Chapter 13

341 49 21
                                    

LATE BUKAR MAHMOUD RESIDENCE
GWARINPA

Wuraren qarfe biyar da rabi na yamma Yasir ne zaune a kan kujera one-seater na falon gidan wanda yake ta qamshin turaren wuta mai masifar sanyi da dadin qamshi. Hira yake ta yi da Mummy. Idan ka kalle su a wannan lokacin zaka iya rantsewa sun dade da sanin juna.

Asali dai kamar yadda Yasir yayi ma Ilham alqawarin zai zo har gida yayi ma Mummy bayani, he actually did. Ilham dai tunda tayi mishi jagora har falon nasu tayi introducing din shi wurin Mummy sai ta wuce daki abin ta. Har a wannan lokacin kuwa Mummy bata ga hotunan ba saboda a yau din bata shiga social media ba.. She was busy doing some accounting work.

Yasir dai bayan yayi introducing kanshi properly ne ya bata labarin abinda ya faru dalla-dalla tare da bata haquri akan yadda ya ja hoton 'yarta ya hau Newspaper da social media platforms kuma yayi mata alqawari hakan ba zai qara faruwa ba. Ko da ya nuna mata pictures din bata wani ga abun tashin hankali ba amma kuma sossai ta ji dadi na yadda abin ya zama mishi big deal da har ya zo don yayi mata bayani sannan ya bata haquri.

Mummy dai tunda ta ji yace mata Ilham tayi fushi saboda abinda ya faru ta sani sarai ko abun motsa baki bazata kawo mishi ba don haka da kanta ta shiga kitchen ta hado ta kawo mishi. Babu yadda bai yi da ita ba akan ta bari amma ta qi.

Aikuwa tun suna magana formally har suka saki jiki da juna suka shiga hira sossai. Halin Yasir ya birge ta matuqa. Dukda kasancewar shi yaron CBN Governor, baya da girman kai ko alama. Gashi yana da saurin shiga rai. Haka kawai ta ji tana son shi. No wonder Ilham is the way she is because of him... tabbas zata ji dadi sossai idan ya kasance sirikin ta but then, there won't be such thing tunda dai aure zai yi kamar yadda aka ce.

Yasir dai tuni ya bude Goran ruwa ya zuba a glass cup ya sha.

Kallon wani bowl yayi a cikin kayan ciye-ciyen da ta kawo mishi yace "Mummy meye wannan??"

Tana murmushi tace "Dambu ne na Kaza... da turanci they call it Chicken floss. Baka san shi ba??"

Analyzing dinshi ya fara yi yayinda ya girgiza kai tare da fadin "ban san shi ba gaskiya"

"try it and see... Qila zaka so shi"

Murmushi yayi yace "okay then"

Aikuwa yana kai dambun bakinshi ne ya lumshe idanuwa tare da fadin "wow.... this is tasty"

Mummy ta fashe da dariya yayinda tace "na San zaka so shi.. Favorite din Ilham ne. Tun tana qarama take son shi. Saboda ita nake yi"

"daga yau a sa ni a ciki Mummy... nima ina so"

"toh shikenan. Daga yau da kai zan dinga yi"

"Nagode sossai" ya fada.

Haka ya sa dambun a gaba yana ta ci yayinda suke ta hira. Kamar wasa bai san lokacin da ya cinye shi ba... Sai empty bowl.

Dago bowl din yayi ya kalli Mummy cikin 'yar qaramar murya yace "Mummy na cinye akwai saura?? ina so in tafi da shi"

Sossai ya bata dariya yadda yayi magana... He actually behaved like a small child.

"Akwai Yasir.. bari in kawo maka" ta fada yayinda ta miqe tsaye.

"Yauwa Mummy, Nagode sossai" ya fada cike da murna.

Haka ta wuce kicin tana yi mishi dariya.

Wayar shi ce tayi ringing yayinda ya duba.

Farouq ne... wanda Nasreen zata aura sannan kuma abokin shi!!

Da sauri yayi answering yace "abokina how far"

Shiru yayi yana sauraron shi sannan yace "Kayi haquri ina Gwarinpa ne, Aliyu ya zo ne??"

ILHAMWhere stories live. Discover now