YAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA'IN

376 13 1
                                    

🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

       (KWANA ARBA'IN)

                 NA  

      MAMAN AFRAH

                🅿️1️⃣0️⃣

Last 🆓 page

     Wannan littafin kuɗi ne 300
  Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375  Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

'''MALAM'''

   Sai da aka yi sallar isha'i sannan ya shigo gidan dan tuwansa ma ƙofar gidan aka kai masa inda suke cin abinci shi da abokansa. Cikin gidan ya nufo bayan almajirai sun shigo masa da tabarma da butarsa cikin gidan dan dama yanzu basu da wasu yara a gidan sai almajirai. Duk an aurar da matan suna gidajensu haka ma mazan babu wani ƙaramin yaro yanzu. Sallama ya rinƙa kwalawa daga tsakar gidan Tasalla da ke cikin ɗakinta ta amsa masa dan yanzu dakyar ta daure ta ci tuwo kaɗan shi ma dan tana jin yunwa na neman kwantar da ita shi ne ta daure ta ci, amma ko tuwon ta ɗauka za ta sa a baki sai ta ji wani ƙululun takaici a zuciyarta dan tana tunanin Inna Azumi na can birni tana asuwaki da kaza.

Malam kuwa turakarsa ya sanya kai bayan ya ƙwalawa Tasalla kira kyawawa guda uku, haka ta tashi ta nufi ɗakin nasa tana kitsa yadda za ta yi kisisinar da zai barta zuwa birni dan ko sau ɗaya ne dai a rayuwarta ya kamata ta je birni ko da kuwa kwa Inna Azumi za ta tsireta idan ta je. Da sallama t shiga ɗakin ya amsa mata tana shiga ya ce.

"Wai ni Tasalla me yake damunki ne, ya za a yi ki bar ɗakin nan babu garwashi kin san dai ja fi so a kawu wuta ɗaki kafin in shigo gida ɗakin ya ɗau ɗimi" Ya faɗa yana kallonta.

  Shiru Tasalla ta yi dan ita gabaɗaya ma yau ta manta da zancen kaiwa wutar ɗakin na Malam.

  "Wallahi Malam sha'afa na yi ka san yau da gobe sai Allah"

"To sai ki je ki ɗakko yanzu idan baki kashe wutar ba in kuma kin kashe sai ki hura ko dai ki tafi maƙota ki samo" Ya faɗa yana ajiye hiraminsa  da ya cire.

" A'a ban kashe ba ma dai cire itacen ne kawai amma akwai garwashi bari in ɗakko maka" Ta faɗa tana ɗaukan ƙaton kaskon wutar Malam ɗin.

Sai da ta ciko shi da garwashi sannan ta dawo ɗakin ta maida ƙofar ta rufe dan dama al'adar Malam ce daga isha'i ta yi yake shigowa gida ya rufe sai kuma gobe in Allah ya sa ana raye. Sai da ya yi shirin kwanciya ya kwanta amma Tasalla tana gaban kaskon nan tana kara hannayenta a jiki tana jin ɗumin wutar.

"Wai kam Tasalla yau duk wani iri nake ganinki ko baki so Azumi ta tafi ba?"

"kai, kai kai, Malam bar faɗa dan Allah, ni da ƴar uwata Azumi abokiyar zamana mai zai sanya na ƙi son tafiyarta"

"Yau ɗin kuma Azumi ce ƴar uwarki Tasalla ko dai kin yi makuwa ne?".

"Ras nake wallahi, dama ai an ce zo mu zauna zo mu saɓa, amma ai ina ƙaunar Azumi"

   Zaune Malam ya tashi da sauri yana ƙarewa Tasalla kallo dan bai taɓa jin hakan ba daga bakinta ko a mafarki.

"Allah sarki ashe akwai ranar da Allah zai nuna min irin hakan nan ɗaya tana yabon ƴar uwarta ku da bakwa jituwa ko da wasa tun daga girmanku har tsufanku amma kuna faɗa sai gashi yau komai zai zama tarihi"

"Yoa ai ka san duk irin makaman yaƙin da mutum ya ɗauka idan ya ajiye nasa kaima ajiyewa kake, wai ɗazu baka ga shigowar Tsahare gidan nan ba?"

"Ni kwa na ga shigowarta dan har gaisawa mun yi"

"Wayyo ashe sai haƙata ba za ta cimma ruwa ba ashe sun gaisa ta faɗa masa me ke tafe da ita" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.

"Ashe ma ta faɗa maka saƙon"

YAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA'INWhere stories live. Discover now