Chapter 12

283 38 42
                                    

ALHAJI USMAN BAKURA RESIDENCE
ASOKORO

A yau Sunday wuraren qarfe goma da rabi na safe Daddy ne zaune a dinning room tare da Mummy yayinda suke breakfast suna hira as usual. Abinci ne kala-kala masu rai da lafiya a gaban su.

A yau din dai daga Yasir har Nasreen babu wanda ya shigo yin breakfast. Yawanci dama weekends haka take kasancewa... that's the only time they get to enjoy a long sleep balle kuma jiya sun je bikin dinner din Marwa sun gaji. Su kan su iyayen sunyi lattin fitowa a yau domin kuwa Daddy bai tashi daga bacci ba da wuri shima.

Daya daga cikin masu aikin gidan ce ta shigo dinning room din cikin sallama yayinda ta qarasa wurin Daddy ta duqa har qasa ta gaishe shi sannan ta miqa mishi Newspaper ta yau.

Daddy wanda ya karbi Newspaper din har ya ajiye ta a gefe sai kuma na ga yayi saurin dauka yana kallon front page din cike da mamaki yace "what's this??"

Hoton Yasir ne da Ilham a gaban Newspaper din, Hoton da aka yi musu jiya a lokacin da yake gyara mata lafaya.

An yi rubutu kamar haka: 'The Young billionaire CEO with his Mysterious queen... who is she???'

Da sauri Mamy ta kalle shi tace "Sweetheart me ya faru???"

Miqa mata Newspaper din yayi yana murmushi yace "Babyn ki ne a gaban newspaper with his supposed new girlfriend"

Zuciyar Mamy wadda ta buga ganin hoton Ilham nan da nan ranta yayi mugun baci yayinda ta qura ma hoton idanuwa babu qyaftawa.

"Meye wannan???" ta tambaya ranta a bace yayinda ta dago ta kalli Daddy wanda yake murmushi.

"Ta ya zan sani sweetheart? amsar ki tana wurin Babyn naki"

"Yanzu me ya hada shi da wannan yarinyar a wurin biki when he is about to get married. Yana nufin bai san za'a baza hotunan nan ba?? idan Humaira ta ga wannan ya zata ji??? what's wrong with him for crying out loud??"

A daidai nan ne Yasir ya shigo dinning room din looking all disorganized... Gashin kanshi duk ya tashi yayi buzu-buzu. Babu shakka yanzu ya tashi daga bacci don kuwa ko wanka bai yi ba.

"Wai wa ya taba mun Mummy na ne???" ya tambaya yayinda ya qaraso cike da damuwa a dalilin yadda ya ji tana ta masifa tun yana kan hanyar shigowa dinning room din.

Daddy wanda ya kalle shi bai san lokacin da ya fashe da dariya ba and it got Yasir all the more confused.

Yana qarasowa wurin ta ne tace "wacece yarinyar da kake tare da ita jiya a biki??"

Confusedly yace "Mamy wacce yarinya??"

Newspaper din da ke hannun ta ne ta jefa a kan dinning table yayinda tace "Ni kake tambaya??"

Wannan shine karo na farko da Mamy take yi ma Yasir masifa haka. Sossai hankalin shi ya tashi ganin yanayin ta.

Da sauri ya dauki Newspaper din ya kalla and Lo.... sai ga hoton shi da Ilham.

Gani nayi ya qura ma hoton idanuwa babu qyaftawa. Da ganin yanayin shi zaka fahimci hoton yayi mishi kyau ne ba wani abu ba... toh fa!

Daddy wanda ya dago kai ya kalle shi ne yace "So tell us, write-up din da aka yi dagaske ne?? who is she??"

Yasir wanda ya kalli Daddy ne na ga ya sakar mishi murmushi yayinda ya kalli Mamy wadda take ta cika tana kumburi ya duqo yayi hugging dinta ta baya yace "Mamy don Allah kiyi haquri. Wannan din fa ba wani abu bane. Kin san yadda 'yan jarida suke da son gossip"

"Ba wani abu bane a wurin ka amma Humaira fa? kana tunanin zata ji dadi idan ta ga wannan?"

"It's not what it seems, trust me... I can explain" ya fada tare da breaking hug din ya zauna a kujerar da take gefen ta.

ILHAMWhere stories live. Discover now