YAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA'IN

199 4 2
                                    

🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

       (KWANA ARBA'IN)

                 NA

  

      MAMAN AFRAH

  Na gode sosai da addu'o in ku gareni, da wanda suka min a grp da na pc har masu kirana ana tare masoya son so fisabilillah😍😍🙏

                🅿️6️⃣

  
       *Hajiya Amina*

    Tun da suka fito daga cikin gidan take ta yiwa Imran nasiha, a kan zaman Inna a gidan duk da dai an takureshi amma bata nuna masa hakan ba.

"Haba Hajiya kin dai san halin tsohuwar nan, tana zuwa ta tafi ma ya aka ƙare bare kuma a ce za a zauna da ita na wani lokaci" Ya faɗa yana kauda kai gefe dan maganar da yake ma ji yake kamar ya saki kuka saboda yadda yake ji, ba komai yake ɗaga masa hankali ba illa nesanta gangar jikinsa da ruhinsa wato Sadiyarsa.

"Duk da hakan da ma a lokuta da dama muna haƙuri da wasu mutanen wanda hakan ne kawai mafita, akwai mutane da dama wanda idan da ana biye halinsu ba za a zauna da su ba. Ka ga Inna tsohuwa ce, kuma ma a al'adance wankan jego ba wani sabon abu bane tun da ana yinsa bare kuma ita da ta haifi yara biyu dole tana buƙatar a taimaka mata musamman da haihuwar ta zama haihuwar fari ce"

"Yanzu ki ga fa abubuwan da Inna take yi tun a asibiti zuwa gida, a haka za ta taimaka mata kin gani dai hatta abincin mai jego ita ke cinyewa to ta yaya za ta bata kulawar da ta dace"

"To ko ma menene kai dai ka ja bakinka ka yi shiru kuma dai ai ba za ta iya cinye ko ma menene ba, dole akwai saura, sannan tun da kai kana nan yanzu hutu ake baka zuwa wajen aiki(School teacher ne) Sai kake yiwa Sadiyar wani abun"

"To" Ya faɗa kamar ba ya so.

"Imran kar fa in ji na san halinka, yanzu magriba ta yi ba wanka za su yi dukan su yaran an goge musu jiki da zaitun, ita kuma da yake jininta ya hau ɗazu da za a sallame ta nurse ɗin ta ce kar ta yi wanka, sai zuwa gobe, duk da dai jinin nata ya sauka amma dai har yanzu akwai kumburi a jikinta, bari in je" Ta ce ganin mai napep ɗin sai horn yake mata.

"Sauka lafiya ni ma masallaci zan shiga in yi sallah"

   Haka Hajiya ta tafi tana ɗan jin ba daɗi a ranta saboda tausayin ɗan nata da yanayin da ta ga fuskarsa tabbas ta san akwai damuwa a ransa duk da bai fito ya nuna hakan  ba.

Sai da ya je masallacin ma ya yi alwalar da aka idar da sallar magarubar ma sai ya zauna a masallacin ya ƙi tahowa gidan.

         '''MAMA'''

  Bayan fitar Hajiya ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta ce.

"Inna mu ma gida za mu tafi, tun da gaki, sai dai fa kin ga Sadiya babu abin  da ta ci sai ruwan shayi dan haka yanzu abinci za a bata"

"Haba Rakiya in ban da dai kina so ki ɗauki alhakina ya za ki ce haka, ni da na zo na tarar da ku a asibitin shin duk baku gabatar mata da abinci ba sai yanzu kike neman ɗora laifin a kaina saboda ga Inna kuka mai daɗin hawa ko?"

"Ba haka nake nufi ba Inna, kin san lokacin da kika zo ai tana bacci to tun da ta haihu ai bata sanya komai a cikinta ba, sai shayin da Hajiya ta bata"

"Amma kuwa yaran nan kun cika sakarkaru, wai dama kina nufin Sadiya babu abin da ta ci? Lallai in da ranka ka sha kallo, wallahi ya za a yi yarinya ta yi naƙuda da sunkuto ƴaƴa har biyu amma a barta da yunwa, ni duk zatona sai da ta ci wani abu sannan ta koma baccin, kuma da na ga ma ina tambayarta ta ci wake da shinkafar nan da na ga bata yi magana ba tunani na ƙam baki take irin na masu haihuwa kin san wasu basa iya cin komai idan suka haihu, yo da na san bata ci komai ba tun zuwanmu da na ɗora tukunya na tuƙa mata tuwo tun da shi ne zai fi riƙe mata cikin kin san cikin jego sai abu mai nauyi" Ta faɗa tana kallon Mama.

YAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA'INWhere stories live. Discover now