Aysha Adam Alhassan Ɗan Fulani
@Women Writer's Association.
Shafi na biyu (2)
Tsalle ta yi jin dariyarsu har cikin ƙwaƙwalwarta, ƙankame Nu'aima tayi jinkinta sai kyarma yake yi, a razane ta furta. "ki taimake ni kadda su tafi da ni sama".
Dariya ce ta kwace wa Nu'aima ta dara sosai, sannan ta riko hannun Aira "Yanzu tun kafin mushiga Masarauta kin fara tsorata inaga mun shiga, ki cire tsoro a cikin ɗukan lamuranki dan bikiga komai ba yanzu ne abun zai fara, waƴanan yaran cikin fada ne suka fito shawagi, a tsorace ta riƙe kunkumin Nu'aima ta na jin wani irin tsoro na shigarta ta ko'ina, murya a daddare ta furta yan- zu ke ma ki na tashi sama Nu'aima?". Bata kai ga karasawa ba ta hangosu chan sama sun lula.KUDUNA.
In ji masu ta ke suka ce ciyabar ilimi.
Zaune ya ke ya dafa kai zuciyar shi na kokarin tinano mai wani abu amma sam ya ka sa tino komai, da zarar ya yi ƙoƙarin tinano wani abu na rayuwarshi sai yaji kamar ana zuba mai ta fasasshen ruwa zafi a cikin kwanyar kan shi, tsaki ya ja ya gyara zama a kyakkyawan Office dinsa wanda ya ke dauke da kujerum zaman mutum biyu masu kallan juna, se tebir wanda ya kasance mamalakin kujerun, karamin frij. Bugun kofar da a ke yi ne ya dawo dashi cikin tunanin da ya zame mai jiki a ko da yaushe, izin shigowa ya bayar ya gyara wa kansa zama, bakinsa dauke da sallama ya murda hannun kofar ya shigo cikin shiga ta alfarma, wurin zama ya makansa a ɗaya da ga cikin tagwayen kujereun da ke kallan juna, mi ƙamai hannu ya yi ya na fadin " ƙalau dai Abokina? na ga idonka ya chan za launi ya yi ja lafiya kuwa?".
Sosa kai ya yi ya na fadin" Lafiya Lau Sofiyan wallahi ciwon kai ne ya ke neman kamani amma in sha Allah Ina zuwa gida zan sha magani, ya a ke ciki ne duk yau bamu hadu ba ko mai dai lafiya ko?".
Jin gina bayansa da kujera Sofiyan ya yi ya ce " Se godiya yau ina gidan ban fito ba sai karfe hudu, lokacin da na shigo a na sallah shine nai masallaci kuma da nashigo na so lekowa kuma aiki ya shamun kai yanzu na samu na tsahirta, shi ne ce bari na leko ka mu dan zanta".
Murmusawa Mushkur ya yi ya na fadin " Se a hankali ni ma ban shigo da wuriba sai azahar na samu na leko, amma yanzu nake shirin tashi dan zan biya gidansu Baffa na ga lafiyasu".
"To ka karasa mana sai na raka ka daman kwana biyu bamu gaisa da Baffa ba so ina office ka sameni in ka kamallah dan ni ban fito da mota ba".
AIRA.
Ganinta a sama ya sa ta sa ke sakin wani irin razanannen ƙara ta na ƙankame Nu'aima, dariya Nu'aima ta saki ta na fadin "in dai ki ka maida tsoro dabi'arki to baza mu shirya dake ba, plz ki natsu kin san ba zan miki wani abu na cutar wa ba, yanzu zan kai ki fada gurin Abbana ki dena jin tsoro dan Allah".Sassauta riko da tayi wa Nu'aima ta yi tana kallon sararin samaniya gwanin burgewa, ƙasa ta maida dubanta taga hallintu wurin ƙanana, a zabure ta sake ƙanƙame Nu'aima ta na fadin "Zan fado ki taimaka mun dan Allah kinji". Bata kulata ta ba ta juya ta rike mata dan yatsanta rintse ido tai dan ji tai kamar an fisgar mata hannu, da sauri ta bude idon dan jinta saukar kafarta a dandamalin kasa, gwalalo ido tai waje ganin wata hadidiyar masarauta me ciki da abubuwan burgewa da ban sha'awa, wai-waya tayi taga wasu irin hallintu masu dogayen kunne, ga su da mugun tsayi wasu kuma kamar ka kife da tukunya dan ƙanƙanta, neman tsoron da take ji tai ta rasa, juyowa tai dan neman Nu'aima amman sam bata ganeta ba saboda ta chanza launinta ta koma irin ta mutanen wurin sai dai zubin jinkinta yanan bai sauya ba.
"AIRA!". Taji an kira sunanta cikin wata murya mai taushi da ɗadin gaske, wai-wayawa tayi dan ganin waye mamalakin muryar. Wata dattijuwa tagani zaune a kan ɗaya daga cikin kujereun alfarma na wurin wanda akai musu ado da lu'u-lu-u, ga wasu furarrani masu kyau da daukar hankali, ganin matar na motsa bakinta ya sa Aira nufo inda matar take dan tattabatar ita ce ke kiranta. Tafiya take tana jin kafarta na taka wani irin lallausan abu mai laushin gaske, idonta ta kai duba kasa ta ga lafiayyun fulaloyine korayen take takawa, mamaki ne ya kamata tambayr kanta takeyi to meyasa su ciyayin wurin bukkarsu basu da laushin irin wanan?. Ganinta a gaban matar ya sa ta hadiye tambayar ta, "Aira!". Ta sake kiranta wannan karan sunan nata bai karade wurin ba, "Ga guri zauna a nan kafin ƙawar taki ta dawo daga sanar da gimbiya Mulaika isowar ki, me ki ke so a kawo miki ki ɗan taba yanzu".
Gurin zaman ta kalla ganin irin kujerar matarne ya sa ta zauna, ta kalli matar tace inajin yunwa duk abin da aka bani zanci". Bata rufe bakiba taga teburi a gabanta an shirya soyayyun kaji da lafiyyar wainar masa, gefe kuma farfesun naman kai ne sai shinkafah da miya, da yan bangaren kuma kindirmo da madara se ruwa cikin wasu fararen tasa, ta ɗayan ɓan garen gassanun naman zabi ne. Kamshi da yakusa kasar da da'ita ne ya matar da'ita mamakin zuwan abincin gabanta, hannu takai cikin sauri ta dauki kwanon wainar tana hadiyar miyau dan yau kwata-kwata bata saka komai a bakinta ba, koda ta tashi ba tai tozali da Ummanta ba kuma gashi ba taga abinci a inda ta saba gani ba, dalilin haka nema yasa tazo bakin Ƙudiddifi ta zauna dan ɗebawa kanta kewar rayuwar kadaici a cikin dajin da gaba duhu baya duhu, a duk sanda tai yin kurin nufar wata hanya sai taji an jawota an maidata inda take zaune, wuri ɗaya take iya zuwa da kanta shine bakin ruwan da ke kusa da su, iya nan kwai take iya takawa da ƙafarta.
Kauda tunanin rayuwarta tayi ta dinga kwasar abinci kusan komai na wurin se data lasawa ba kinta, ni shadi take ji yana shigarta ganin yau ne karo na farko da ta taba zuwa wata duniya ta daban da ba tattaba, lumshe ido take tana jin wani irin kamshi na tunkarota, a hankali ta bude idanuwanta ta sauke akan wata kyakkyawar mata, cikin shiga ta alfarma irinta mutanen wurin sai dai ita shigarta ta babanta da ta sauran mutanen wurin yanayin kalar tufafin jikinta, akan labbanta ta furta "Furta Gimbiya Mulaika".
Jin an tabata tai firgigi ta juya kyalkyalewa da dariya Nu'aima tayi tace "Sarkin tsoro kawai ki taso muje gun gimbiya ku gaisa kafin Shugaba ya fito shima, amman dai kin koshi ko?".
Gyada mata kai kwai Aira ta yi, ta mike tsaye suka fara jerowa a tare.Kaduna.
Cibiyar ilimi.Fulani ce
Comment
Share
Paid book ne Naira dari uku (300), 6322646280 Aisha Adamu Fidelity Bank. a turo da shaida ta wannan number 09064234445 idan kuma kati ne a turo shima ta lambar
Free page.
Page 2
YOU ARE READING
MAKIRCIN CIKIN GIDA
Spiritual_Munkasance a cikin duniyoyi mabanbanta masu cike da abubuwan birgewa da ban sha'awa, na taso cikin tawa duniyar da bansan kowa ba bansan wacece ni ba, a mafarki mai kama da zahiri na ke jin kamar ina da wasu a hali makusanta, ina jin ni ma kamar ko...