*🪄AUREN MUTU KA RABA....!*
*"Mijinta ne dan ra'ayi cikakken dan boko,koda sukayi aure a farkon Auren ya nuna mata baya bukatar haihuwa daga gareta. Koda tay cikin zaisaka ta zubar kotana so ko bata so,sai gashi rana daya kwasam tay asarar mahaifarta na dindin din shikuma yay mata Alkawarin zama da ita "MUTUKA RABA". "Shin menene zai faru anan gaba da Allah ya zubawa zuciyarsa wata sabuwar sha'awar samun haihuwa..?*
CHAPTER 1️⃣
FCMB Bank kaduna.
6pm.Yammaci ne lokacin daf an tashe ma'aikatan first city monurment bank kenan ayayinda kowani ma'aikacin bankin ya fito cikin salon shigarsa na ma'aikacin banki, wanda yawancinsu sunsaka suits da necktie ne, wasu kuma sun saka kala kalan cooperate wears kowa nata kansa cikin gaggawa domin kai kansu gida.
Daga cikin hadadden motarsa kirar elegance datake sheƙi ya fito aciki hanzari cikin sigar shigarsa mai tattare da aji da burgewa wanda tun tsayawarsa da budewarsa motar kusan idanun kowa ke kansa tsabar kyaun da Allah ya zubawa halittarsa.
Dogo ne dirarre, mai madaidaicin jiki, shiba fari ba shiba ba baƙi ba
Saidai Allah ya zubawa fuskarsa kyau da kuma kamala. Kimtsatsen Sajensa daya sha gyara tare da bakin suman kansa masu matukar daukar ido suka dada kawatashi, yana da fareren idonu round and sexy wanda inya zuba makasu zaka rantse a buge yake tsabar layi da sanyinsu.Gaban wata karamar motar 406 ya dosa yana takunsa bisa sauri da tsari, wanda kayan jikinshi ma kawai abun kallone dan suit ne na designer giorgio armani, warm royal blue colour da yar cikinsa fara kal mai tsada,sosai suits din ta amshe sa cak cak ta rike shi tamkar domin shi akayi designing dinta duk dama bawani abun mamaki bane awajensa daya kasance yana saka tsadaddun kaya duba da sunan gidansu da ya fito na masu kudi.
yawancin kayan da yake sakawa masu aji ne wanda zasu bayyana shi a matsayinsa na jan namiji,shidai he is alwys looking officially elegant and matured bazaka taɓa ganin inda ya gaza wajen zuba wanka da cancare kwalisa ba duba da irin muhimmancin matsayinsa a bankin gabaki daya.
Yana isa gaban motar ya dan dakata tareda da kwankwasa glass din motar, daga cikin gilashin motar take kallonsa zuciyarta na mata wani irin ƙuna tare dajin karsashi, tare da jin tsananin haushin tuntsirewar da mafarkinta na kasancewa matarsa yay.
Tsaye yay yanamai gyara zaman suits dinsa looking soo nervous after some time ta sauke ajiyar zuciya snn ta sauƙe glass din motar ahankli, tana dagowa sama suka hade ido dashi alokaci guda tabi ta dauke kanta.
Wani irin haɗe rai tay ganin ya sako mata fuskan tausayi yanata kallonta dashi.
Muryansa a sanyaye Yace babe kina lafiya?
Shiru tayi Bata amsashi ba, yace..uve been ignoring me, magana nake son muyi..2 mintTun bai karasa ba ta daga mai hannu cikin katseshi Idonta dake a lumshe ta wara tare da cewa "Ive heard enough of u mr othman."
"Wai wani magana zamuyi dakai bayan wanda ni da iyaye na muka maka?"...Aure ne dai na fasa! Please go and Stick with ur wife Allah ya shiryeka kuma.
Kansa ya shafa cikin jin tashin hankali yace "tasneem kiyi hakuri ki saurare ni, wallhy karya matata take muku ba haka bane halina.
Wani kallo ta mishi snn tace "Karya?...hahaha
Toh uban me yasaka kayi shiru lokcin datake faɗa, "why didnt u defend urself? Mtsww. ,Kai malam abar ma wann maganan. Iyaye na sun riga sun yanke hukunci, sunce babu aure tsakani na dakai. period.Hanklinsa tashe Yace "ohhhh ohhh tasneem why are u not understanding me, sam baki ganewa..,toh ki dan karamin lokaci mana in wanke kaina...na rantse miki da Allah karya matata takeyi..i promise i wll win yr trust again, ina matukar bukatar karin auren nan,Lokaci kalilan kawai xaki bani kinji tasneem? Zan iyayin komi ko binki kamr jela kike so nayi i will do it.