Part 4

1 0 0
                                    


💝💝Ummu salma 💝 💝

By salma zakariya

Free page


A hankali ta shiga takowa cikin tsakar gidan zuciyanta na bugawa.... Tana Kallonsu tace"Ina kwana" a takaice biyu daga cikinsu suka amsa da "lafiya Lau" Daman su biyar ke tsaye a gurun, sai ita datake zaune, data fara ganin salman...

Sauke buhun gwanjon Dake kanta tayi staring into them tace"in bud'e maku kugani?

Gyad'a mata Kai siririyar tayi batare datace komaiba... A hankali tashiga warware d'arin da matarnan tayi mata, d'ago manyan idanunta tayi bayan ta gama kwancewa ta kallesu, Suma kallon nata sukayi....

Mikewa matar Dake zaunen Nan tayi har tana watsi da b'awan gyad'a datake barewa ta qaraso gurun Salman... Dugawa kasa tayi tasa hannu ta dauki gwanjon kamar wacce taga kayanta datake Nima.... Da sauri Suma sukayi kanta Suna ribibi harda Ture juna sukeyi, banda siririyan cikinsu, data tsaya atsaye Baki bud'e tana kallon su, ta rasa Mai ke damun matan gidan, da inhar suka ga gwanjon kaya toh fa kamar an biya masu hajji ne... Dragging buhun suka fara yi, har dankwalayen wasu na fad'uwa kasa, but they didn't even turn to look at it, balai ace su dauka su daura Akai kuma...

Waro idanu Salma tayi ta rasa abun Yi, daga karshe dai tayanke hukuncin yin magana, smartly da Dan karfi tace"ni kubani abuna, nama fasa siyar muku da kayan" 

Lokaci d'aya ko wacce ta dawo cikin hayacinta..... A hankali Salma ta Tako har inda wacce ke rike da buhun take, sannan ta Sanya Hannayenta a hankali ta kwace buhun... Tatara kayan daya Dan zube a kasa garin ribibin nasu tayi, sannan ta sanyasu cikin buhun, tashiga daure wa" tana gama daurewa ta Kalli matan Dake kusa da'ita sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi kamar wacce tayi race, a natse tace" Dan Allah Koh kin taimaka ki aza ni? Ajiyar zuciya Mai karfi matan ta sauke tana faman hura hanci tace"yanzu baza ki siyar din bane? A hankali Salma ta gyad'a mata Kai idanunta na observing dinsu... Da sauri matar Dake zaune a tabarman Nan tayi gurun tabarmar...Hannu ta sanya ta zubar da b'awan gyad'a, sannan ta juyo ta dawo gun Salma ta shimfid'a tabarmar tana kallon Salma murya can kasa bakamar d'azun datayi using harsh tune ba tace"d'iyata zo ki zuba su a tabarmanan sai kowa ya zab'a'' kallonta kawai Salma tayi batare da tace komai bah... 

Ganin har yanzu Salman Bata sauko daga fushin datayiba yasanya matan cewa"yi hakuri ki zuba, na maki alkawarin, ba wacce ta Isa tayi iskancin dasukayi d'azun ....

Murmushi Mai kyau Salma tayi tana kallon matan, a zuciyanta tace"sai kace ba ita ta fara jawo abun dasukayi d'azun din bah.... A hankali batare data bar kallon matan bah tace "Mai zai Hana in yita fito maku dashi, Kuna Gani, cos if aka zuba a tabarmanan, bazan iya ganin iya Wanda ya dauki kayan bah"...... Ajiyar zuciya matan ta sauke tana kallon sauran matan ta gefen Ido tace"yar Nan zuba kawai ba abun da zai faru, I have a daughter like you, Kuma bazan so ayi mata Abu mara kyau ba, Dan haka ni da Kai na zan sanya masu Ido, inga yar iskar da zata cuceki"... kallonta sauran matan sukayi, da D'an d'aga murya sukace" kece dai yar iskar badai muba" tabe Baki siririyar Dake tsaye a gefensu tayi sannan ta bar wurun batare data ce dakowa komai bah.... 

A hankali suka shiga zaban kayan daya masu, Suna biyan kud'in...... Sai binsu da kallo Salma keyi, Dan bata manta kashedin da gwaggo tayi mata bah.. kusan Rabin kayan suka siye, sannan ta daure sauran dayayi ragowa..... Aza mata kayan sukayi sannan ta fice daga cikin gidan.....

Karfe hud'u Daidai ta dawo gida, jikinta duk amatce saboda, yawo da Kuma shiga ranar datayi....a zaune ta Sami gwaggo da Mallam isuhu,Suna magana murya kasa kasa.... Qarasowa tayi ta zube a kasa tana kallon gwaggo a hankali tace "gwaggo na gama siyar da dukka kayan..... D'ago Kai gwaggo tayi tana washe Baki tace" a'a lalai, ya'u kace Salma tayi abun kirki" kallon Mallam da yake mata kallon tambaya tayi sannan tace" uhmm, ban gaya Maka ba, yanzu mun fara san'an gwanjo" gwalalo idanunsa yayi Yana fad'in" kace ya'u, Muna da Shan jar Miya acikin gidan Nan" hararanshi tayi tace" da Wani kud'in zaka Sha jar Miyar? Shuru yayi Yana wiki wiki da Ido kamar mara gaskiya yace"wasafa nakeyi" Yana gama fad'in haka yaja bakinsa yayi Shuru..... Kallon Salma gwaggo tayi sannan tace "kin zubamun Mayon idonki, kamar wata sabuwar mayya, bazaki mikomin kud'in bah" Ciro kud'in data b'oye acikin hulanta, Salma tayi sannan ta Mika mata cike da ladabi.... Amsan kud'in tayi,kamin tashiga g'irga kud'in hakuranta a washe......Dan Jim tayi bayan ta gama g'irga kud'in..... D'ago Kai tayi fuskarta na nuna Wani irin expression...... 

UmmusalmaWhere stories live. Discover now