🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩🍼
(KWANA ARBA'IN)
NA
MAMAN AFRAHFCW
🅿️1️⃣
Gabaɗaya ta jibge kayan cikin wardrobe ɗinta a kan gado, sai zuba wa take a cikin wata babbar bakkon kai da gani tamkar ƙaura za ta yi, sai da ta kwashi son ranta ta maida sauran. Akwatin ƙarfe ta ɗakko irin tasu ta mutanen da, kayanta ne na fita unguwa ƴan atamfofinta sabbi. Sai zuba kayan take tana ta faman murmushi gabaɗaya wani irin daɗi take ji a ranta
"Yau sai kwanan binni" Inna Azimi ta faɗa tana ƙoƙarin zige zip ɗin bakkon nata, hango sallayarta ya sanya ta dakata da zige zip ɗin ta ɗakko abin sallar tana cewa
"Kar in je in ke cewa a bani abin sallah dan ni bana son yin sallah sai a kan sallaya ta bare ma su yara da kunya kake bani-bani in da abinka kwa sai dai a ga ka ɗakko" Ta ce tana sanya sallayar ta dannata daƙer ta samu ta shiga saboda cika da bakkon ta yi.
Wanka ta shiga abin ta, tana ta sauri ta fito, kallon ɗakin kishiyarta ta yi ta yatsina fuska a ranta ta ce
" Humm ba zan faɗa miki ba jikata na naƙuda, ba sai dai ki ganni da kayana zan tafi birni in yaso baƙinciki ya kasheki, tun da ke baki da dangi a birni" Ta faɗa har da wani gatsine kamar wata ƙaramar yarinya.Ɗakinta ta shiga sai da ta shafa mai tsaf, ta sanya kwalli sai wani kallon ƙaramin mudubi take tana wani gyagygyara fuska tamkar wata ƴar budurwa. Sai da ta gama tsaf ta ɗakko atamfarta batik a linke a kan gado daman takanas ta fitar da ita saboda ta sanya idan za ta tafi.
Sanyawa ta yi a jikinta ta ɗakko ɗankwalinta irin na tsaffin nan ɗan kantu mai santsi ta ɗaura har da yi gwaggwaro a gaban goshi, ƙasan gado ta sunkuya ta ɗakko takalminta ɗan madina domin shi ne wanda take sanyawa in za ta gidan biki dan shi ne na ganin sarki, ta fiddo shi ƙofar ɗaki ta ajiye, ta ɗauki silifas ɗinta wanda ta cire duk ya wani tsufa ya katale, ta shiga da shi ɗakin ta sanya a ƙasan gado, madarar turarenta ta ɗakko ta shafa abinta, sai ta kwalbar turaren a ƙaramin aljihun bakkon tana cewa.
"Wannan sai ranar suna kuma zan shaga abuna, yo a kan me zan ke wari ranar suna a raina min hankali ganin daga ƙauye nake" Ta faɗa tana taɓe baki.
Sauran goranta ta ɗauko ta ɓantala tana ci ta ƙulle sauran ta saka a ƙaramar jakarta ƴar pos wacce jikarta Sadiya ta bata.
"Yauwa na gama komai bari in je in tambayo Malam, dan ma kar ya ji ya wai dan wallahi tafiya babu fashi" Ta faɗa tana fitowa ta nufi turakar mijin nasu da ke can wajen hanyar zauren gidan.
Kai da tsaye ta danna kai turakar Malam tana mai cewa
"Gafaranmu dai"
"Allah mana gafara" Cewar Malam yana kallonta mamaki bisa fuskarsa ganinta da shirin fita dan ya san biki ma sai na wanda yake da kusanci da ita take saka atamfofinta na adakar ƙarfe, hakan na nufin biki za ta ko sanar masa bata yi b ya faɗa a ransa.
Inna Azumi kwa sai da ta gama shigowa ɗakin ta lura da Tasalla da ke zaune a ɗakin sai lokacin ma ta tuna Tasallar ce da girki.
Wani kallo ta yiwa Tasallar ta ce
"Umm in ji mai ciwon haƙori" Ta faɗa tana samun wuri ta zauna. Shi dai Malam har lokacin kallonta yake da mamaki, sai da ta zauna ta ce.
"Sannu Malam" Kallonta ya yi tare da gimtse fuska sannan ya ce
"Yawwa sai ina, dan na san dai zancen gizo bai wuce na ƙoƙi tun da na ganki da shirin fita"
"Haba Malam, dama magana ce nake so mu yi" Ta faɗa tana kallon Tasalla dan so take Malam ya ce Tasalla ta fita dan bata so Tasallar ta san da tafiyar tafi so sai ta fiddo jakarta ta mata bazata.
YOU ARE READING
YAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA'IN
ActionLabari ne na barkwanci a kan wata tsohuwa da ke zuwa zaman wanka gidan jikarta