MAKIRCIN CIKIN GIDAAysha Adam Alhassan Ɗan Fulani
Shafi na Shida (6)
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
_______Da ido Nablah ke bin Alina cikin zuciya tana mamaki wato makoyin mafiyi, yanzu yarinyar nan har tai saurin zuciyar da zata aikata wanna al'amari kai kaji tsoron icen da ba'a tan kwaranba.
Mikewa tai tabarta cike da mamaki kudin tabi da kallo tana girgiza kai hannu ta kai ta dauki kudin tana mamakin karfin hali irin na ƙanwara wacce suke ciki ɗaya.
Mashkur yana zaune a kan tambar da Hajiyan su tasa khalis autar su wacce bata wuce shekara ashirin ba ta shinfiɗa musu shida mahaifinsa, kuloli abinci ta ajiye musu a kan tabarma da aka shimfiɗa. Plat Mashkur ya dauka yana kokarin zuba abinci ya ji sallama Yayansa Haidar. Amsa sallama Baffa ya yi shi ma wurin zama yaiwa kasan yana gaida mahaifiyarsu Hajiya Hadiza, Mashkur ne ya ajiye mai plat din tuwon shinkafah miyar kubewa yana fadin "Yaya ina wuni ya yanma dafatan ka dawo lafiya".
"Lafiya qlau Alhmudllh kai fa?" Ya ba shi amsa ya na jan plat din gaban shi juyawa ya yi wurin mahaifiyarsa yana mika mata gaisuwa, cikin fara'a ta amasa mishi ta na mai ya hanya, se da suka gama cin tuwon sannan su kai musu sallama suka kama hanyar gida. Suna isa gida kowa ya kama hanyar part dinsa, Maskur ya na shiga falonsu bakinsa dauke da sallama cikin ikon Allah yau yaji duk wani abu ya mai sauki, sabanin kulum da ya ke jin faɗuwar gaba a lokacin shigowa da fita gida yau wa sa yau ya ke jin shi.
Murda hannun kofar ya yi bakin shi dauke da sallama kamar kullum yauma yaran suna zaune suna cin abinci, sai dai babu Alina a wurin, zama ya yi a kusa dasu ya na jansu da wasa, daga bisani ya miƙe ya nufi ɗakin Alina nan ma shiga ya yi da sallama ya na duban inda take tsaye a bakin durowa ta na haɗa kayanta cikin wani ƙaramin akwati, mamaki yake cikin ransa me za tai da kaya haka, kasa hakuri ya yi ya kira sunanta wanda tunda ya shigo bata juya ba bare ta nuna tasan Allah ya hallitasa a wurin. Jiyowa tai fuska babu yabo babu fassalah ta na fadin" Ure welcome dear Ina ka maƙalene yau mun jika shiru".
Wurin zama yai ma kansa gefen gadonta yana fadin " Gidan Baffa naje hadda abinci muka kwasa nida yaya a chan, but baby kayan meye ki ke haɗawa ne naga kina shirya akwati haka?".Kallan shi ta yi tana fadin "tafiyar gaggawa ce ta taso min kasan Finally year ni ke a school toh su ɗan turamun Abuja ne yin wani bincike sun bamu one week in Sha Allah muna kamallah wa zan dawo".
"Yaushe ne tafiyan!".ya furta yana du banta
"Jibine ranar Saturday in Sha Allah, zamu tafi a motar makaranta".
"Okay Allah ya kaimu amma da zaki bari mutafi tare na kai ki ko babyna "
Karamin tsaki taja tana kare mai zagi a zuciya a fili kuma ta furta haba dan Allah kadai bari mutafi da ƴan ajinmu abin zai fimin dadi wallahi".
Bai cemata uffan ba ya saka hannu cikin aljihu ya ciro wayarshi da ke ta ruri tana neman a gaji gaggawa, mikewa ya yi ganin kirane daga shugaban Officer dinsu ya bar mata ɗakin.
Kamar jira Alina ta ke yi ya fita tafara tsigaleshi a fili tana, zagagge gwandon zage-zagenta a cikin ɗakin.Aira
Dafah Nu'aima sarki ya yi ya saka mata albarka, inda jama'arsa suke ya kallah ya soma magana cikin murya mai nuna iZZA da isar mulki irin nasa "A yau na yar jewa duk wani na cikinku ya dinga kare kansa da ga zuri'arsu KWANGWAL, duk wanda suka takala kadda ya yarda ya kwaci kansa sai dai ban lamunce da cutarwa da wani abu na cutarwa ba, abu daya na yadda da shi shine ku dinga konasu da ayar Allah, na lura su bazasu chanza ba a kan dukkan wata mugunta da suke yi, sun hana jinsimu zaman lafiya sannan sun hana bil'adama zaman lafiya sun haukata wasu, sun raba mata da miji sun shiga jikinsu sun musu mummunan illah, amma fah suma bil'adama akwia nasu sakacin basu damu da addu'a ba ga san zuciya, kishiya ta kai sunan kishiryata wurin boka a haukata ta, sun mallaka mazajensu, DUNA bakin Aljan ya zama shi ne na hannun da mansu wurin firgita bil'adama ya na bin inuwa, ya na sa ciwon kai mai tsanani ya na sanya kasala wurin aikata dukkan aikin alheri ya na bin jiki kaji kamar ana maka raɗa ko a ana maka magana, akwai ayoyi da yawa a cikin kur'ani na karya sihiri ku jajirce wannan karan yaki za muyi dasu sosai a kan dukkan wata cutar tasu a yau ɗiyata tai nasarar samun kona wani yanki na jikin shugaban azzaluman jinsi dan haka ku ma ku zama cikin shiri a kowani lokaci zasu iya farmakar ku dan an taba musu shugaba ina mawa kowa fatan alheri za ku iya tafiya".
Godiya Jinsi Aljannu ma biya sarki LULU'AIDAH sukayi suna ta murna da basu damar da sarki ya yi da yawansu nata sarawa Gimbiya Nu'iama akan kokarinta na kona wani sashe na jikin Kwangal. Meƙewa gimbiya tai ta nufi cikin gidajensu wanda ya ke cikin masarauta, hannunta ta daga sama ta kewaye bukkarsu Aira wadda tuni bacci ya dauketa saboda duhun dare.
Kwangal ya na zaune a kan reshen da Nu'aima tai wurgi da shi a lokacin da ayar Allah ta fara huda shi wuta tafara cin jikishi, ba cewar da ya yi yasa ya fada a kan bishiryar rimi, nishi yake da ƙyar ya dunkule hannu yai sama da shi sai ga wuta na mulmulowa ta na gangarawa cikin dajin, a fusace ya samo magana "Yau ya dau alwashin tunda aka tabashi a kan bil'adama to sai na kona su Aira kurmus". Wani uban ihu ya saka ganin wutar da yake turawa ta na komawa ruwa, a zabure ya sake kai hannu sama sai ga ruwa mai mugun karfin ya sauka a dajin amma abin mamaki ruwan baya zuwa wurin su Aira . A fusace ya kara an giza ruwa da nufin mamaye dukkan dajin amman sam ruwan ya ki karasawa wurin. Cikin murya mai ci ke da Amo ya furta "JAHIM Bai kai ga karasawa ba wanda ya kira da Jahim ya bayyana a gabansa yana huci ya na zaro harshe waje idon jajjawur kamar ruwan wuta.
Dur ƙusawa ya yi a gaban kwangal ya na sadda kai cikin wata gigitaciyar murya yake fadin "bisa umarninka ni ke nan zuri'ar wa za'a hallaka maka cikin iko da isar mulkinka ubangidana".
Bushewa da dariya Kwangal ya yi yana fadin "ƙone min dajinan kaf dinsa, wasu bil'adama nikeso a hallaka su saboda su yau wuta tai nasarar shiga jikina, bazan kyalesuba".
Yana rufe baki dajin ya fara jijjiga bishiyoyin ciki suka dinga jijjiga suna bushewa take ko'ina ya mamaye da wuta ya na wani irin hayaki, duk abinda JAHIM ya ke bai sami bukkarsu Aira ba hankalin Kwangal ya yi kololuwar tashi, miƙewa ya yi yana dingisa kafarsa Sunan Jahim ya kira cikin bacin rai yace "mu bar dajin yanzu zuwa wani lokaci ma waiwaye shi".
An gama shugaba cika aiki da biyayya shine aikina a ko yaushe shugaban dukkan nahiya.Duk hargagin da su Kwangal keyi Nu'aima tana kallo burinta da ya matsa sai ta bayyana a inda ya ke ta kona shi, washegari da sanyin Asuba ya motsa Nu'aima ta sauka a kofar bukkar su Aira hannunta dauke da babbar kula mai rai da lafiya. Da sallama ta shiga cikin bukkar Aira ta hango zaune akan sallaya ta na addu'a, hamdala taiwa Allah cikin ranta ganin ƙawarta ta na addu'a ban garen Umma ta kallah se shirgan bacci take yi ta na minshari, nan ma godiya ta sake mawa Ubangiji da ya shirya komai yadda ya ke so.
Kaduna Mashurk na fita yai dakinsa yana amsa waya Nabla ce ta shigo fallonsu Alina da sauri tai ɗakinta ganin shigewar Mashurk dakinsa, tana shiga ta kalli Alina tana fadin "Ya kuka yi maganar tafiya ya amince miki".
Kallan Anty Nabla tayi ta sheke da dariya ta na fadin "ai ki shirya jibi zan tafi gobe kuma mu je gurin boka dan wanna karan akwai aikin da nakeso ya mun wanda zan ja kudi masu mugun yawa dasu".
"Toh yanzu Alina dawani lokaci zamuje wurin Bokan gabas dan kinsan ni yanzu Ban cika son fita ba saboda yanayin da muke ciki da Haidar abu kadan ya ke jira zai ce min ba haka ba".
Tsaki Alina taja tana janye akwatin gefe tana kullewa "kewai Anty!" ta furta meyasa ki ke tsoron Yaya Haidar ne mutumin da baifi kibawa malam dubu hamsin ba yagama miki dashi amma kin tsaya kina tsumulmula"."Kaiyya!" Nabla ta furta a kasan zuciya "Wato dai yaro-yaro ne". A fili kuma tai murmushi tace "Kema kin sani Alina gaba tafi baya yawa, ke dai ki iya takunki saboda karki zama kyandir mai kona kanshi ya haska wani ita rayuwa bata da tabbas, yanzu ki ke kan ganiya komai zakiyi ki dinga tuna zaki iya zamewa akan ruwan kubewa mai yaukin gaske Alina, kinsan abinda nai kwantan kwacin shi bakiyi ba banbancina dake Ni bana bin maza".
Fulani
Comment
Share
Paid book ne Naira dari uku (300), 6322646280 Aisha Adamu Fidelity Bank. a turo da shaida ta wannan number 09064234445 idan kuma kati ne a turo shima ta lambar
Free page.
Page 6
YOU ARE READING
MAKIRCIN CIKIN GIDA
Spiritual_Munkasance a cikin duniyoyi mabanbanta masu cike da abubuwan birgewa da ban sha'awa, na taso cikin tawa duniyar da bansan kowa ba bansan wacece ni ba, a mafarki mai kama da zahiri na ke jin kamar ina da wasu a hali makusanta, ina jin ni ma kamar ko...