MAKIRCIN CIKIN GIDA
Aysha Adam Alhassan Ɗan Fulani
Shafi na biyar (5)
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
__________Hannu Aira ta riko suka zauna a kan wani dutse ta ke iska ta dauke su basu tsinci kansu a ko'ina ba sai abakin bukkarsu Aira, gwalalo ido Aira tayi ta ce "Kai har mun kawo? Umma"ta hau kiran mahaifiyarta. Hannu Nu'aima ta ja suka shiga ciki, duk da dattin dake jikinta wanda sanadin haukar da takeyi ya sa hakan ya zama da bi'arta duk da Aira na iyakar bakin kokarinta wurin chanza mahaifiyarta kayan da Nu'aima ke kawo musu, se ankai rana ruwa sannan ake samu ayi wanka a chanza kayan shima da duka hadi da cizo da ya kunshi, Umma ke nan kyakkyawar macece ta na zaune a gefe fara ce tas da'ita jikinta yai lukui-lukui doguwace, mai diri sosai har gitsatsen gashin ta dogo har ka fada, fuskarta dauke da dogon hanci da idanuwa kyawawa masu sheki, bakinta dan daidai wanda lips din suka zama jajajir.
Turs sukayi ganin ta zaune da wasu magunguna ta na lasa ta na kyalkyalewa da dariya mai amo, dafe kai Nu'aima tayi tai saurin fesge ledar hannun Umma, wurgi tai da ledar wacce kamar jira take a yi a jefa da'ita ta kama da wuta, cikin ƙanƙanin lokaci ta kone. Ihun da Umma ta fasa ne yai saurin dawo dasu da ga kollon da suke wa wutar, a han zarce Nu'aima ta feso ruwa da ga bakinta ta kashe wutar data kama a gaban Umma sanadiyar zubar da maganin ya yi a kasa.
Tsaki Nu'aima ta ja ta na yarfe hannu hamdala taiwa Ubangiji ganin wutar bata sami inda Umma ta ke ba, sake zabura Umma tayi a gigice tai waje ta na ihu ta na birgima a katsa, a guje suka biyo ta kokarin riketa Aira take amma sam ta kasa wani irin kululun abu ne ya tokare wuyan ta wani irin haushi ta ke ji ya na kamata a fili ta fara magana cikin wata irin murya mai amo, wacce ta karade ilahirin dajin "Na rantse da tsarkin mulkin Allah matukar baka chanza wanna mummunar dabi'ar ta ka ba to wallahi zan kona ka kamar yadda na kona ledar nan idan badda mugun hali da bakar mugunta meye hadinku da bil'adama ku je ku tun kari jinsi irin naku mana".
A tsoro ce Aira taja baya ta na duban Nu'aima wacce gaba ɗaya idanuwansa sun rikiɗe sunyi jajjawur, Ihune ya fara karade wurin dajin ya samo girgiza ya na wani irin rangaji ya juyawa wata irin bakar guguwa na taso, magana ce ta fara karade dajin cikin wata basamudiyar murya mai firgitarwa, "Ba ke ba ko shi da kanshi Lulu'aidah ya zo wallahi bazai kwashe damu lafiya ke har kin isa kina karamar hallita a cikin a halinku ki ce zaki jadani, karyarki ta sha karya yarinya a cikin su ke ba komai bace kuma da sannu zan dauketa na nisanta da inda ku ka kafeta wallahi na dau Alwashi sai na kashe ta har lahira".Fitsari ne ya kufcewa Aira gaba ɗaya ta kiɗime da jin batu daga inda ba ta iya hango kowa sai bakar guguwa da ta tirnike duk wani lungu da sako na dajin, ƙankame jikinta tayi jin muryar Nu'aima ta sake karaɗe dodon kunnenta "karya ka ke maci amanar addini da sannu zaka ga karshen ka, kuma wallahi nidin da ka raina ka ke ganin kafi karfina ni ce zan kawo karshen zalincika ga hallintu Ubangiji, ka sani ɗuk randa bil'adama suka sakoka a gaba to wallahi ranar watan tonon a sirinka ya tsaya na rantse da Ubangiji da ya hallicemu sai ka gane cewa kai din datti ɓaragurbi ne mai tsananin wari, zakayi mutuwar wulaƙanci mafi muni da ƙaskanci kuma da hanuna ni Gimbiya Nu'iama zan kona ka KWANGAL".
Bushewa da wata irin dariya ya yi take ya daga ilahirin bishiyoyin dake dajin yai sama dasu suka dawo suna komawa wajen su a harzuke iskar ta fara komawa ja, a fusace ya fara magana wadda tsananin rudewa ya sa Aira suma a wurin, "Karya ki ke waye ke yau she aka yiki da ki ke da zarra furta waƴanan kalaman toh ki sani da ke zan fara matsawar baki rabu da su ba ke zan fara hallakawa na kona gawarki na haɗa bakinta gawayin gawar ki dan karawa kai na ƙáimi".A fusace Nu'aima ta furta " kayi karya dan makaryata jikin makaryata ba kai ba kaf zuri'ar ku, da ku ka zama butulu a wurin bautar Allah babu wanda ya isa ya tabani ya zauna lafiya, wallahi Ubangiji se ya wulaƙanta ku kaf zuri'arku sai Allah ya kone duk wata hallita ta halinku, me za'ayi da datti a cikin duniya masu bautar wani Allah kun sanya cuta a zukatanku, kun ki Allah kun ki yadda da kur'ani gaskiya ne, Ubangiji maji rokon bayinsa shi zai bani damar da zan kona ka da ayar Allah اللّٰهُ لَاۤ اِلٰهَ اِلَّا هُوَ الۡحَـىُّ الۡقَيُّوۡمُۚ لَا تَاۡخُذُهٗ سِنَةٌ وَّلَا نَوۡمٌؕ لَهٗ مَا فِى السَّمٰوٰتِ وَمَا فِى الۡاَرۡضِؕ مَنۡ ذَا الَّذِىۡ يَشۡفَعُ عِنۡدَهٗۤ اِلَّا بِاِذۡنِهٖؕ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ اَيۡدِيۡهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۚ وَلَا يُحِيۡطُوۡنَ بِشَىۡءٍ مِّنۡ عِلۡمِهٖۤ اِلَّا بِمَا شَآءَ ۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ السَّمٰوٰتِ وَالۡاَرۡضَۚ وَلَا يَـــُٔوۡدُهٗ حِفۡظُهُمَا ۚ وَ هُوَ الۡعَلِىُّ الۡعَظِيۡمُ tun bata kai karshe ba dajin ya dawo da hasken shi komai ya dawo daidai, wurin da Umma ta ke yashe a kasa ta karasa cicibarta tayi ta kai ta cikin bukka ta kwantar da'ita, gyara komai na wurin tayi ta dawo inda Aira ke kwance a sume.
Tsugunawa tai a wurin ta na karanto wasu abubuwa wanda iya ita ka dai ne take jin abin da ya ke furtawa, bude ido AIRA tai hankali ta na fadin "Har mun iso?". Dan gaba ɗaya tamance abubuwan da suka faru, dariya Nu'aima tayi cike da hamdalah take kallan Aira cikin ranta tana ƙara godewa Ubangiji da yasa aikinta na yau taci nasara, gashi riko da Addu'a da aiki da'ita ya anfaneta kuma in sha Allah koda AYATUL-KURSIYE zata rusa tawagar ɓakaken aljannu.
Riko hannun Aira tayi suka miƙe a tare suka nufi cikin buka su, a kwance suka tarar da Umma a inada Nu'aima ta shin fiɗe ta. Wani sauti Nu'aima take ji daga fadarsu wanda ke nuni da ana nemanta cikin gaggawa, mikewa tai da sauri taiwa Aira sallama a gaggauce ta bace a wurin.
Tana barin wurin ta bayyana a cikin masarautar Sarki Lulu'aidah dandazon jinsinsu ne a wurin kowa ya nemi wuri ya zauna takawa tai har gaban sarki ta zube a kasa ta na miƙa gaisuwa, bai amsa mata ba ya fara magana wacce duk wani mahalukin dake cikin masarautar ya najin me yake faɗa "Meyasa zaki biyewa KWANGAL bayan kisan baida imani zai iya kashe wanna matar da ɗiyarta, a yau kin mai rauni a kafa yana chan yana jinya kin harbeshi da ayar Allah, idan ya nufe mutane da bakin aikinsa kin san abun ba zai yi kyau ba".
Durkusa tai har kasa ta na fadin " tuba nike shugaban shuwa gabanni, afuwan Sarkin sarakunan duk duniya, na same shi ya kaimata bakar ƙaya ne wanda cin wannan abun a gareta mummunan hatsari kuma hakan zai sa duk abin da zamu bata na magani ba zeyi tasari a kan ta ba, Ubana na kaina ka gafarceni babu abinda KWANGAL zai iya yimin muddin ina tare da addu'oi da ayoyin Allah, ka sani shi Alkur'ani yana tafe da duk wasu magunguna na sihiri, da dukkan wani abun damuwa. Na yi imani da Ubangiji da muke mai Sallah biyar a dukkan safiya da maraice, babu wani wanda yai saura a zuri'a su KWANGAL da ya'isa ya tako inda muke, tabbas na san dukkan mugun aikinsa na dan wani lokaci ne amman da sannu ni NU'AIMATU ɗiyar Sarkin da baya karya bare saba zance sai na kawo karshe wanna zalunci nasu a doron duniya, ka yafeni idan har nayi kuskurene harshe wurin sanar da sarki".
KADUNA.
Kwankwasa kofar dakin Nabla take a hankali duba da lokacin da dowar Haidar ya yi, jin a taba kofar a lamun za'a bude ya sa taja baya tana addu'ar Allah yasa yayarta Nablah ce zata bude kofar ba wan mijinta ba, cikin sa'a kuwa Nablah ta bude ta na duban ta, a hankali ta furta.
"Magana nazo muyi ya Haida ya nan ne?".
"Bayanan!". Nablah ta furta "shigo muje ciki lafiya kuwa ko wani abu ne ya hadaki da Mashkur".
Girgiza kai tayi tana zama a kan ɗaya daga cikin kujerun falon, kusa da'ita Nablah ta zauna ta na furta "wai lafiya kin tashi hankalina"."Lafiya ƙalau Anty wai Mubeen ne yace zan rakashe Abuja zeyi sati ɗaya kuma sai dai nutafi tare".
A razane Nablah ta furta "Abuja fah!". Anya "Alina zaki ga Annabi Rahma kuwa? Da aurenki zaki tashi ki bar gari lallai abun naki ya shahara wallahi kin fara fin karfina a kan duk wani al'amari ina goya miki baya amma banda wanna dan bansan irin ƙaryar da zaki sani nayi a wannan karan ba, kiyi wa Allah ki janye wanna abu dan ba mai kyau ba ne".
Bandir din yan dubu-dubu ta a jiye mata a kan ciya ta na fadin "Wannan ya isa ko kina buƙatar kari, burina muje wurin Bokan gabas ya sake kullle ma sakanan baki dan naga kwana biyu neman tonamin asiri yakeyi saboda bini-bini yana kan bibiyata, sai dai maganin da boka ya bani na ya na kasa yin magana akan dukkan abin da na yi, ya na aiki amma na ga kwananan sai na kara tashi tsaye ki sa mana ranar zuwa kawai maganar tafiyata duk abin da na tsara shi zaki bi kuma kiyi yadda nace".
Da ido Nablah ke bin Alina cikin zuciya tana mamaki wato makoyin mafiyi, yanzu yarinyar nan har tai saurin zuciyar da zata aikata wanna al'amari kai kaji tsoron icen da ba'a tan kwaranba.
Fulani ce
Comment
Share
Paid book ne Naira dari uku (300), 6322646280 Aisha Adamu Fidelity Bank. a turo da shaida ta wannan number 09064234445 idan kuma kati ne a turo shima ta lambar
Free page.
Page 5
YOU ARE READING
MAKIRCIN CIKIN GIDA
Spirituale_Munkasance a cikin duniyoyi mabanbanta masu cike da abubuwan birgewa da ban sha'awa, na taso cikin tawa duniyar da bansan kowa ba bansan wacece ni ba, a mafarki mai kama da zahiri na ke jin kamar ina da wasu a hali makusanta, ina jin ni ma kamar ko...