🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩🍼
(KWANA ARBA'IN)
NA
MAMAN AFRAH
🅿️8️⃣
Inna sai numfarfashi take, nishinta na fita ta kwanta lifet da ribda ciki, kawai jiran tsammani take, dan duk tunaninta aljanin ne ya shigo kawai neman inda take yake yi.
"Allah ka gani ZAMAN WANKA na zo, hanyar zumunci ne, idan kuma ba aljani bane mala'ikan mutuwa ne Allah ka yafe min kura-kuraina, ka haɗa mu a aljanna da Malam, ka sa ni kaɗai ce matarsa a can ban da Tasalla" Cewar Inna a zuciyarta.
Gabaɗaya ta sanya hannunta ta riƙe ƙafar gadon, duka hannayenta a jikin katakon suke, dan gudun kar aljanin ya ɓanɓarota daga ƙasan gadon. Har aka fara kiran assalatu Inna tana ƙasan gado Sadiya kwa bata falka ba, saboda kwana da ta yi ta waye tana gwagwarmayar naƙuda hakan ya sanya ta gaji bare haka nan ma nauyin bacci gareta.
'''IMRAN'''
Tun da ya buga ƙafarsa a jikin kujera ya ƙara razana Inna, jin ɗif a ɗakin babu motsinta hakan ya sanya ya gane ta mugun tsorata dan haka bai ma san lokacin da bacci ya ɗaukesa ba. Sai dai lokacin sallah ya yi alerm ɗin wayarsa ya fara masa sallama, tashi ya yi ya kunna fitalar falon ya fara kiran Sadiya sau boyu kawai ya kirata dama ba dan ya tasheta ya yi kiran ba dan Inna ta jiyo muryarsa ya san tana nan har lokacin a tsorace dan haka ɗakin ya nufo ya zo ɗaukan kayansa dan ya yi shirin tafoya masallaci. Daga setin da Inna take a ƙasan gado daga nan drower kayansa take, haka ya buɗe ya sanya kayan da ya yi amfani da su wajen tsorata Inna ya ɗora musu wasu kayan ya ɓoye su yadda ba za a gani ba ya ɗakko wami yadi riga da wando, ya juyo ya fito daga ɗakin sai dai ya yi matuƙar mamaki da Inna ta ji shigowarsa amma bata fito ba, kuma ya tabbatar idonta biyu, dan babu yadda za a yi bacci ya ɗauketa dan bata cikin kwanciyar hankalin da bacci zai ɗauketa.Sosai abin ma ɗaure masa kai da ya ga bata kan gadon, yana tunanin inda za ta ɓuya a ɗakin sai da ya je zai buɗe drower ne ya hangi rigarta a ƙasan gadon aikuwa kamar dai ya yi ta ƙyaƙyata dariya.
"Ashe ma abin naki tsoro ne ba dai ke MAI ZAMAN WANKAN da za ta addabi mutane ba ma ji ma gani wai an rufe tsohuwa da ranta" Ya faɗa a zuciyarsa ya fito falo ya sanya yadin da ya ɗakko ya fita domin yin alwala ya tadi masallaci.
'''INNA'''
Tun da Inna ta hangi hasken fitilar falo gabanta ya shiga faɗuwa dan duk tunaninta aljanin ne.
"Ya Allah ka makantar da aljanin nan kar ya ganni, idan kuma shi ba aljani bane mala'ikan mutuwa ne ka sa in cika da imani, ka haɗa ni a aljanna da Malam Allah ka sa ni kaɗai ce matarsa a can ban da Tasalla" Ta faɗa hawaye na gangarowa daga idanunta.
Har sai da ta ji Imran ɗin yana ƙwalawa Sadiya kira hakan ya tabbatar mata ba aljanin bane Imran ne ya tashi. Ta san jin Sadiya bata amsa ane ya taho ɗakin. Amma sai ta ƙyaleshi har ya gama uzurinsa ya fice.
"Babu abin da zai sa na faɗa maka akwai aljani a bayi, sai ka je kaima kun yi ido huɗu da shi ka gan shi ra'ayal aini, sannan in ga ƙarshen kurmanci dan na san yau in ka rinƙa ƙwanzama uban ihu sai duk maƙota sun ji ka sai ka gwammace kiɗa da karatu, dan yaro bai san wuta ba sai ya taka, yau za mu ga ƙaryar rainin wayo" Inna ta faɗa a ranta tana hasashen yadda Imran ɗin zai yi idan ya ga aljanin.
Shiru -shiru bata ji ihun Imran ba, abin ya bata mamaki dan ita mugunta ce ta sa ba za ta faɗa ba ma bare ya fs zuwa bayin, tana a haka sai ƙaran buɗe ƙofar gida ta ji ya fita masallaci, sosai ta girgiza da hakan.
YOU ARE READING
YAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA'IN
ActionLabari ne na barkwanci a kan wata tsohuwa da ke zuwa zaman wanka gidan jikarta