Aysha Adam Alhassan Ɗan Fulani
@Women Writer's Association.
Shafi na Hudu (4)
Ganin ya kasa furta komai ya sa ya chanza kalaman bakinsa wanda wannan karan ya samu nasarar furtawa ya na fadin "Har kindawo daga school din?".
A tsiyace ta kalleshe ta furta "kwarai kuwa".
In da matar yayanshi take ya duba ya ce Anty Nablah barka da gida, ya yara dereba ya dauko su daga makaranta ko?"
Washe haƙwara tayi ta na kara boye kudin hannunta wanda a tunaninta bai gani ba, tsaki ya ja a kasan zuciyarshi ya nufi kofar ɗakin nasu, ya barsu a tsaye. Ya na shiga yaran suka fara "oyoyo Abiee". Rungumesu ya yi zuciyarshi babu daɗi, wurin zama ya makansa a kujera mai zaman mutum ɗaya, babbar cikinsu wacce bazata wuce shekara goma ba ta ƙara so ta zauna gefenshi ta na fadin" Dady tare da momy ku ka dawo, tunda muka dawo daga school ba mu sameta ba".
Lumshe ido ya yi ya na duban Khadijah babbar ƴarsu, hadiye wani malolon bakin ciki ya yi ya furta" Ta dawo ta na wurin Momy Nablah kuje kuyi mata sannu da zuwa. Da gudu suka fita su uku ne yaran mata biyu na miji ɗaya, Khadijah, Suhaima se Abubakar ta kwaran Baffa mahaifinsa. Miƙewa ya yi jin zuciyarshi kamar ba za ta dauke shi ba, ɗakin shi ya nufa yasa mukuli ya bude, ya na zuwa ya fada kan gado sai juyi ya ke tambayar kansa ya ke shin meyasa a duk sanda Alina zata taka dokar Allah da abubuwan rashin kyautatawa ya ke kasa yi mata magana wanna wani irin iftila'ine.
Inallilahi wa'iinna inailihi raji'un, ya ke ta furtawa wanna wace irin masifah ce, tinani ya soma yaji still kansa ya fara masa kuɗa da wani irin juyi kamar zai fita a gangan jikinsa, dafe kansa ya yi da sauri ya na sake ambaton Allah. Miƙewa ya yi da sauri ya dauki mukulin mota da sauri ya bar ɗakin dan ji yake kamar duk gidan haka yake, baibi takan Alina da ke zaune a falo ba ya fito ya nufi wurin motar sa.
A gaggauce ya shiga motar yai mata key bai zame ko'ina ba se gidansu, ya na shiga ya iske Baffa na daura alwalar magriba da hanzari ya ƙarasa kusa dashi ya tsuguna, ya na tsuganawa Baffa ya miƙamai butar ya na fadin" daura alwalar muje masallaci amma lafiya na ganka kadawo ko kayi mantuwa ne?".
Girgiza kai kawai ya yi ya daura niyya tare da fara gabatar da alwalah, ya na kamallawa suka nufi masallaci, da ya buɗi baki da niyyar sanar da Baffa halin da a ke ciki se yaji kamar an daure mai baki, koda suka idar da sallah tambayar duniya Baffa ya mai a kan ko lafiya amma yai shiru se dai ya ce lafiya kwai ya dawo suyi sallah ne.AIRA
Hannunta da ke cikin na Nu'aima ta sake ƙanƙamewa saboda jin yanayin ta ke babu ɗadi sam, ta so Gimbiya Mulaika ta labarta mata wani abu daga cikin labarin ta amman sam bata samu hakan ba, toh yanzu kenan dama wani daliline yai sanadin zuwansu nan dajin. Jin murya mai dan girma na kiran sunanta ya sa tai saurin dagowa ta na duban inda a ka kira sunan nata, SARKI LULUWAIDA ya ke kiran sunanta bayan zamansa a kan kujerar mulkinsa, Nu'aima ce ta raɗada mata a kunne kije gurinshi ya na son ya yi magana dake. Miƙewa tai ta ƙarasa gaban shi ta ɗurkusa har kasa kamar yadda tai wa Gimbiya, gaisuwa ta miƙa ta cigaba da tsuguno, hannayensa ya saka ya dagota ya na sakin mata murmushi, itama murmushin ta mai ya zaunar da'ita a kusa dashi, hannu ya daga sama sai ga shi ya dawo da wata kwarya ya miƙa ma Aira, ya na fadin "Amshi ki shanye a bin da ke ciki".
Babu musu ta kai hannu ta amsa kwaryar madara ce a ciki sai kamshi ta ke kafa kai ta yi ba ta dagoba sai da tashanyen tas sannan ta miƙa kwaryar, wani irin dadi da gardi taji madarar na mata a baki lumshe ido tayi ta na jin dadi ya na lulubeta ta ko wani lungu da sako na jikinta. Jin muryar Sarki ya sa tai firgigi ta bude idanuwanta a kan Lulu'aida da ke fadin "Wanna madara da ki ka sha maganin tsarice babu wani mahalukin da ze iya cutar dake a doron duniya zan baki wani wani magani ki dinga sawa mahaifiyarki a cikin abin sha in Sha Allah da sannu zata dawo hayyacinta, yanzu yanma ta yi ki tashi Nu'iama zata rakaki gida nan da zuwa wani ɗan lokaci ƙadan zata kawo miki magani mahaifiyarki, ta shi ku tafi mahaifiyarki ta dawo ta na ta neman ki maza kuje Nu'aima".Godiya AIRA tai ma Sarki Lulu'aida sanna ta dawo gaban gimbiya ta zube nan ma ta kwashi wata godiyar, riko hannunta gimbiya tai ta zura mata wani siririn zoben zinari mai kyan gaske, murza hannun ta yi tace "babu ke babu bacin rana in Sha Allah sharri dukkan abun hallita ya tsallake kanki amma duk da haka ki dinga ya waita addu'ar da Gimbiya ke koya miki hakan zai matukar tai maka miki kinji ko".
Godiya ta sake wa gimbiya ta miƙe suka fito kamar jira Nu'aima ta ke tai saurin fadin" kinga al'ƙaryamu ko? Mutafi a ƙafah ne ko k a iska, wanne ki ka zaba a ciki".
Waro ido ta yi ta na fadin "Iska!" ta na dafe sai tin zuciyar "kai Nu'ima ta ya ya zamuyi tafiya a kan iska ko dai so ki ke ki tsorata ni"."Taya zan tsorata ki bayan dazun ma kin mance a kan iska muka shigo fada".
Riƙe baki tai ta na mamaki tabbas se yanzu ta tuna cewa sun fara tafiya a ƙafah ta hadu da wasu yara ƴan mitsilaye masu lafta laftan kunne, tsoratar da tayi ya sa Nu'aima daukarta a iska, dafah kafadar Nu'aima tai da sauri ta na fadin "YAwwa tambaya ƙawata, lokacin da muka shiga masarauta na ga hallitarki ta koma irin ta mutanen wurin yanzu kuma da zamu fito kin koma Irina wai ku na chanza kamanni ne ko kuma riga ku ke sakawa ne? Ni ban gane ba wallahi".Fulani ce
Comment
Share
Paid book ne Naira dari uku (300), 6322646280 Aisha Adamu Fidelity Bank. a turo da shaida ta wannan number 09064234445 idan kuma kati ne a turo shima ta lambar
Free page.
Page 4
YOU ARE READING
MAKIRCIN CIKIN GIDA
Espiritual_Munkasance a cikin duniyoyi mabanbanta masu cike da abubuwan birgewa da ban sha'awa, na taso cikin tawa duniyar da bansan kowa ba bansan wacece ni ba, a mafarki mai kama da zahiri na ke jin kamar ina da wasu a hali makusanta, ina jin ni ma kamar ko...