrance din gidan... Yana cije leɓe ya tura kofan parlon.. a hankali ya sanya kafa cikin kayatacen parlon, dayasha ado ga funitures kaikace ba'a Nigeria kake bah. Wata dattijuwan matace chocolate color, dabaxata haura shekaru arba'in bah.. zaune take akan sofa tana jan jasba'a, sanye take da hijabi dogo har kasa. Da mamaki take kallonsa, cikin nuna kulawa tace " Umar, daga ina kake cikin wannan lokacin? Koh kallon direction ɗin ta beyi bah, ya haura upstairs. Sauke idanunta daga kallonsa tayi, tana me girgixa Kai..
Yana Qarasawa ya tura kofan wani hadadiyan daki daya kawatu da funitures komai nashi purple Umar ya shiga.... Bin ɗakin dayake share saf, kamar akwai mutum aciki yayi da kallo, a hankali idanunsa ya sauka kan hotunansa dake mane a ɗakin, murmushi ya sake a daidai lokacin da idanunsa ya sauka kan wani hoto, lokacin yana ɗan karaminsa, yana mane jikin wata mata datayi kama dashi, da alama she's their mother, sai aunty husna , dake mane da daddy.. sauke idanunsa daga kan hotan yayi, jiki a matce ya shiga closet dan tuɓe kayan dake jikinsa.. yana fitowa ya faɗa toilet batare da ɓata lokaci bah.. daure da towel ya fito, Koh shafa mai beyibah, ya karasa cikin closet, xura jalabiya yayi ajikinsa, sannan ya fito ya shimfida sallaya ya tada sallah, cos baya tunanin zai iya takawa a yanda yake ɗin nan, zuwa masallaci, dan sema sojojin sumashi dariya.... Yana iddarwa ko axkar bai tsaya yayi ba, ya faɗa kan gado....
YOU ARE READING
Ummusalma
RomanceThirteen year old salma has been through a lot in the past, from losing her parent, to then having an aunt that wasn't too fond of her. Beat after beat and punishments, after the next, she still pulls through.