👩🍼ƳAR ZAMAN WANKA🤱
(KWANA ARBA'IN)
NA
MAMAN AFRAH
🅿️2️⃣
Tun da ɗan acaɓan ya kaita tasha, ta biya shi kuɗinsa har gaban mota ya ajiye mata jakarta tana ta zabga masa godiya kamar wanda ya kawo ta kyauta. Mota na cika suka kama hanyar Kano, Inna Azumi ta samu wata tsohuwa mai shegen surutu irinta aikuwa suka rinƙa zuba kamar daman sun san juna, tafiya ta yi tafiya Inna Azumi ta fara gyangyaɗi a haka suka ƙaraso Tashar ƴan kaba ɗan sahu ta samu unguwa uku zai kai ta, suna cikin tafiya ta tuna cewa bata sanar da Mamar Halima ba dan dama ƙarya ta yiwa Malam a kan cewa ta ce ta taho, kawai dai Inna Azumi ta kira su gaisa sai take ce mata suna asibiti Sadiya na naƙuda shi ne fa ta shiryo ta taho ba tare da ta sanar da ita ba.
Ganin wayar babu caji ta mutu ta taɓe baki a zuciyarta ta ce
"Yo ya za a yi da ni, ni da gidan ɗana duk da dai ya mutu amma ai babu mai korata daga gidan jikokina, dole na je na tabbatar kar na fara zuwa gidan Halima(Sadiya) Na tarar an bar ta a gidansu saboda wankan jego, ko da kuwa ma hakan ta kasance dole na mayar da yarinyar ɗakinta na mata zaman wanka dan ba kasafai wasu mazan ke son matansu su je gidan iyayensu wankan jego ba" Tana cikin saƙar zucin ta lura sun kusa layin da za a ajiyeta, dan haka ta shiga nunawa ɗan sahun inda zai bi har dai suka ƙaraso ƙofar gidan, idanu ta ƙwalalo lokacin da ta yi tozali da danƙareran kwaɗo a ƙofar gidan ɗan sahu bai ankara ba ya ji ta ce
"Na shigenge ni Azumi"
"Lafiya dai Baaba" Ya faɗa yana kallonta da mamaki, ganin ta dage sai zabga salati take kamar an ce wani ya mutu.
"Yo ba dole ba na yi salallami ɗan nan ka ga gidan da na zo a rufe"
"Haba Baaba ya za a yi da ki taho baki sanar da mutanen gidan ba, gudun haka ne ya sa ake faɗa, gashi na ga da alama ma kamar ba a gari kike ba dan na ga lokacin da kika sauka daga mota"
"Wallahi kuwa ɗan nan ba a gari nake ba daga wani garin nake, amma na san inda zan same su, mu je tarauni"
"To Baaba" Haka ya juya kan napep ɗin suna tafiya tana ta faman surutu har suka kawo ƙofar gidan da ta nuno masa zai ajiyeta tun kan su ƙaraso.
"La'ilaha illallahu muhammadur rasulullahi S.A.W, yau dai na ga ta kaina wannan wane irin abu ne kamar an haɗa baki" Ta ƙarasa faɗa tana tafa hannuwa.
Ɗaga ido ɗan sahun ya yi aikuwa ya sauke a kan ƙofar gidan ashe nan ɗin ma a kulle.
"Gakiya Baaba kin taka fawul a ce ko ina babu kowa kamar basa son zuwanki" Ya faɗa yana tuntsurewa da dariya.
"Kai ɗan nan ka kiyayeni ni nan da kake gani can gidan ɗana ne nan kuma gidan jikata kuma na san inda suke suna asibiti jikartawa za ta haihu zatona duk sun dawo shi ya sa"
"To ki musu waya mana" Bani sa caji kai bari dai ka ga" Ta faɗa tana fitowa daga napep ɗin ta lissafa kuɗinsa ta biyashi kamar yadda ya faɗa, ya fito mata da jakar kayanta kamar yadda ta buƙata.
"Baaba ziyara kika zo ko ƙaurowa kika yi?" Ya faɗa cike da sheƙiyanci lokacin da ya ɗaga bakkon ya ji wani uban nauyi.
"Ka ji ni da ja'irin yaro to ina ruwanka" Ta faɗa tana juyawa ta shige gidan da ke maƙotaka da gidan Sadiyar, shi kuma ya ja ya tafi yana ta dariya dan hatta yadda take magana dariya yake bashi, ga wani uban gwaggwaronta kamar bututun zuba kalanzir.
Tana shiga suka gaisa da matar ta sanar da ita gidan Sadiya ta zo a rufe, nan matar ta ce suna asibiti tun da sassafe. Matar ta ce ta zauna kafin su dawo dan ta gane kakar Sadiya ce ta taɓa zuwa gidan sun haɗu lokacin ita Inna Azumin ta zo, cewa ta yi bari ta samu ko almajiri ne ya ɗakko mata jakarta.
YOU ARE READING
YAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA'IN
ActionLabari ne na barkwanci a kan wata tsohuwa da ke zuwa zaman wanka gidan jikarta