💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )( A heart touching love story & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
PAGE 43 🥀 ❤
▪WASHE GARI ⛅⛅
zaune duk mutanan gidan su ke cikin dining room , ban da Ali da Raïssa
yau tun karfe 6 ya tada mutanan gidan , ya ce yau a tare duk za su yin breakfast , Raïssa da Ali kuma ya ce su shiga kitchen su shirya musu breakfast , ko wanka ba su yi ba su ka shiga kitchena hankali Marwan ya ja wani dan karamin tsaki ya kai hannu ya buga table din da dan karfi ya na fadin " za ku fito ko sai na shigo kitchen din ? "
duk mutanan wajen sai da su ka razana , dan da ga ganin yanayin shi babu wassa a ciki
a haka Ali da Raïssa su ka fito kitchen su ka shirya breakfast din saman table , sannan Raïssa ta ajiye wa Marwan mug din coffee a gaban shi kafin ta juya ta koma kitten dincikin sanyin murya ya ce wa mutanan wajen " ku yi sauri ku tafi , kar ku yi late "
babu wanda ya ce ufan su ka fara yin breakfast
Marwan kuwa ya kai hannu ya dauki Mug din Coffee da Raïssa ta ajiye gaban shi , ya kai saitin bakin shi zai shacak ya tsaya ya na kallon screen din wayar shi da ke ajiye gefe , a hankali ya ajiye mug din ya dauki wayar shi ya fara karanta text din da ya shigo wayar kamar haka
* KAR KA SHA , SUN ZUBA WANI ABU A CIKI *ya na gama karantawa wani Text din ya shigo , shi ma ya karanta sannan ya ajiye wayar ya na sakin wani dan karamin murmushi ,
ya kai hannu ya dauki coffeen shi ya kai baki ya ci gaba da shasai da kowa ya kammala breakfast din shi sannan su ka tashi daya bayan daya su ka fice , Noor kuwa sai da ta yi wa Marwan da Twinkle kiss a kumatu sannan ta tafi
su na barin wajen Marwan ya kalli Twinkle ya ce " momy , ki na son fita yau ? "
dan zaro idanu Twinkle ta yi ta na fadin " Marwan fita kuma ? ni yaushe rabo na da fita , ni ko harabar gidan ban san yadda ta ke ba "a hankali Marwan ya riko hannunta ya kai saitin bakin shi ya manna mata kiss , cikin sanyin murya ya ce " momy , ba fa cikin prison ki ke , ki na da yancin fita , yau dai sai kin fita , dan haka tashi ki je ki shirya , ke da Sam ku tafi , ni zan je office akwai wani client da zan gani , bayan mun gama sai na tardo ku "
har ta bude baki za ta yi magana Sami ya riga ta cewa " yeah momy , ku je ku shirya yanzu mu tafi "
a hankali Twinkle ta gyada mishi kai kafin ta mike ta na sakin murmushi ta nufi stair ta Haye , yau tsawan shekaru goma rabon ta da ta fita gidan , har ta manta ya garin Abuja ya ke , kawai an kawo ta an garkame kamar wata prisoner
ta na barin wajen Marwan ya mike tsaye ya yi mika ya na fadin " Sam , ku je da momy , ina ga ni zan dan konta kafin na tafi office "
a hankali shi ma Sami ya mike ya na fadin " are you okay ? kontawa a wannan lokacin , ko dai ba ka da lafiya ne ? "
wani dan karamin murmushi Marwan ya yi ya na karasowa cikin parlourn ya nufi doguwar sofa ya haye ya konta ya na fadin " don't worry , kawai jiya na cika dare ne ina aiki , kawai ku tafi , kar ka damu "
gyada mishi kai Sami ya yi , dai'dai lokacin da Twinkle ta sauko stair , ta na sanye da wata tsadadiyar Abaya white color mai mugun kyau , ta yi Rowling veil din ta a kai sai tashin qamshi ta ke gwanin burgewa
VOUS LISEZ
HASKE BIYU ( YAR JARIDA )
RomanceLABARIN WATA YARINYA MAI SUNAN SAFA KE DA MUGUN SHA'AWAR AIKIN JARIDA , WATA RANA A KA SAKA TA REPORTING A KAN WANI DOCTOR MAI SUNAN DOCTOR AMAR MUSADEEQ , SANNU SANNU BAYAN HADUWAR SU KA FADA SOYAYYAR JUNA AMMA WANI MUGUN ABU YA FARU WANDA YA RABA...