Part 2

3 0 0
                                    

💝💝Ummu salma💝💝

  By salma zakariya

Free page


#2

Zaune take acikin Dan madai dai cin d'akin su, staring into space, tana tuna nin, how her life turn to be like this All of a sudden.... Murmushi daya Fi kuka ciwo tayi tana tuna lokacin da take tare da iya yanta abin kaunarta ke Raye...she always get what she wants, Koda kuwa Daddinta Bai da kud'i, sai mommy ta Siya mata, she always eat what she want, ta Sanya kaya Mai tsada Sannan taje makaranta Mai tsada which is private school.... Kallon kayan Dake jikinta tayi da Basu da banbanci da rags. Wasu hawaye masu zafine suka gangaro daga cikin idanunta, tana tuna lokacin da gwaggo ta Tatara kaya yakinta bayan rasuwan iya yanta ta siyar dasu, a cewanta wai zata sanyata makarantan islamiya dashi, Dan Bazata iya zama da d'iyar arniya ba haka kawai bah...... Salma salma ta tsinkayo muryan gwaggo tana kwalla mata kira..... A razane ta dawo daga duniyan tunanin data shiga, cikin sauri ta mike tsaye ta fito daga dak'in bayan ta share hawayen Dake fuskarta..... Kallon gwaggo data hade giran sama data kasa tayi kamin ta amsa cikin siririyar muryanta tace"na'am" kallon up and down gwaggo tayi mata tace"uban me kikeyi a dak'i bayan nace ki Tatara kayan wankin hafsa ki wankesu fess.... Kallon gwaggo tayi dawani iron expression Sanna tace" banfa karya har yanzu bah" a tsawace tace" idan kina son kici abinci a gidan Nan Kam sai kin gama wankin tukunan" idanuntane ya taro kwalla a hankali tace" gwaggo bazan iya komai ba, batare da naci komai ba and ni bazan iya wankin batare da naci komai ba " and ni bani ya ma wanki ba " ta karashe maganar hawaye na gangarowa cikin

 idanunta ..... Ko tanka mata gwaggo Bata yiba ta janyo Wani karamin kujere Dake kusa da ita, ta zauna Sannan ta dauko fatan doyan da ta ajiye, Bud'ewa tayi ta fara ci hankali kwance.... Turo kofan gidan akayi, Wanda Hakan ya Sanya gwaggo Mai da hankalinta wajen.... Wani datijo ne ya shigo cikin gidan bakinsa dauke da sallama...... Amsa sallama nasa gwaggo tayi sannan ta mike tsaye ta dauko masa ta barma ta shimfid'a masa tana washe hakora tace"sannu da dawowa" zama yayi kan tabarmar yana fad'in yawwa" Dan kallon abinci datake ci yayi sannan ya Maida dubansa ga salma Dake tsaye har yanzu tana matso kwalla.... Tabe Baki yayi yana Maida dubansa gun gwaggo data hak'ikance sai kwasan fatan ta takeyi tace" ita Kuma wanna maiyar Mai Akai mata take kuka? Ajiye abinci Dake hanunta tayi tana lashe yatsun hanunta tace"kyale yar iska" tabe Baki tayi ta kara da"Makita, wanki nace tayi, tace ita Bata iya ba... Niko nace ba ita ba abinci ya'u in har batayi wankin ba, Dan ya'u hafsa Bata da kayan sawa" lashe Baki yayi yace" shareta Dan Allah, uhmmm zan samu sauran fatan, in Dan lasa? Tsuka gwaggo taja, batace komai ba, taci gaba da cin abinci ta, yayin da Salma ta taka a hankali ta koma cikin dak'in nasu, Dan kwaso kayan wankin hafsan.....Kallon gwaggo yakeyi yayi kasa da murya yace"haba uwargida na, abin farin cikin isuhu" washe hakora tayi tana fad'in "lalai Mallam, wato ni zakayi ma dad'in Baki? Ni abin farin cikin Kane fa kace" Dan girgiza kafafunta tayi sanan ta kara da "shine ka tashi ka daukomin, wata macen da Sunan kishiya"kad'a Kansa yayi yana fad'in" bazaki Gane bane saude, ai ke kanki kinsan cewa ke kadaice macen Dana ke ji da'ita duk fad'in duniyan Nan, saboda kwawawan halinki" kankance idanunta tayi sanan tace" Mallam dubeni Nan "kallonta yayi yana Dan marairaicewa fuska tace" idan wanna doyan ne yake tsole ma Ido, to gwanda ma tun wurri kacira ran cinsa, Dan wallahi, kadaiji rantsuwan musulmi Koh, toh bazan baka bah" Dan zaro idanunsa yayi yana Mai sa sauta murya tace" toh shikenan ai duk yanda kikace"marairaice fuska yayi tace" Dan Allah, Koh sauran tuwo bazan samu ba, Dan waccan kazamar ba abin data cika ni dashi ya'u tun safe dashi sai masifa da bala'i.... Cin abincinta taci gaba dayi batare da ta Kuma ce dashi komai ba, yayin da shikuma ta barshi da had'iye miyau, kamar Wani sabon maybe.... Kallon kwanun abincin yayi tace"yanzu saude, ko loma daya bazaki bani bah? Tatara sauran ragowan dayayi saura cikin kwanun tayi sanan ta zubasu a bakinta ta cinye shi tas.....

UmmusalmaWhere stories live. Discover now