YAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA'IN

255 8 0
                                    

🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

       (KWANA ARBA'IN)

                 NA

  

      MAMAN AFRAH

                🅿️4️⃣

   "Kai jama'a shi kuma irin tasa baiwar kenan?" Inna ta faɗa gabaɗaya jikinta ya ɗauki karkarwa, musamman da ta ji Hajiya Amina ta ce wai wasu maciji ake haifa ɗayan kuma mutum.

"Wallahi sai ma kin buɗe kin gani da idaonki kin san an ce gani ya kori ji"
Cewar Hajiya Amina.

  Daidai nan Imran ya dawo riƙe da ledoji a hannunsa amma Inna ba wai ta ledojin take ba duk kwaɗayinta da son abin duniya sai ta ji duk bata cikin nutsuwarta.

  "Ni Azumi barni in mutu maza su kai ni ba mata ba, ai in kin ganni a lahira kaini aka yi" Ta faɗa tana ɗaukan Husainin ta miƙawa Mama ta ɗauki Hassan ɗin hannunta na karkarwa har yaron ya so kuɓucewa ya faɗi.

"Haba Inna ya za kike garaje a kan jaririn da aka haifa yanzu" Imran ya faɗa a fusace dan yanayin da Innar ta miƙo yaron tamkar wacce ta riƙo kashi.

"Jakar uban nan kayya, ɗan malafar uba ka ce fa, ashe dai kana magana rainin hankali ne yasa kake maƙe murya kamar ka haɗiyi rariyar tankaɗe, to dukana za kayi fa da hayayyaƙo min, yo wa ma ya sani ko haka bayanka yake irin na miciji abu a duhu, wa ma ya sani ko kai yaron ya gado na san ko haka naka bayan yake wannan yarinya Halima ba faɗa za ta yi ba, dan mu kaf danginmu babu masu fatar macizai"

"Me kika ce" Imran ya tambaya yana kafeta da idanunsa da suka masa jajir dan da ace matar nan bata da haɗi da matarsa wallahi sai ya shuka mata tsiya tunda ita bata san annabi ya faku ba.

   "Yo ni kwa mai na ce, abin da wancan ya ce shi na ce kirarin mai tsoro" Cewar Inna tana kawar da kai gefe.

  Hajiya kwa ta kasa furta komai dan yadda Innar ta jangwaɓar da yaron tamkar ɗan mutuntumi ba ɗan mutum ba.

"Ina ƴan uwan Sadiya Abdussamad wacce ta haifi ƴan biyu ɗazu?" Wata nurse  da ke tsaye ta faɗa tana daga tsaye kan barandar ɗakin haihuwar sai wani yatsina take tana taɓe baki.

"Gamu nan" Cewar Ashrof tana miƙewa tsaye.

"Haba Asharofa bakya barin in bata amsa dai dai da ita, to in banda raini ta kallemu duk mun haifi uwarta ma mun yi jika da ita ta wani mere baki, ina ƴan uwan Sa'adiyya" Inna ta faɗa tana gwada maganar matashiyar.

  Wani kallo nurse ɗin ta watsawa Inna, ta ce

"Ta falka ana buƙatar mutum ɗaya ya zo, dan sallamarta ma za a yi dan babu matsala" Ta faɗa tana gyara hijabinta da yake iya kafaɗarta.

  "Bismillahi ku bari ni in je tun da ni kaɗaice banganta ba, ku duk a nan na sameku" Inna ta faɗa tana miƙewa ta gyara ɗaurin zaninta tare da ɗankwali, ta daidaita mayafinta.

"Haba tsohuwa ya ana neman masu ɗan gwaɓi -gwaɓi za ki taso bayan ke ma da za a taimaka miki kina buƙatar taimakon, ta ya za ki taimakawa wani?" Ta faɗa tana kama tsantsa.

"Ke ki kiyayeni da ganinki ko auren fari baki da shi amma sai a ɗaukeku aiki saboda kun yi karatun masu jajayen kunne, ku ke karɓar haihuwa kafin ku je gidan miji kun gama haddace komai, kun san ta yaya ake haihuwa har kun ɗinkesu tamkar wata ƙwarya, to ni nan har gozomanci na yi a ƙauyenmu" Ta faɗa tana hawa kan barandar da za ta sadata da
ɗakin haihuwar.

"Inna dan Allah ki bari ko Mama ko Hajiya su je mana ke fa ko ɗakin baki sani ba" Ashrof ta faɗa tana marairaicewa.

"Ke rufe min baki matambayi ai baya ɓata, zan tambaya kuma ma Allah na tuba ko daga bacci na tashi ai bazan kasa shaida Halima ba, duddubawa zan yi har in ganta, ke ɗin da gulma ajali in ba a yi ba a mutu" Ta faɗa tana wani gatsinen gefen hanci.

YAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA'INWhere stories live. Discover now