CHAPITER TWO 💖

13 1 0
                                    





💫🥀   HASKE BIYU 🥀💫
                      
( YAR JARIDA )


( A heart touching love story & destiny )



STORY & WRITTEN BY :

ANISH

Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
❤⚘ EXILED PRINCE  ⚘❤
    ( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

                      


BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

            








  PAGE 2 🥀 ❤
 
                   








Kallon ta da kyau momy ta yi , ta na shirin magana wayar Safa ta fara ringing
Hannu Safa ta kai ta dauki wayar ta na kallon screen din

Nan ta ga bakuwa number ce ke kiran ta
A hankali ta dago kai ta kali momy kamar ita ce ta kire ta sannan ta dawo da kallon ta kan wayar kafin ta daga kiran ta kai wayar a kunne ta na sallama

A daya bangaran kuma sai da a ka amsa mata sallamar ta sannan a ka daura da cewa " ina magana ne da Abokiyar hira  ? "

Kallon momy ta yi ta na zaro idanu ta na tambayar kanta ya a ka yi ya samu number din ta
Cen kuma sai ta bude baki a hankali kamar ba ta son maganar ta ce mishi  " e ita ce "

" yawwa barkan ki da wannan lokacin , ki na magana ne da shugaban gidan Tashar Tauraruwa da ke nan Abuja , na kira ne saboda ina yawwan kallon shirin ki saman kafofin yada zumunta , so zan so na baki damar ki yi aiki a tare da mu , zan turo miki duk karin bayani da ki ke bukata a Text da kuma adress din seat din mu , idan kin amince sai ki tardo ni gobe a office di na misalin karfe 10 na safe , nagode " ya na gama fadar hakan ya katse kiran ba tare da ya jira amsar ta ba

Baki saki ta ke kallon momy ta na zaro idanu ta rasa magana
" lafya wanene ya kira ki ? " momy ta tambaya ta na tsare ta da idanu

Wata yar siririyar kara ta saki ta na fadawa jikin momy ta rungume ta ta na fadin " momy , shugaban gidan Tashar Tauraruwa ne ya kira ni , ya ce in na shirya in aiki tare da su "

Cike da murna momy ta rungume ta ta na jerowa Allah godiya , dan ta san shi ne babban burin yarinyar ta ta

Sai da su ka ida rungume²n su sannan su ka raba jiki cike da zumudi mama ta ce " yanzu yaushe za ki je , a ina gidan tashar ya ke ? "

" gobe momy ya ce zai turo min adress din su , sai na tarda shi babban offishin su wajen karfe 10 na safe ya min sauran bayani "

" alhamdoulilah , abu ya yi kyau gaskia , amma fa ni ban san a wace jaha babban offishin su ya ke ba "

Ta na shirin mike wa ta ce " a Abuja ya ke momy "

Cak ta tsaya sakamakon hannun ta da momy ta yi
Da sauri ta juyo ta na fadin " minene momy ? "

Mikewa tsaye momy ta yi , duk yanayin fuskar ta ya sauya kamar wadda a ka turowa sakon mutuwa

" Safa,  Abuja fa ki ka ce ? "
" e momy Abuja " ta fada cikin ko in kula

Sakin hannun ta momy ta yi kafin ta ce " Safa kin shirya komawa Abuja bayan duk abun da ya faru .. ."

Da sauri Safa ta katse ta da cewa " don Allah momy kar ki ce a'a , ai ba wajen ba zan sauka so kar ki damu , na san dalilin da ki ke jin tsoron , amma wannan abun ya riga da ya wuce , su je su suka sani , wlh har ga Allah ni ban rike wannan abun ya rai ba , please momy don't stop me , kin fi kowa sanin shi ne babban buri na a rayuwa , kar ki hana min shi " ta kai karshen ta na marairaice fuska

HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) Où les histoires vivent. Découvrez maintenant