Chapter 17

316 44 31
                                    

ALHAJI USMAN BAKURA RESIDENCE
ASOKORO

Wuraren qarfe tara da rabi Daddy da Mamy suna zaune maqale da juna a kan kujera 3-seater na babban falon Daddyn yayinda suke hira suna kallon TV.

Yasir ne ya shigo falon cikin sallama.

A lokacin da ya dawo gidan kai tsaye sashen shi ya wuce yayi wanka sannan ya shigo main house ya ci abinci shine ya zo wurin iyayen nashi.

Sanye yake cikin qananan kaya na wandon three quarter da Polo T-shirt sai baza qamshi yake yi. he looked so clean as usual!

Kai tsaye wurin su ya nufa tare da russunawa ya miqa ma Daddy hannu yace "Sannu da zuwa Daddy, Ya hanya??"

"Alhamdulillah Son.... Kayi kyau as always"

Murmushi Yasir yayi yace "Nagode Daddy"

Mamy wadda ta Harare shi ce tace "sai yanzu ka ga daman dawowa?? zauna ka fadi mun emergency din da ya hana ka dawowa kayi dinner akan lokaci"

Yasir wanda yake murmushi ne ya zauna yace "Yi haquri Mamy, wallahi Ilham ce..."

"what??" ta fada cike da tsananin bacin rai yayinda ta murtuke fuska.

Hakan ne ya sa Yasir yayi shiru yana kallonta confusedly.

Daddy wanda yake murmushi ne yace "Kana nufin Data analyst dinka???"

"Yes Daddy"

"Me ya faru da ita?"

Daga nan ne ya basu labarin abinda ya faru..

Mamy dai gaba daya ran ta a bace yake. Tabbas ta fahimci cewar Yasir is interested in the girl and she has to stop that nonsense.

"Allah sarki. Ya jikin nata??"

"Da sauqi Daddy.."

"toh Allah ya bata lafiya"

"Ameen" ya fada tare da kallon Mamy wadda ta murtuke fuska.

Girgiza kai yayi sannan yace "Mamy kiyi haquri"

"Ka dai san auren ka ya kusa ko???"

"Yes na sani Mamy"

"focus on it"

"I will" ya fada tare da kallon Daddy wanda yake kallon shi yana murmushi.

"Ka ci abinci??"

"eh.. sai da na ci sannan na shigo"

"toh shikenan"

"bari in je in kwanta.. I am tired"

"ba dole ka gaji ba.. ka je ka yini a asibiti saboda wata wadda ba kowa ba"

Murmushi yayi yace "Mamy Ilham is my data analyst, ma'aikaciya ce a kamfani na"

"whatever" ta fada yayinda ta mayar da idanuwan ta akan TV.

Daddy wanda yake murmushi ne ya kalli Yasir yayi mishi sign akan he should let it be.

Shima murmushi yayi sannan ya miqe tsaye ya nufi wurin Mamy ya duqo yayi mata kiss a kumatu yace "Good night my love"

"Good night" ta fada kai tsaye ba tare da ta kalle shi ba.

Kallon Daddy yayi yace "Sai da safe Daddy"

"Allah ya tashe mu lafiya, Please rest well ka ji??"

"I will in sha Allah"

Bayan ya fita ne Daddy ya kalli Mamy yace "wai meye matsalar ki da yarinyar ne?? kin taba haduwa da ita ne tayi miki ba daidai ba ko me??"

"Ni ban taba ganin ta ba, bana fata ma in hadu da ita. Kawai bana son yadda take zama very close to him ne. Aure fa zai yi, me zai sa ya zama so attached to the girl now??"

ILHAMWhere stories live. Discover now