_MUTU KA RABA.._
08060712446 chat only no calls please.
_CHAPTER 8..._
Bakaramin mamaki ne ya turnuke mahaifiyar othman ba musammn dataga irin tarban mutunci da nafisa tafara yi mata,jikinta a sanyaye daga ganinta kasan she is soooo shocked at nafisa's behaviour wanda tsabar irin tarban murna da abubuwan kirki data tarbeta dashi har saida itama tafara jin kamar ma karyane kawai maman isha ta gilla mata akan nafisa.
Cos how comes ace nafisa batamasan sunayi ba, ko irin fushin nan batayi bare kuma ta nuna wani alaman guilty conciense, kuma tana musu kirki haka kamar wani abu baiya faruwa tsakaninsu.
Tana cikin wann nazarin muryan nafisan ya katseta. Satar Kallonta kawai take ganin Tanata murmushi harta karaso da ita cikin hadadden falon nasu tanamai cewa. Mumy you're most welcome. Fatan hanya dai kalau?Ya aka bar mutan gida,You're most welcome, ma! Come, come and sit down.
Har kan kujera tamata iso bata ko daga kanta akan yadda matar take binta da kallon tsananin rudani da mamaki babayan ta zauna nafisa ta dauko mata jakarta na handbag ta aje mata adaf gefenta snn tace mata ina zuwa bari naje na kawo miki abun taɓawa nasan kin gaji.
Batama jira amsarta ba ta wuce kitchen jim kadan ta fito dauke da tray tana fitowa dede lokcin shima othman ya fito.
Mamaki ne ya turnukesa dayaga maman nasa dan bata gayamai zata zo Kaduna wajensu ayau ba infact kwama biyar din nan ma fushi take dashi bata daukar wayarsa
A mamakance Yace Mama dama kece."?What a surprise. Snnu da zuwa fatan dai gidan lafiya ya kuma gajiyar hanya?
Ta kallesa sama sama tace lafiya..sai bata kara cemai komi ba.
Nafisa ne ta aje duk abunda ta kawo akan table snn ta dauki cup ta zubawa surkanta mango juice mai sanyi ta mika mata a aladabce ta amsa ta rike batare da takai baki ba.
Nafisa tana murmushi ta dubi othmn snn tace i am so happy mama tazo mana, kai nasha mamaki ganin mama.. babe imagine dazun nan inata shiryawa araina cewa zanje kaduna in mata kwana biyu ashe ma tana tafe. Ure most welcome naji dadin zuwanki mumy kisha ruwan sanyi akwai zafi fa.
Tana ta maganan da fara'a ayanayinta, tsakanin uwa da ɗa kuwa sai satar kallon junansu suke acikin yanayin sacewar jiki da tsananin mamakinta.
Har Gwara othman ma yana iya mata yaƙe amma mamansa kam kasa iya fahimtar halayyar nafisa tayi a kwakwalta kwata kwata.
Aranta cewa take Anya nafisa zata iya aikata wayann mugayen abubuwan da aketa faɗa akanta kuwa?
Tunawa tay da cewa tun dacan datake zuwa taci mata mutunci akan rashin haihuwa ko ta xazzageta cikin habaici nafisa bata taɓa ramawa ko tay fushi ba. Nafisa yarinyace mai sakin fuska gata da kirki wanda ko ayanzu ma kirkin nata ne ya dada daure musu kai ita da danta othamn.
Tun faruwar Abun da akaywa su isha shikansa othman bai iya samun karfin gwiwar tuhumarta kai tsaye da maganan ba bare yasan ko eh itace din ta aikata.
Fushin da mahafiyar tasa takeyi dashi mai tsanani yasaka shi a damuwa sosai.
Ita kanta zuwa tayi yau taciwa nafisa mutunci snn ta fitar da ita agidan danta sabida abun ma mata ciwo ganin yadda danta ya dawo
shanyayye mijin tace wanda baiya iya ganin lefin matarsa.Saidai yanayin dataxo ta tarda nafisan cikin mutunci da fara'a sosai ya kashe mata jikinta sosai.
Tana cikin wann yanayi nafisa tace mama? Mama bakiji ba..
Atake Dukansu suka dago suna kallonta.
Tana murmushi mai sanyi tace dama kitchen zan shiga shine nace bari na tambayeki me kike son a dafa maki?