MAKIRCIN CIKIN GIDA PART 9

6 3 0
                                    

Aysha Adam Alhassan Ɗan Fulani

SHAFI NA TARA (9)

                    بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

_____Kwanciya ya yi sannu a hankali ya ji kanshi yana komawa normal a hankali bacci ya kwasheshi.
Bacci  ya yi sosai mai cike da mafarkin mai ban tsoro, a razane ya farka duk ya jiƙe da zufah waige-waige yafara yana ƙarewa dakin kallo mummunan mafarkin da ya yi ne ya fara dawowa mai a zahiri, a ƙideme ya miƙa ya dauki mukulin mota ya fito harabar gidan.

Ssfiyan ya hango tsaye da megadi, Safiyan yana hangoshi ya ma megadi sallama yana fadin.
   "Gashi can bari na ƙarasa tunda ya fito".
Tun da ya tunkaro shi ya ke nazar ta shi, ya na karasawa ya riƙe mai hannu ya na fadin.
         "Abokina ashe kana gida, amma lafiya naganka wani iri haka".

"Inafah lafiya Safiyan mudai je cikin gida dama wurinka nai niyyar zuwa kuma sai gaka, muje ciki ka ji komai".

Tun bai gama fadin maganar ba ya yi gaba, adaidai kofar ɗakin  Nabla suka cikaro da yayanshi yana fitowa, gaisawa sukayi suka nufi shashin Mashkur, suna shiga falo Mashkur ya sawa kofar key ya nemi wuri ya zauna a inda Safiyan ya zauna yana fadin.
    "Aboki ban da wanda ya wuce ka, a yau na tashi da wani irin al'amari mai ban al'ajabi, Fatima yau Allah ya bani ikon tunawa da'ita kullum inaji na inada wani abu mai mahimmanci amma dana fara tunawa sai inji kaina kamar zai bar gangar jikina, jiya na dawo Alina take mun sallama da daddare akan yau zasuje Abuja narasa dalili da yasa ban iyawa Alina fada a duk sanda zatayi ba daidai, na sani kaima ka sani Alina bin maza take bansan dame zan kare kaina a gurinta ba, tun daga ranar dana tabbatar mawa kaina cewa da gaske bin maza take na daukewa kaina mu'amular auratayya a tsakanina da'ita, jiya munyi sallama yau na tashi bayanan na shiga na duba batanan shine na kira Aboki inji ya batun zuwansu Alina Abuja tun kafin inyi magana yake cemin an basu hutu jikina ya yi matukar sanyi da jin kalamansa mikewa nayi da niyyar rubuta mata takardar saki saboda nagaji da'ita, ina zaune naji kaina ya hau sarawa shine na samu na saurari ƙur'ani cikin hukunci Ubangiji na samu sauki na kwanta bacci, cikin bacci nai mafarkin Fatima tana daure a cikin wani ɓakin daji tana kiran sunana abinda na kasa fahimta shine ina Fatima take nasan tana da ciki, ta haifeshi ko yaya gaba ɗaya na kasa gane lissafin kaina a riƙice nake akan al'amuranan".

Jinjina al'amarin Safiyan ya yi yana godewa wa Ubangiji da yadawo da abokinsa kan hanya bayan rasa gane kanshi da sukayi shekara da shekaru "Nikam bazance komai ba amma zai fi kyau mu tafi wurin Baffa domin magana nan nada matukar tsaho magance wacce ba'iya ni kadai zan fayyace maka komai ba, sai dai abu ɗaya nakeso ka adana shine maganar matarka Alina ka barta iya ku biyu kaga abinda Allah zeyi, yanzu taso muje".

Babu musu ya miƙe ya dauki mukulin mota ya mikawa Safiyan suka fito inda motocin gidan suke, ya dauki ɗaya daga ciki suka nufi gidan Baffah. Tunda suka shiga mota Mashkur ya dafe kanshi dan ji yake yana mugun sara mai,  inallilahi wa'inna illahi raji'un ya furta yana fadin wayooo kai na  wuta suke zubamin a ciki innalillahi".
A birkice Safiyan ya taka birki ya riƙe Mashkur yana tofah mai Addu'a ganin Mashkur na saki ihu ya sa Safiyan saurin fita a motar ya shiga gidan Baffah da gudu yana fadin.

   "Baffah dan Allah zoka taimaka min mu shigo da Mashkur yana mota baida lafiya".
      Baffah dake kokarin shiga ɗaki ya saki labulen ya biyo bayan Safiyan yan a fadin" inallilahi wa'inna alaihi ra'jiun me yasa meshi haka ".
A riƙice ya nufi wurin mota suka ciroshi sai jujjuya kai ya ke yana wani'irin ihu mai ban tsoro, ciccibarshi suka yi suka nufi gida dashi.
     Umma na ganinsu ta shinfiɗa ta barma ta na salati da salallami dafa kanshi Baffan ya yi yana karanto mai addu'a. Sannu a hankali ya fara sauke wata irin a jiyar zuciya a gaggauce yana waige-waige, duban Safiyan Baffa ya yi yana fadin meyasa meshi haka?".

Wallahi Baffa allura ce ta tono garma ina tunanin al'amarin Mashkur akwai sihiri a cikinsa wanda sai dai Ubangiji, zuwa nai gida na sameshi ya fito yana kokarin barin gidan hannushi riƙe da mukulkin mota, shine ya ke sanar mun da cewa dama wurina zaije amma mu shiga ɗaki tunda na shigo, muna shiga ya ke labarta mun cewa ya yi mafarkin Fatima nan Safiyan yai wa Baffa bayanin abinda yafaru.
"Dama biri ya yi kama da mutum". Cewar Umma dake gefe tana riƙe da baki
         "Haba ace tun batan yarinyar nan ko kaunar maganarta baya ya yi ɗuk sanda zaka yi mashi magana sai yace shi a kyaleshi, toh Alhamdullilahi komai zaizo karshe tunda wannan karan ya buɗi baki da kanshi to baza mu kyale ba."

Baffah dake rike da kanshi yana sake tofeshi da addu'a ya miƙe ya nufi cikin ɗakinsa ya dauko wata gora cike da ruwa  ya zauna ya yi Bismillah ya shafe mai jikinshi da ruwa.

Mintina ƙalilan sai ga Mashkur ya soma dawowa cikin hayyacin, atishawa ya din ga yi a jere wani irin bakin hayaki na fita daga sassan jikishi. Fashewa da kuka Umma tayi tana fadin na shiga ukuna shikenan an kashe mun yarona wannan wani irin iftila'ine ya ke faruwa da shi Baffa hayaki fah yake wayyo Allah na Baba waye ya maka wannan ɗanyen aiki".

Rikota Baffa ya yi ya zaunar da'ita ya cire hular kanshi.
"Ki saurara da kukanan dan Allah muga yadda jikinshi zai koma yanzu addu'a ya ke bukata duk da ruwan da nabashi kankat ne wurin maganin duk wani sihiri dake jikin ɗan Adam idan har mutum zai yi wannan tofah wakara ka ce sahihiya".
Da sauri Safiyan ya furta Baffa "Wannan wacce addu'a ce haka dan naga da'a alama abokina ya dawo daidai dan naga yanzu kamar bacci ya ke".
Zama Baffa ya gyara yana duban Umma dake share hawaye. Safiyan ya kira ya na fadin "Manza Allah da kansa ya ce akwia wasu ayoyi a cikin Alkur'ani mai girma muddi mutum ya tsarkake jikinshi sai ya samu waƴanan abubuwa
1)A samu ruwa mai tsafta, ganyen magarya koraye masu kyau guda bakwai (idan an samu busassu sunfi), sai a nika a zuba cikin ruwan.

2) Sai a karanta suratul fatiha a cikin sa, kuma a dinga yi nunfashi yana shiga cikin ruwan.

3) Sai a karanta Ayatul Kursiyyu (aya ta 255 na cikin suratul Baqara).

4) Sai a karanta Suratul A’araf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122.

5) Sai a karanta Suratul Yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan aya ta 82.

6) Suratul Kafirun kafa daya

7) Falaki da Nasi kafa uku- uku.

8) Sai a karanta wannan addu’a
“Allahumma rabban-nas az’hibil ba’as ashfi wa antash-shafi la shifa’a illa shifa’uk shifa’un la yugadiru sakaman” kafa uku.

9) Sannan za’a iya karawa da wannan addu’a “Bismillahi urkika min kulli shai’in yu’uziyka wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika” kafa uku

10) Insha Allahu ta’ala idan aka karanta wadannan, kuma mutum ya dinga sha so biyu a rana safiya da yamma, ya kuma dinga wanka dashi a waje mai tsarki, ko kuma ya samu tawul ya jika da ruwan ya dinga gogawa a jikin sa, Insha Allah nan da sati guda kowani irin sihiri ne Allah (S.W.T) zai karya shi.

Basai mutum yaje wajen boka an danfare shi ba.
AYATUSH~SHIFAA
surorin qur,ani guda shida dake karya sihir ko asiri.

1.suratul tauba:ayata 14.
2.suraratul yunus ayata 57.
3.suraatul nahli:ayata 69.
4.suratul isra,i:ayata 82.
5.suraatul shu,ara:ayata 78~82.
6.suraatul fuslilat:ayata 44

Idan ka lazumce wannan tofah babu kai babu fadawa taskar sihiri sai dai wani hukunci na Ubangiji, yau kimamin kwanaki bakwai kenan idan har Mashkur zaizo gidanan to yana shan wannan ruwan a cikin ruwan fansar gidan, cikin ƴan kwanakinan na lura dashi kamar baya cikin hayyacinshi hakan yasa nadawo da zargina na shekarun baya akan anya ba sihiri akayi wa yaronan ya koma haka ba.



Fulani
Comment
Share
Paid book ne Naira dari uku (300), 6322646280 Aisha Adamu Fidelity Bank. a turo da shaida ta wannan number 09064234445 idan kuma kati ne a turo shima ta lambar
Free page.
Page 9

MAKIRCIN CIKIN GIDAWhere stories live. Discover now