Chapter 15

329 41 3
                                    

LIMI HOSPITAL
CENTRAL AREA-ABUJA

Kwance take a kan gadon dakin tana bacci yayinda Cannula take maqale a hannunta ana qara mata ruwa.

Yasir ne tsaye gaban gadon yana ta kallonta. Har a wannan lokacin bai gama samun natsuwa ba, He looked completely disorganized.

Mummy wadda take zaune a kan kujera kuwa sai kallon shi take yi tana mamakin level of concern din da yake nuna ma 'yarta. Mamaki take yi ace after all these babu soyayya?? Yana nufin duk cikin halin shi ne na taimako???wanne irin mutum ne shi kuwa???

Kusan minti talatin kenan da suka shigo dakin. Kamar yadda likita ya buqata, Mummy tayi mishi bayanin ciwon na Ilham. Ta fadi mishi duk wani abinda yake buqatar sani wanda hakan ya taimaka qwarai wurin tabbatar da kalan medication din da za'a bata.

"Duk laifi na ne da ban sa mata ido wurin cin abinci ba" Ya fada cike da damuwa.

"Babu laifin ka Yasir.. ta ya zaka san bata ci? Ilham tana da taurin kai. Kullum sai na kira ta na tambaye ta idan ta ci abinci sai tace mun ta ci. Na so in dinga yi mata packaging abinci tana zuwa da shi amma sai tace mun wai bata son abinci ya dade kafin ta ci shiyasa muka yi da ita zata dinga ci a ofis but clearly bata ci. Idan ka ga yadda nake fama da ita wurin cin abinci zaka yi mamaki...."

"In sha Allah komai zai canza Mummy. A kullum zan tabbatar ta ci abinci. daga yau na dauki responsibility to make sure of it"

Murmushi Mummy tayi sannan tace "thank you Yasir. Yanzu dai zo ka zauna ka huta. Kamar yadda likita ya fadi maka she will be fine. Da zarar ruwan nan ya shiga jikinta shikenan. I am sure zuwa dare ma likitan zai sallame mu"

"You think so??"

Mummy tana murmushi tace "Yes. so please kwantar da hankalin ka. Zo ka zauna"

Ajiyar zuciya ya saki sannan ya nufi kujerar da take gefen ta ya zauna.

"Mummy in tambaye ki??"

"go ahead Yasir"

"Zaki dan bani labarin Ilham?? yadda ta girma and all..."

Mummy wadda tayi dariya tace "why not??"

Daga nan ta fara bashi labari.

*******************

ASALIN ILHAM???

Abubakar Mahmoud wanda ake kira Bukar ya kasance dan qaramar hukumar Marte a cikin Maiduguri. Mahaifin shi ne dan Marte yayinda mahaifiyar shi ta kasance mutumiyar N'djamena a qasar Chad.

Bukar shi daya iyayen shi suka haifa a duniya. Mahaifin shi a wannan lokacin ya kasance manomi ne. Yana da qatuwar gona wadda yake shuka gyada. A duk lokacin da aka girbe ta kuwa har daga garuruwa ake zuwa ana siya. Yana samu babu laifi. Bukar dai ya taso yana zuwa makaranta sannan yana zuwa gonar mahaifin shi yana taimakon shi wurin supervising ma'aikata. A nan cikin garin Maiduguri yayi karatun shi tun daga primary har zuwa jami'a. Bukar dai tunda ya shiga makaranta na daya yake yi. Har ya gama karatu result dinshi mai kyau ne.

Da first class yayi graduating daga jami'ar UNIMAID inda ya karanci accounting. Yana gamawa yayi masters a bangaren Business administration.

Bayan ya gama karatun shi ba da dadewa bane ya samu aiki a FIRS a nan cikin garin Maiduguri. Abubakar yana da qoqari sossai. Nan da nan yayi fice a ma'aikatar.

Duka shekara daya da fara aiki ne aka yi mishi transfer ya koma Head office na Abuja.

Da farko bai so transfer din ba saboda gaba daya rayuwar shi a kusa da iyayen shi yayi ta amma Mahaifiyar shi ta lallashe shi ya tafi. A matsayin shi na namiji yakamata yayi building future dinshi da kyau and it's a very good opportunity.

ILHAMWhere stories live. Discover now