FIVE 💦

9 1 0
                                    

💫🥀   HASKE BIYU 🥀💫
                ( YAR JARIDA )

        




( A heart touching love story & destiny )





STORY & WRITTEN BY : MEERAH 👑✌❤



Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

❤⚘ EXILED PRINCE  ⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION 

👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY




TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

👇👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i














                    BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM













               PAGE 5 🥀 ❤

      

    








* UNITED KINGDOM  ( LONDON )















Wani tanpasheshen office ne na glass , mai bala'in kyau da girma
Komai na cikin office din sai kyali ya ke kamar , yanzu a ka ciro kayan da ga cikin ledodin su
Tiles din wajen sai kyali ya ke kamar ka zuba ruwa ka sha , ya sha mopping ba kadan ba , kai a takaice kun san yadda manya²n office din kassashen waje su ke to wannan ma haka ya ke ba sai na fada muku ba

A hankali a ka turo kofar glass din
Wani kyakyawan matashi ne ya shigo office din , kan shi a sunkuye ya na duba wayar shi ya na sanye da wasu kaya blue da ga saman su wata blouse Fara irin ta doctor , ya na sanye da face mask Fari

Kai tsaye wajen Desk din shi ya nufa ya zauna saman lalawsan chair din wajen , ya na ci gaba da latsa wayar shi

Ya na a haka wata baturiya sanye da kaya irin na shi ta shigo amma ita ba ta sanye da blouse

Ta na shigowa ta nufi bakin desk din da sauri ta na fadin " Doctor akwai matsala , mara lafiyan da a ka ma theater jiya har yanzu bai farfado ba " ta fada da turanci

Slowly ya dago da kan shi ya sa hannu ya zame face mask din shi
Allahuma Barik , Gaskia matashin nan ya hadu , skin din shi fara da ita , amma ba fari sosai ba ta so ta dan yi chocolate , ya na da dara daren idanun farare kal kamar madara kwayar cikin su kuma ash colour ce , ya na da dogon hanci mai kyau da dan karamin baki lips din shi pink colour ma su laushi kamar audiga , ya na da kontancen saje baki kirin , eyebrow din shi masu kyau a konce kamar shi ya zana su , ya na dogayen eyelashes sai su ka karawa dara daren idanun shi kyau , ya na da yar suma kadan amma ba sosai ba , dan a bayan keya kawai ya tsaya , gashin kan shi darck black ne har wani kyali ya ke da ga gani ka san ba kananan kudade a ke kashe mishi ba
Ya na da dan tsayi , ga kuma murdaden jiki kamar wanda ya samu horon kwararen soja , dan da ga gani bugu guda zai yi maka mai kyau lahira ta yi bako  a shekaru zai yi 33 years haka 

Dan guntun tsaki ya ja kafin ya ajiye wayar shi saman table din ya kali nurse din cikin wata zazzakar murya cike da nitsuwa ya ce " kun duba bugun zuciyar shi  " ya fada da turanci shi ma 

" eh ta na bugawa amma alurar da a ka yi mishi , ya kamata a ce ta sake shi yanzu " ta fada cike da shaku

" Léa , ki kontar da hankalin ba abun da zai same shi , ku dai ku tabatar da zuciyar shi ta na bugawa , zai farfado , ai dama alurar ta na kaiwa 24 hours so don't worry " ya fada cike da nitsuwa kafin ya sunkuyar da kan shi ya dauki wayar shi

HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) Où les histoires vivent. Découvrez maintenant