MAKIRCIN CIKIN MAKIRCIN CIKIN GIDAAysha Adam Alhassan Ɗan Fulani
SHAFI NA NA TAKWAS (8)
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
A razane Aira ta jiyo da kallonta ga Nu'aima wacce ta gyaɗa mata kai alamun tabbatar mata da iya gaskiyarta ta faɗi gam ta sake matse hannunta cikin nata tana fadin.
"Haba diyar sarki me zeyi sanadiyar rabuwarmu bayan a cikin duniyata babu wanda na sani in bake ba, shin suwaye sanadin zuwana menene MAKIRCIN CIKIN GIDA,suwa suka kullah hakan da na kasa gane gabas bare na tattance yanma, Nu'aima zan zabi zama dake akan kowa zan hakura da komai na cikar muradeena na zauna da ku".Girgiza kai Nu'aima tayi tana murmusawa mangwaro dake hannun Aira ta karba tana nuna mata wani yanki na jikin magwaron tana fadin.
"Kalli nan kiga wani abun al'ajabi ƙawata".
Waro ido waje Aira tayi tana mamakin ganin inda ta gatsa ya yi baki sai wani irin motsin ƙadan-ƙadan wurin yake yi. Jada baya tai da sauri cike da tsoron ganin wurin data gatsa, a rikice ta ke fadin.
"Innalillahi wa'ina alaihi raji'una Qawa meye shi wannan din".
Wullar da mangwaro taiyi a nesa da su Aira tabi inda mangwaro ya sauka da'ido taga magwaron ya kone kurmus, sake rudewa tayi ta juyo tana kallan Nu'aima da ke kyalkyala dariya.
"Wayyo Allah!" ta furta a fili
"Wai me yasa dukka wannan abubuwan haka ne daga daukar magwaron shikenan sai mugun dafi a jikinshi".
Matukar bazaki dinga addu'a adukan abinda zakici ba tofah kina tare da cin guba a ko yaushe dan wata rana ma idan bikiyi a hankali ba to Kwalgal akan ki zaiyi nasara kinga aikinmu ya lalace kenan, mutuminan baida imani akan bil'adama sam bansan har tsahon yaushe zai dena aikata mugun aikinsa ba, meyasa zai cutar da itaciyar Allah ya mai da ƴaƴan jikinta guba, ban san yau she zai gane musulunci shine gaskiya ba amma muddin bai dena wallahi asirinsa zai tonu kwanan in Sha Allah komai yazo karshe da yar dar Allah".Galala Aira tai da baki tana sauraranta rintse ido tai a lokacin da Nu'aima ta sawa zance ta aya, tambayar kanta take wai wasu irin abubuwane haka suke faruwa wani zance kuma ɗiyar sarki ke yine shin waye yake cutar da'ita waye wanna Kwalgal din da yake sauya itace ya maida shi ɓaragurbin duk tsananin kyan magwaron nan ashe (BARAGURBIN KYAU gareshi. sabon littafina wanda idan mai dikka ya bamu a ron rai zamu daura a kai).
Karamin tsaki taja a fili tana duban Nu'aima wacce tai tsaye tana kallanta.
"meyasa bazaki sake hakuri akan komai ba na gaya miki saura kiris ƙawata".Cewar Nu'aima murmushin Aira tayi suka cigaba da jerowa har bakin bukkarsu, a kwance suka tadda Umma na kwasar bacci wurin zama sukai wa kansu a bakin kofah kan inuwar bishiyar da ta lullube bukar.
Sunan Nu'aima Aira ta kira tana fadin. "Dan Allah ki taimaka ki labarta min wani abu dagan gane dani ko zan samu sassauci da hargitsatsun tambayoyin da zuciya take min a kowani lokaci".
Murmusawa Nu'aima tayi tana fadin "Abu ɗaya zan iya sanar miki shine ki jajirce da addu'a a koyaushe nasani muddin muna rayuwa watarana zamu samu sassauci akan abubuwan da suke damun rayuwarmu ta yau da gobe, Aira kedin kamar kowa ce kina da Ahali sannan kuma kuna da yawa amma kiyi hakuri nan gaba kadan zaki sudu da a halinki"."Meye MAKIRCIN da ya fito dani daga cikin a halina?". Aira ta furta tana sake kai dubanta ga ƙawar tata".
"Banda amsar tambayar nan dan wannan aikin bil'adama ne su zasu amayar da wutar da suka zubawa cikinsu, a ranar tonon asiri zasu labarta muku komai ke da mahaifiyarki wacce bata da laifin komai hasalima tsananin kirkin ta ga danginta da a halin babanki yai sanadiyar jefata cikin wannan hali".
Mamakine ya lullube Aira wanda ya kasa boyuwa a fuskarta shiru tai dan gaba ɗaya tambayoyinta ta san babu mai bata amsa zefi ta hakura har se lokacin da aka ce za'a sanar da'ita ya yi.KADUNA
karfe bakwai tai sallama da yara ta nufi ɗakin Anty Nablah tai mata sallama, bakin get Nablah ta rakota tana tambayarta "kinyiwa Mushkur sallama?".
"Eh yana ciki yana bacci nasan idan ya kamallah zai tambaya ina nike kyace mai mun kama hanya" Ta bata amsa girgiza kai Anty Nabla tai tana jinjina al'amarin Alina ta koma cikin gida.Shabiyu na rana suka bar garin Kaduna ita da Mubeen sai murna take yana tuki suna hira dubanta ya yi yana fadin.
"Kwana nawa ki ke so muyi a chan ne babyna?".
Langabe kai tayi ta turo ƙaramin bakinta gaba murya shagwaɓe tana fadin.
"nadai ce one week zanyi but idan kana buƙatar kari sai muyi fiye da haka, wallahi kwanan zan balle aurena na dawo wurin ka muyi aure dan ni banga amfanin zama da wanchan solo biyon ba babu abinda yake bani wanda zanjini zamzam ina komawa zan tirsashi ya sakeni na huta tunda kai ure ready baby".Dariya mai cike da jin ɗadi Mubeen ya saki yana jawota jikinshi manna mata kiss ya yi a gefen kumatun "Baby!" ya kirata sunanta ya daura da fadin.
"Zan aureki mana kuma zan ware miki gidan ki ke ka dai muyi rayuwarmu duk cikin matana babu wacce take ban hadin kai kamar ke idan mun dawo daga Abuja sai kiyi yadda zakiyi muga ko za'a samu abinda ake so".
Langabe wa ta sake yi a jikinshi tana manna na mai kissing din a wuya taka birki ya yi da sauri yana fadin.
"Haba baby kadda kisa mu fadi a hanya mana".
Kyalkyalewa da dariya tayi tana barin jiki shi ya cigaba da tukin, basu zame ko'ina ba sai cikin hotel din dake cikin Maitama ɗakine mai dauke da gado da durowa dai karmin teburi da kujerar zaman mutum biyo, ta jikin bango kuma Tv ne da sauran kayan kallo. Dodar taji dakin yadau sanyi Ac.
A kwatinta ta a jiye akan kujerar ta cire facemask din fuskarta tayi da gyalenta ta ajiye a gefe. Tumbur tayi ta shige bayi tai wanka tana fitowa ta iske Mubeen kwance shima babu wasu waddatutun kaya a jikinshi, fadawa jikinshi tai tana aika mai sakwanni masu rikitarwa, biye mata ya yi suka chaskale.Karfe goma Mashkur ya farka da ga bacci da ya dauke shi bayan dawowa daga sallar asuba, bakinshi dauke da salatin Annabi ya farka yana miƙar gyagije gajiyar bacci, ƙafafuwan shi ya sauko kasa ya nufi bayin dake manne a dakinshi wanka ya yi tare da dauro alwala, tawul din dake kanshi wanda ya tsane ruwa dashi ya rataye bakin kofar bayin ya ajiye.
Sallaya ya shimfida ya gabatar da sallar walha yana idarwa ya jawo kur'ani ya karanta daidai gwargwadon abinda Allah ya hore mishi ya mai da shi wurin da ya dauko ya nufo falonsu, jin wurin tsit ya sanar dashi babu kowa, ɗakinta ya nufah ya murda kofar jin shiru ya tunatar dashi zancenta na jiya da taimai bakwan kwana na tafiya Abuja.
Girgiza kai ya yi kawai yanufi kiching yana lalubawa yaga babu komai a cikin kiching, tsaki ya saki a fili yana jawo flas ko zai samu ruwan zafi nan ma wayam babu komai a cikin Alina ya furta a fili cike da kunar zuciya ya jawo wayarshi a cikin aljihu. Falo ya dawo ya zauna a kujera mai zaman mutum ɗaya, ya na latsa wayar ya hau kira, ya na mai da wayar zuwa amsa kuwwa. Ring ɗaya a na biyun aka dauka daga chan ɓangaren akai salama!. Amsawa Mashkur ya yi ya na fadin.
"Na gaida oga ya aiki kuma ya fama da ɗalibai".
"Alhamdullilahi!" Wanda aka kira da Oga ya furta ya daura da fadin.
"Ina Madam dinka suna gida suna hutu ko kafin a koma".
Damm! Damm!! Damm!!! Gaban Mashkur ya yau duka yana tsinkewa gaba daya lissafi shi ya kwace da jin maganar da ke fitowa daga bakin ogo, daurewa ya yi ya saki murmushi da yafi kuka ciwo yana hadiyar wani abu da ya tokare mai maƙogaro, magana ya soma kamar ana fisgota daga bakin shi ya ke fadin " Aikuwa suna shan hutu gata chan ɗaki tana bacci yanzu haka cewa nayi bari na kiraka mu gaisa tunda kwana biyu ban samu na leko ba"."Ayya ai babu komai Abokina komai yanan lafiya yadda ake buƙata nima zuwa anjima kaɗan zan bar office in koma gida muma mu huta".
Godiya Mashkur ya yi mai wanda gaba ɗaya yanayi ne kawai batare da ya tantance make yake cewa a kan labbasa ba, hawaye ne ke saukowa akan kunci da zuciyarshi tai mai baƙi ƙirin, wayarsa ya dauka ya kira layin Alina Wanda ke ring Kamar zai tsinka wayar, amma sam bata amsa ba aƙarshe ma ya koma Number busy, dafe kai ya yi yana furta kalmar."inallilahi wa'iinna inaili raji'una Ya Allah ka kawo min dauki a cikin wannan al'amari mai tsananin, Allah na san kasan dani kaine ka jaranceni da mata mai bin maza ya Allah ka sausauta mun akan dukkan abubuwan da nakeji a cikin kwakwalwa ta".
Mikewa ya yi kamar wanda aka tsikara ya koma dakinshi hargitsa dakin ya ke yi yau ya yi alkawarin sai ya tuno abinda kwakwalwarsa ke kokarin tunatar da shi a kulum sai yaji mugun ciwon kai, kanshi ya soma ciwo mai tsanani yana jin ana mai ƙuda da wani irin ihu a cikin ɗodon kunne sa, zame jiki ya yi ya nufi kan gadonshi ya jawo wayarshi yai connecting wayarshi da TV a take ayar Allah ya fara amo a dakin nashi cikin muryar Shaikh Sudais".
Kwanciya ya yi sannu a hankali yaji kanshi yana komawa normal a hankali bacci ne ya kwashe shi.Fulani
Comment
Share
Paid book ne Naira dari uku (300), 6322646280 Aisha Adamu Fidelity Bank. a turo da shaida ta wannan number 09064234445 idan kuma kati ne a turo shima ta lambar
Free page.
Page 8
YOU ARE READING
MAKIRCIN CIKIN GIDA
Spiritual_Munkasance a cikin duniyoyi mabanbanta masu cike da abubuwan birgewa da ban sha'awa, na taso cikin tawa duniyar da bansan kowa ba bansan wacece ni ba, a mafarki mai kama da zahiri na ke jin kamar ina da wasu a hali makusanta, ina jin ni ma kamar ko...