.🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩🍼
(KWANA ARBA'IN)
NA
MAMAN AFRAH
🅿️9️⃣
'''TASALLAH'''Tun da Inna Azumi ta fito daga turakar Malam ranta ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, hankalinta ya tashi, ji take tamkar ta je ta dokewa Inna Azumi ƙafa ta karyata katsak ta ga da ƙafar da za ta tafi birnin, ta san dai duk nacin son tafiyarta ba ta tafi da ƙafa a karye ba.Ta so ta nemi alfarmar Inna Azumi a kan ta tafi da ita ko ta ga yadda birni yake amma kuma girman kai rawanin tsiya ba zai barta ta aiwatar da hakan ba, ko ma an yi hakan to kuwa ta san ba za ta tsallake zunɗen mutanen gari ba, a kan cewa ta tafi dangin kishiya shishshigi da neman ɗuwawun zama, bayan nan ta san duk sanda suka dawo ta jawa kanta gori har da gore-gore daga Inna Azumi wanda babu ranar ƙarewarsa .
Takaicin kishiyar tata take ta ƙoƙarin dannewa, wai har da cewa ta riƙa mata sana'ar ƙuli-ƙuli, wannan abu ya mugun tsaya mata a rai. Wato saboda ita basu da kowa a birni hasali ma bata san hanyar da ake bi aje birnin ba, shi ne Malam zai bata izinin tafiya ZAMAN WANKA har kwanaki hamsin saboda yana tsoronta.
"Tasalla ki cigaba da bani labarin mana ke d kike bani labari amma kin yi shiru kamar ruwa ya cinyeki" Cewar Malam ganin tun fitar Azumi Tasalla ta sunkuyar da kai ƙasa ita ba mai zaman makoki ba ita ba mai lazimi ba, gata nan dai kamar an dasa ta.
Dakyar ta danne wani wahaye da yake ƙoƙarin fin ƙarfinta, ta yi dariyar yaƙe ta ce.
"Ai a nan labarin ya ƙare" Ta faɗa kan nata dai a sunkuye dan tana ɗagowa hawaye ne zasu malalo mata.
"Ikon Allah ke fa kika ce mahaukacin ya biyosu suna ta shirgar gudu a titi ana ƙafa mai na ci ban baki ba, ai labarin daga ji ba a kai ƙatshensa ba amma kuma ki ce ya ƙare" Malam ya tambaya mamaki fal fuskarsa.
"Na ce maka a nan labarin ya ƙare" Ta faɗa ƙwalla na cika idanunta daf take da gangarowa amma ta hanasu fitowa dan kissa da kisisina, dan kar Malam ya ce dan Inna Azumi za ta je birni take yin kuka dan tun da ta share hawayen farko a ɓoye bata bari wasu sun biyo bayansu ba.
"To ai shikenan, bari na fita na ga tafiyar Azumi kar ta ɗauki ƙafa cewar ko tafiyarta ban gani ba, haka ya ɗora babbar rigarsa a kan kayan jikinsa ya fito ya barta, dai dai an ɗakkowa Inna Azumi kayanta.Tasalla kwa na ganin fitar Malam sai ta fashe da kuka tana jin ina ma ita ke ƴan uwa a birni ta zo tafiya Malam zai rakata ya ga tafiyarta a bi da ita ta tsakiyar gari tana washe baki.
Amma ina gabaɗaya danginta a ƙauye suke, Malam tana jin lokacin da Malam ke cewa Inna Azumi jakar nan kamar wanda za ta ƙaura hakan ya sanya ta tashi ta leƙo ta tagar ɗakin Malam ɗin aikuwa ta yi ido biyu da jakar Inna Azumi da ke shaƙe da kaya almajiri na riƙe da ita.
"Wayyo ni dama ban haɗa kishi da wacce take da dangi a birni ba da na huta da baƙincikin tafiyar Azumi" Ta faɗa a ranta tana sharar hawaye. Tun da Malam ya fita bai dawo ba har ta gaji da zaman ɗakin masa ta fito ta koma ɗakinta, dan lokacin da ta fito ma da ta yi tozali da ɗakin Inna Azumi rufe da kwaɗo sai da ta ji kamar ta yi ta zabga ihu da kururuwa mutane su kawo mata ɗauki, dan halin da ta tsinci kanta a ciki.
Tana shiga ɗakin ta zauna a ƙasa ta shiga rasga kuka kamar wata ƙaramar yarinya kowacce aka ce ubanta ya mutu, sai da ta yi mai isarta ta nemi wuri ta kwanta tana ta saƙar jaki, ta saƙa ta kwance, addu'a take ta yi a zuciyarta Allah ya sa Inna Azumi su faɗi a machine ta ji ciwon da zai hanata tafiya birni ZAMAN WANKA. Jin shiru-shiru bata dawo ba kuma ba a kawo mata wani labari ba ta san cewar Inna Azumi ta tsallake.Haka ta tashi tana ta ƙuncin rai ta ɗora tukunyar danbun rana tana jin a ranta cewar yanzu kenan ita za ta ke ta ɗorawa da sauke wa tun da Azumi birni ta ɗauka.
YOU ARE READING
YAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA'IN
ActionLabari ne na barkwanci a kan wata tsohuwa da ke zuwa zaman wanka gidan jikarta