Aysha Adam Alhassan Ɗan Fulani
@Women Writer's Association.
Shafi na Uku (3)
Garin Kaduna garine mai cike da wayayun mutane masu ji da kudi da ilimi, kan babban titin da Ahadmu Bello ya ke murza sitiyarin motar ya na sakin mata murmushi, lumshe ido ta yi ta buɗe su fes a kan lafiyyar kwaltar da ke mammale a kan titin yana ta zuba sheki. "Baby!". Ta kira sunan shi cikin wata irin murya wadda ta jiƙu da qaƙale, "ka kaini bakin layinmu ka ajiyeni da ganan zan ƙarasa gida ba se ka kaini gida ba".
Juyowa ya yi ya dubeta ya ce pretty me yasa ki ke san wahalar da kanki ne ki bari na karasa dake mana haba babyna".
A jiyar numfashi ta sauke wanda iya ita kadai take jin hakan, zance zuci ne ya debeta ta na fadin "bazaka ganeba gara dai a rabu a nesa yafi mana alheri". A fili kuwa ƙaƙalo murmushi ta yi ta na fadin " No baby akwia in da zan ɗan biya ne kafin gidan shiyasa plz kaga ma mun ƙaraso sauke ni kwai nan ma ya isa".Umarninta ya bi ya sauketa sukayi bankwana, kudi ya ciro bandir ɗaya yan ɗari biyar biyar ya miƙa mata, hannu biyu tasa ta karba ta na fadin "kaima ka shiga bank ne dan naga new cormas ne".
Kaɗan ya yi murmushi ya ciji lips dinsa, fisgo maganar ya yi da kyar ya furta " manajan bank din ne ya kawo mun har gida ina ni ina wahalar da kaina a kan wasu sabbin shigowa ai muna zaune suke zuwa inda muke, yar ɗari biyu ɗari ce zata rabaki da mutane yanzu, kudin hannunki zasu isheki ko kina bukatar ƙari?".
Tunda motar ta tsaya ya zuba musu ido ya na da ga nesa da su yana kallan sarautar Allah, dam gabanshi ya fadi duk da ba wannan karan bane na farkon ganin shi da Alina tare da wani, wani irin tuƙuƙƙi ya ke ji a zuciyarsa wacce take dukan tara-tara kamar zata faso kirjinasa inallilahi yai saurin furta a lokacin da ya ga mamalakin motar ya sake zuro hannu ya na ƙoƙarin riko hannu Alina matarshi, a zabure ya furta"Wayyo Allah na ni Mashkur wanna wacce irin masifah ce take dawainiya da ni a rayuwata inallilahi wa'iinna inaili raji'un, ya Allah ka shiga cikin al'amarin a Allah ka dubamin ba dan iya wata ba". Ganin taja baya da sauri ta na dariya tai hanyar get din gidansu ya sa yaji ya fara samun sauki daga zufar da take keto mai a dukkan sassan jikinshi.
Dafe kanshi ya yi wanda ke sarawa babu bata lokaci, inallilahi wa'iinna inailihi raji'un ya dinga furtawa a gaggauce har sai da yaji sassauci sannan ya daina furtawa a kan labbasa ya koma ambaton kalmar a cikin zuciyarshi.Kwankwasa kofar motar da a keyi ya sa shi sauke wani nauyayyen a jiyar zuciya ya kai hannu ya bude ya na duban Sofiyan dake tsaye a ya na miko mai takardun da ya dauko daga cikin gidansa,murmushi ya ƙakalo ya daurawa fuskarsa dan kaucewa tuhumar tashin hankalin da fuskar ta bayyana a ƴan daƙikun da busu wuce second goma ba, amsa ya yi yai mai godiya suka kai sallama ya ja motar shi da kyar dan ji yeke kamar ana tsinke mai jiniyoyin jinkinshi haka ya ƙarasa gidanshi wanda ya kasance nesa da Sofiyan kadan dan ta zarar bata fi ta gidajeje shida ba a tsakinsu......Sauri-sauri ya ke ya ƙarara gida dan ya sauke wa Alina ruwan rashin mutuncin da ta debowa kanta, parking ya yi bayan me gadin ya bude mishi get, cikin gidan ya nufah yaji wata irin faduwar gaba na dirar mai a zuciya. Shiga ya yi cikin gidan hangota ya yi a kofar ɗakin Nablah ta na mika mata kudi, buɗe baki ya yi da niyyar tambayar ta daga ina take amma sam ya kasa, ji ya yi bakinsa kamar an daure mai, ya ilallaihi ya furta a ƙasan zuciyarshi tambayar kansa ya ke me yasa a duk sanda Alina za tai wani abu na rashin darajawa idan yazo zai mata magana bakinshi se ya kulle gaba ɗaya ya kasa furta ko da kalma ɗaya.
AIRA
Takawa sukayi har gaban gimbiya Mulaika, ganin Nu'ima ta tsuguna ya sa Aira saurin yin yadda ta ga tayi itama, gaisuwa suka mika a tare suka tashi wurin zama Nu'aima ta nuna wa Aira sannan itama ta zauna kusa da'ita.
"Aira!" Gimbiya ta furta cikin wata irin murya me sanyi "A yau kinshigo cikinmu dan kawo ziyara wurin mu, mu na muki barka da zuwa cikin a halin Sarki Lulu'aida. Tun kina jaririya ni ke jin labarin ki a wurin ƙawarki gimbiya Nu'aima, nasan zuciyar ki akwai ciwo mai tsayi sosai wanda kusan kullum ki ke kwana da shi ki ke tashi a cikin rayuwarki amma kadda kidamu in Sha Allah nan bada jimawa ba komai zaizo karshe zaki koma cikin a halinki kiyi rayuwa mai ƴanci, akwai yar matsalah tsakaninmu da wasu irinmu ne shiyasa mu ka kasa samun daidaituwar al'amari".
Tun da gimbiya ta fara magana Aira tai ƙasa da kanta gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi wani irin abu take ji ya na shigarta ta ko'ina, so take ta dago ta tambayi Gimbiya Mulaika shin wacece ita?, shin akwia hallitu irinta a gidan duniya? Ko itama ta na da wasu dangi makusanta ko wasu a hali? Su wayesu? wacece mahaukaciyar mahaifiyarta?. Jin an dafatan ya sa tai saurin dagowa ta yi ta na duban Gimbiya Mulaika, "Ki a dana tambayoyinki da sannu amsarsu zata zo gareki in sha Allah?"Kaduna.
Cibiyar ilimi.Ganin ya kasa furta komai ya sa ya chanza kalaman bakinsa wanda wannan karan ya samu nasarar furtawa ya na fadin "Har kindawo daga school din?".
A tsiyace ta kalleshe ta furta "kwarai kuwa".
In da matar yayanshi take ya duba ya ce Anty Nablah barka da gida, ya yara dereba ya dauko su daga makaranta ko?"Fulani ce
Comment
Share
Paid book ne Naira dari uku (300), 6322646280 Aisha Adamu Fidelity Bank. a turo da shaida ta wannan number 09064234445 idan kuma kati ne a turo shima ta lambar
Free page.
Page 3
YOU ARE READING
MAKIRCIN CIKIN GIDA
Spirituale_Munkasance a cikin duniyoyi mabanbanta masu cike da abubuwan birgewa da ban sha'awa, na taso cikin tawa duniyar da bansan kowa ba bansan wacece ni ba, a mafarki mai kama da zahiri na ke jin kamar ina da wasu a hali makusanta, ina jin ni ma kamar ko...