SIXTEEN

7 2 0
                                    

💫🥀   HASKE BIYU 🥀💫
                  *( ~YAR JARIDA )*~

        



( A heart touching love story & destiny )






STORY & WRITTEN BY : MEERAH 🪻🩵


Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
    
❤⚘ EXILED PRINCE  ⚘❤
( LOVE MEETS POWER  ) 👑🔥




~*TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL*~

👇👇👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

~*TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION~ 
*
👇👇👇👇👇👇👇👇

                       https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY







BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM








               ~PAGE~ 16 🥀 ❤






Dan karamin tsaki Amar ya yi ya na kauda kai gefe ya ce " bro ni fa ba karamin yaro ba ne da za ka tsaya ka na tambaya ta ina na je "

" Okay , duk abun da ya faru da kai kar ka ce ban fada maka ba " ya na gama fadar haka ya juya ya koma cikin bedroom din

Da kallo Amar ya raka shi har sai da ya Haye saman bed sannan shi ma ya shigo cikin dakin , ya wuce toilet
After some minutes ya fito sanye da bathrobe ya shiga dressing room , jim kadan ya fito da ga shi sai short ya nufi bed geffen Assad ya konta

                 





* WASHE GARI ( misalin karfe 11 na safe )







                  * SAFA 💋






Zaune su ke cikin library din university , ita da Haoua da Djamila , Alhamdoulilah Djamila yanzu jiki an samu sauki , kuma duk yan gidan su sun sake mata fuska kamar ba a yi komai ba , sai dai yanzu ta zama shiru , maganar kirki ma ba ta yi , Sai dai ta yi zaune waje guda , ta yi zugum kamar gunki ta kurewa waje guda ido , da ta zauna ba abun da ta ke tunani sai babyn ta , har ga Allah ta so cikin nan kamar rayuwar ta , yanzu kuma ta rasa shi , ba ma shi kadai ba , ta rasa kimar ta , da darajar ta , saboda mutumin da ba tsakanin shi da Allah ya ke tare da ita ba , yanzu ya na ina ? Ya gudu ya bar ta , da cikin bai Zube ba , yanzu ita da babyn zai gudu ya bar su , ga shi ba wani halin kirki gare su ba  , ya za ta yi da shi , ci da sha suturar shi, karatun shi duk wa zai kula mata da su , ga shi har yanzu ba ta Kamala karatun ta ba , kenan sai dai ta hakura da karatun ta kula da babyn ?
( Allah ne kawai ya cece ki da ga wannan tubbun 😴😴 )

Ta yi nisa cikin tunanin ta ya jiyo Muryar Safa ta na fadin " Djami tunanin mi ki ke yi haka tun dazu ina yi miki magana "

A razane ta dawo cikin hayacin ta na fadin " no ! no ! ba komai "

Kare mata kallo da kyau Safa ta yi
Cikin sanyi ta riko hannun Djamila ta saki wani cool murmushi ta ce " okay , ki rage yawwan tunani kin ji , ga exams nan sun gaba to ya kamata ki maida hankali kan karatun ki "

Dan karamin murmushi Djamila ta yi ta na gyada ma Safa kai
Sakin hannun ta Safa ta yi ta na shirin magana kamar da ga sama ta jiyo Muryar Amar ya na fadin " ke ki na meda hankalin ki ne kan karatun ? "

Dum ta ji gaban ta ya fadi , a dubu dari ta mike tsaye ta juya ta na kallon shi
Ya na tsaye bayan ta , ya na sanye cikin trouser white colour , da t-shirt navy blue , ya saka wata face mask baki sai tashin kamshi yake yi

HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) Où les histoires vivent. Découvrez maintenant