Aysha Adam Alhassan Ɗan Fulani
Women Writer's Association
_Munkasance a cikin duniyoyi mabanbanta masu cike da abubuwan birgewa da ban sha'awa, na taso cikin tawa duniyar da bansan kowa ba bansan wacece ni ba, a mafarki mai kama da zahiri na ke jin kamar ina da wasu a hali, ina jin ni ma kamar ina da ƴancin a rayuwata, kash sai dai bansan kowa cikin rayuwata ba,ko wanne ɗa'a na samun kulawa irin ta uwa, amma ni tun da ga fara wutsil-wutsil ɗina a cikin mahaifiyata madadin shafawa da lallashi irin na uwa, ni duka da tokari nake samu, na rayuwa da wusu hallitu waƴanda na kasa tantance ni ma irinsu ce ko ya ya?._
Shafi na farko(1)
Zaune take a gafen ƙuɗiɗɗifin da ke ta tumbatsa da ruwa, yai kasa yai sama sai hausina ya ke ya na yi kamar zai zubo waje. Kallan ruwan take ta na hango wani abu a sama sai sheki yake yi, ƙafafuwanta ta zura cikin ruwan wai-wayawa tai da sauri jin kamar ana kiran sunanta ganin babu kowa ya sa ta sake mai da hankalin a gurin kwallon da ke sheki a saman ruwan. Ganin kwallon na tahowa gareta ya sa ta kyalkyalewa da wata irin dariya mai cike da zumudin san kwallon ta ƙara so in da ta ke, chak kwallon ta tsaya a tsakiyar ruwan ta na jujjuyawa tai sama tai kasa. Kallan ruwan Aira ta yi taga ya dena hawa ya na sauka se dai-dai inda kwallon ytake ya ke hawa, ƙafarta da ke cikin ruwan taji kamar ana mata susa a tafin kafarta, dariya ta saki ta na jin dadin susar ƙadangare da a ke mata a cikin ruwan. Dago kafar tai da sauri ta na kyalkyalewa da dariya, mai da kafar ta sake yi taji ruwan ya koma kamar siminty ga ruwan ta na gani amman ya daskare a kafarta a ido kuma ruwa ta ke gani. Miƙewa ta yi ta taka kafar a cikin ruwan taji lafiya ƙlau take takunta ba tare da ruwan ya ja taba, tafiya ta ke zuwa wurin kwallon da take sama da kasa, ta na karasowa wurin ta ga ruwan ya yi matattakala. Da sauri ta dauki kwallon zata juya zuciyata na raya mata ta shiga taga me ke cikin wurin, kin bin zuciyarta ta yi ta juya da niyyar komawa ta ji sautin muryar mahaifiyarta na kiranta juyawa ta yi dan jin in da sautin ke fitowa ta ga daga wannan matattakalar ne. Chak ta tsaya tabi wurin da kallo zuciyarta na bata shawara ta bi kilah mamanta nan take zuwa daman ta barta a chan tai ta nemanta. Amincewa tai da shawarar zuciyarta ta, fara ta ka wurin tai ta na shiga. Ba tayi aune ba ta ganta cikin wata kyakkyawar alƙarya mai daukar ido, wurin ya yi mafisar haduwa idonta ta kai sama taga babu koda ɗigon ruwa a wurin mamakine ya shinfiɗu a fuskanta to ina ruwan da ya kawo ta wurin ya ke ta tambayi kanta, ganin babu wanda zai amsa mata ya sa ta sake fiddo ido waje ta na duban wurin da kyau dan karewa kyakkyawar alƙaryar kallo. Korayen gayenne suka ƙawata wurin tare da jan furanni masu kamshi, idonta ta kai duba waurin wani tsauni mai kyan gaske ruwa ne ya ke sauka ta wurin sai wata faffadar gada wacce a kayi wa ado da furarrni masu daukar ido, takawa take zuwa wurin ganin gilmawar abu ya sa tai saurin juyawa, chak ta tsaida dubanta a kan kyakkyawar fuskar matar da ta gani, mamaki fal ranta ta furta "Nu'aima nan ne garinku dama?".
Murmusawa wacce a ka kira da Nu'aima ta yi ta na takowa inda Aira ke tsaye,karan hancin ta ja ta na fadin " kullum burin ki kibiyoni kizo kiga inda ni ke rayuwa, shine yau na zabi wannan hayar ta kawo ki cikin a halina idan kin shirya biyoni muje abar kauna"."Ooohhhh!" Aira ta furta ta na bin bayan Nu'aima da sauri ganin ta doshi wurin da gadar ta ke ya sa ta kara sauri ta na fadin "ki tsaya sauranki ya yi yawa kin ga bansan hanya ba".
Jin haka ya sa Nu'aima tsaya chak ta na jiran karasowar Aira, nufar kan gadar sukayi a tare Aira se kalle-kalle takeyi tunda ta ke a rayuwarta wuri ɗaya kawai ta sani shine bukkar da suke rayuwa ita da mahaifiyarta, jin an riko hannunta ya sa ta dawo da kallanta ga Nu'aima. Sake baki tayi ta bi wurin da kallo ganin wasu irin hallitar na ta kai wa da komowa saurin ƙanƙame Nu'aima ta yi jinkinta na kyarma, cikin rawar baki ta ke fadin"Wayyo Allah ina ne nan wace irin duniya na shigo ni Aira inallilahi wa'iinna inaili raji'un ta sa ke furtawa a kideme ta na sa ke ƙanƙame ganin wasu yara da suke dabda kasa suna tun karo, rudewa ta sake yi ganin yaran sun tashi sama suna mata dariya.Fulani ce
Comment
Share
Free page.
YOU ARE READING
MAKIRCIN CIKIN GIDA
Spiritual_Munkasance a cikin duniyoyi mabanbanta masu cike da abubuwan birgewa da ban sha'awa, na taso cikin tawa duniyar da bansan kowa ba bansan wacece ni ba, a mafarki mai kama da zahiri na ke jin kamar ina da wasu a hali makusanta, ina jin ni ma kamar ko...