COUSINS NE

3 2 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/CZDpCbctmI0GoJOqGRVNq0

🙆🏽‍♀️ *❤️COUSINS NE* 🙆🏽‍♀️❤️

*NA NANAHKHADII* 💅🏽🛍️


Page... 1&2

Yanayi ne na sanyi, duk wata bishiya kad'awa takeyi, hakkan yasa garin yayi d'ad'i, da wannan lokaci na bazara, hakanne yasa duk wani Dan adam, dake cikin garin sanye yake, da kayan d'ari....

Sharad'a phase 2 kenan, unguwa ce ta masu Hali, hakanne yasa ko ishasshen motsi babu, ba wani tafiya nayi ba na hanga, wani k'aton gidan sama mai farin Gate, koda nashi ga d'akin dana ji motsi na kutsa kai, kwance take kanta ko d'an kwalli babu, ta duk bak'in gashinta ya bazu a pillown da take kwance, duk hankalinta nakan instagram d'in da take kallo, hakanne yasa bata maji fitowan, Fateemeerh daga toilet ba, da haryanzu jikinta ke turiri,alaman ruwan datayi wanka dashi yana da zafi sosai, k'arasawa tayi tare da yarfa mata ruwan dake hannunta, sai time d'in ta d'ago ido tare da turo baki tana fad'in,  "wlh Fateemeerh bana son wannan d'a bi'ar taki, a sanyin nan ji yadda kika watsa min ruwa, ta k'are maganar tare da jan gutun tsaki, dariya sosai Fateemeerh tayi tana fad'in,  " waya ce ki kashe min room heater, kuma kinsan sanyi akeyi,  bata ko d'ago ido ba tana share, ruwan da ta zuba mata tace,  " kinsani fa idan najima dashi a d'aki jiri nakeyi and kin kunna, kusan hour 1 kinata zaune kink'i shiga, sai da duk abu ya hau kaina, Fateemeerh bata ce komai ba, dan tasan bata da gaskiya, wuce wa tayi gaban dressing mirror, ta gama goge ruwan jikinta, kafin ta fara shafa mai, shirune ya biyo baya, hankalinta kwance take shafa manta, saide kamar wacce ta tuno wani abu, da gudu ta mik'e ta dira bayan khadeejarh tana dariya, khadeejarh kam yi tayi kamar bata ji mutum ba, "ke ni wlh dad'ina dake fushi, kinsan meye? Sai lokacin ta juyo kanta ta kalli Fateemeerh, dake dariya kamar mara gaskiya,, " a'a sai kin fad'a,  "please karki ce a'a Dan Allah muje mu duba tsohuwa mai ran k'arfe mana, kwana biyu banji dramar ta ba, teb'e baki khadeejarh tayi tare da juya kanta, tana fadin, " a'a nikam bazan je ba, haka kawai ana zaune k'alau in nemo ma, kaina magana, ke kinsan daga ta ganmu zata fara maganar Aure, kamar mun girma duk wata budurwa dake garin Plateau, " ni dama nasan haka zakice idan ta fad'a yana fitowa a jikin mu ne? Kinsan yadda tayi zazzabin nan, idan bamuje mun duba ta, wlh duk randa ta shigo gidannan baza mu sha ruwa ba, to ma da kike maganar mita, ai ta kwararki ce, bai kamata kina gudun halinta ba, ai halinku iri d'aya ne, ta k'are maganar cikin zolaya, dan Allah muje mana,  nan nauyan ajiyan zuciya khadeejarh ta sauke, kafin tace  "to naji amma ba zamu jima ba, " yauwa yar uwata Dan Allah tashi kisa kaya mu tafi.

Sanda suka gama shiri tsab, dukan su cikin wata purple after dress, bbu wanda yayi make up, man baki dukan su suka shafa, amma hakan bai hana kyansu bayyana ba, d'akin Mamah suka nufa tare da yin knocking, izinin shiga aka basu, can gefe a k'asa suka zauna, kafin suka sanar ma da Mamah in da zasu, shiru tayi tana nazari kafin tace sai sun dawo, amma kar su jima, zuma cikin jarka ta d'akko ta basu tace, "karsu jima.

Koda suka fita, kamar marasa gaskiya suka fita, suna adduan kar suyi karo da Baba ya dawo, ya hanasu tafiyan k'afa, cikin sa'a kuwa har suka yi nisa babu kowa, nan saka saki ransu su kaci gaba da, tafiyar su suna hira.... Tunda idonsa ya sauka kanta yayi reverse, tare da juyi yana bin su, har suka shiga gidan Kakah....

Suna shiga wani k'amshin daddawa ya doki hancin su, kallon juna suka yi suna k'unshe dariyar su, ganin har zaku shiga parlour ne, Fateemerh ba daina dariya ba yasa khadeejarh fad'in...."kinsan idan ta kama mu muna dariyar nan ba barin mu zatayi ba, pls ki bar dariyar nan haka, da kyar Fateemerh ta saita kanta, suka shi ga, wani k'aton hotone black and white, da bai b'oye kyan ta a zamanin ta ba, na hanga kuma akwai kamanin ta ko ba bbu yawa a jikin, jikokinta guri sallama sukw tayi, kafin ta dogaro sandar ta tafita, tare da fadin,   "inata ansa muku ko baku da kunne ne? Dariya sukayi dukan su, tare da fad'in, "mu da muka zo duba ki karki mutu, baki fad'a mana in da kika b'oye kud'ad'ennan ba, sanda ta buga a iska tana fad'in, " ai bazan mutu yanzu ba sai kun kawo min jikoki na gansu, sai lokacin da tunda saka fara mgana Fateemerh ba tace komai ba tace, "mufa du baki mu kazo yi ba mgnar aure ba, kallon Fateemerh tayi tana buga mata sandar da bata iske ta ba, " ke dama baki da kunya, takwarata tafi mutunci, gara a aurar dake wannan bakin rashin kunyar ya mutu, dariya sukayi dukansu suka gaiaheta da jiki, ta ansa sun jima suna hira kafin sukayi sallar azzahar, har sun juya zasu fita ta kira su suka dawo, gefe suka zauna, sai kuma ta fashe musu da kuka,  "yanzu da ku da iyayen ku nayi nayi, ku fito da miji kunk'i sun daure muku gindi, wlh danaji sauki zaku ga abun mamaki, kallon juna sukayi kafin suka sauke ido, da kyar suka rarrasheta da alk'awarin kwannan zasu fito da miji, nan kuma zuciyanta tayi sanyi, harda saka musu albarka, suka lallab'a suka fita, suna dariya, tunda suka kama hanya bbu mai mgna, har sukayi nisa, sai can Khadeejarh tace,  "wlh yau dai sai naci abincin nan, kullun restaurant d'an k'ank'ani sai k'amshi, mu shiga mana ko takeaway muyi, turo baki Fateemerh tayi tare da fad'in, " ke wlh kin fiye kwad'ayi meye abin sha'awa a wannan gun? Kallonta khadeejarh tayi tace,  "ra'ayi riga wlh saina shiga nida kudina, bata ko saurari ansar Fateemerh ba ta shige, nan Fateemerh tagama yar mitanta ta bi bayanta.

Suna shiga yayi parking, gefen restaurant d'in, ya bi bayan su, zaune take hankalinta duk yana kan chatting, bata ko ankara da zaman sa, kan kujeran dake facing d'inta ba, dadda d'an husky voice d'in sa ne ya dawo da ita, daga duniyar chatting d'in da takeyi, d'ago ido tayi a razane suka had'a ido, ganin kwarjinin sa ne yasata saurin sauke nata k'asa, "sorry nabaki tsoro ko? Afuwan am Aleeyu by name nd u, wani fari tayi da ido kafin tace,  " Fateemerh, murmushi yayi yace "nice name, please naga ku biyu kuke tafiya, if am not mistake d'ayar nake nema, murmushi mai k'unan rai tayi tace, " ohh khadeejarh gata can tana oder acan, tana fad'in hka tare da pointing masa, khadeejarh dake k'arasowa gun, tunda ya kafe ta da ido, ya kasa daukewa harta k'araso, bata ko nuna taga mutum ba, dan ita tazata kwashe-kwashen Fateemerh ne tace, " malama mutafi ko? Fateemerh da tunda Aleeyu ya kafe khadeejarh da ido itama ta kafe shi da ido, sai tym d'in tace..." baki ga bak'o bane? B'ta rai tayi tace,   "am so ni dan Allah ki tashi mu tafi, murmushi Aleeyu yayi ya mik'e, tare da fad'in, " am Aleeyu by name, nariga naji sunanki gun k'warki, please do me favour, kiban num dinki karna cikaki da surutu, murmushi tayi, daya shi jin ya dace, saide tace, "kayi hkri bani da waya, Fateemerh naji haka tayi saurin cewa, " don't mind her, hka halinta yake ga num din, baice komai ba ya ciro wayansa, saide kafin sugama khadeejarh ta isa k'ofa, da sauri Fateemerh ta iske ta, tana fad'in,  "wlh baki da wayo irin mazannan da suke tsada har zaki tsaya kina jama aji? Harara ta watso mata kafin tace..."ke wannan ya dama, bbu wanda ya sake mgna har suka isa gida, anan Mamah ta ringa musu sun dad'e, cewa sukayi da k'afa suka je, nan tace ai bbu wanda yasa su, jiki a sanyaye suka wuce d'akin su....

*08039171989*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 09, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

COUSINS NE Where stories live. Discover now