💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )
( A heart touching love story & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH 🕊
【THE ROYALTY LOVE 🕊👑🌺】
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 : FREE BOOK
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ : PAID BOOK
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION
👇👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIMP A G E 20 🥀 ❤
Sun dauki wajen good ten minutes a haka kafin Safa ta ce mishi " minene hadin ka da gidan da mu ka je da safe "
Kallon ta ya yi ya na fadin " ke ya kamata na fara tambayar me ye hadin ki da su dan tun da mu ka je gidan yanayin ki ya sauya "
Sai da ta dan dauki lokaci kafin ta ce " ni na fara tambaya "
Murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " labarin ya na da tsawo gaskia ban san ta ina zan fara ba "
" fara da ga farko mana "Yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " okay zan fara da ga Farko , ni da Assad dai twins ne kamar yadda ki ka sani , Parents din mu duk haifafun Nigeria ne cikakun haoussawa ne , Mahaifin mu sunan shi Musadeeq Abdoul Qadir , mahaifiyar mu kuma Hassna , lokacin da su ka yi aure ina ga mahaifin mu ya na da shekara 25 , Mom kuma 18 , bayan sun yi aure sai da su ka dauki wajen one years ba su samu haihuwa ba , su na cikin ta biyu Mom ta samu cikin ta na farko , amma ba kai three months ba ya zube , ba su wani kawo komai a ran su ba su ka kai kukan su ga Allah cikin rahamar shi ko ba su kai ga yin two months ba ta samu wani cikin , a wannan karan ma ya sake zubewa , a yanzu ma ba su wani damu ba , asali ma bayan zubewar cikin , su ka bar Nigeria baki daya su ka koma UK da zama , bayan wani lokaci haka su ka sake wani cikin , yanzu ma ya sake zubewa , wannan karan ba su hakura ba sai da su ka je likita dan jin abun da ke damun su , nan doctor ya fada musu cewa , Mahaifar Mom ba za iya daukar baby ba , nan Doctor ya ba su shawarar su biya wata matar a dasa mata kon haihuwar su a mahaifiyar ta , sai ta haife musu babyn su in ya so da ga baya ko da biyan ta ne sai su yi , ashe lokacin da doctor din ya yi musu maganar akwai wata nurse me sunan Fatma da ta jiyo su , bayan sun baro hospital din nurse din ta biyo su har gida , nan ta fada musu cewar ta yarda a dasa mata kon haihuwar su , amma ta na bukatar kudin dan ta ci gaba da rayuwar ta a UK salary din ta ba ya isar ta kuma ta na da yan uwa da ta ke kula da su a Nigeria , ba musu su ka amince dan dama abun da su ke bukata kenan , a haka su ka fara zuwa Hospital a na Duba Mom har lokacin da ta samu ciki , a ka cire shi da ga jikin ta a ka dasa wa nurse din nan , a tare Mom da Dad su ka dinga kula da nurse din nan , har gida ta dawo da zama tare da su , a haka har lokacin haihuwar ta ya zo , ta haifi Twins maza kamanin su daya sai dai kwayar idanun su ta banbanta , nan kuma a ka samu matsala dan nurse din nan tsaye ta yi ta ce ta fasa ba ta son kudin a bar mata babyn ta , abun ba karamin tadawa Mom & Dad hankali ya yi ba , babyn nan ba na ta ba ne ita kawai ta yi sanadiyar shigowar su duniya ne amma babu daya me jinin ta , amma nurse din nan ta ki ta ce ba za ta iya rabuwa da su ba , sai da babyn nan su ka yi two weeks a hannun nurse din nan kafin a samu sulhu tsakanin su , nan Mom da Dad su ka hakura su ka ce za su iya bar mata baby guda , ta ba su gudan tun da su biyu ne , kuma za su ba ta makudan kudade yadda za ta kula da kan ta , ta kuma kula da babyn , har karatun shi ma sun dauki nauyin shi , jin hakan ya sa nurse din nan ta yarda , ta ba su babyn na farko , su na karbar shi ko kwana ba su yi ba a garin UK su ka shiga jet su ka koma RUSSIA da zama , ita kuma nurse din nan ta dauki babyn ta ta koma cikin ahalin ta da shi , nan kuma ta shiga sabuwar cakwakiya dan ahalin ta sun ce ba su yarda da yaron nan ba , dama ba karatu ta je yi ba yawwan banza ta tafi , duk yadda ta so ta kwatanta mu su yadda ta samun babyn sun ki yarda , haka ta dauki babyn ta , ta koma UK da shi , bayan na cika shekara hudu ta sake dawowa da ni Nigeria wajen Sister din ta wadda ita ce Matar uncle di na da mu ka je gani dazu da safe , da ga Nigeria kuma mu ka tafi RUSSIA wajen Mom & Dad di na , wani abun mamaki da mu je ka a ranar Mom ta haifi babys din ta da kan ta Twins kuma , ashe bayan tahowar su RUSSIA magani su ka fara nema har Allah ya sa su ka samu , mun yi One week a cen Momy ta ce za mu koma UK amma na ce ni ba zan je ba , zan zauna tare da yan uwa na , abun nan ya yi matukar kona mata rai har zubewa ta yi saman guyiwowin ta , ta na roko na kar na bar ta na yi hakuri mu koma , Nan ne Dad ya kawo shawarar ta bar ni a nan RUSSIA na yi karatu na , bayan na Kamala sai na koma cen UK wajen ta har na samu aiki , cike da zumudi na yarda saboda a lokacin da na ga Assad ji na yi kamar ba zan iya rabuwa da shi ba , shi ma haka ya ji cikin zuciyar shi amma sai ya danne ya na yi min fuska , ba dan Momy ta so ba ta hakura ta bar ni a RUSSIA ta koma UK amma duk bayan three months ta na zuwa gani na , sannu sannu na fara karatu a RUSSIA ni da Assad da kuma wani friend's din mu da ya zo da ga Nigeria shi ma , a haka har Wassiq da Wassif little brothers din mu su ka taso mu ka ci gaba da karatun mu a tare , Bayan wasu shekarun mu ka samu little sister kuma mai sunan Rahaf , amma mu na kiran ta da Puppy , lokacin da ta cika shekara 10 Mom ta rasu , a lokacin saura one years na Kamala karatu na na doctor , lokacin da momy ta dawo dan gani na ta ji labarin Mom ta rasu abun ya yi ma ta matukar Zafi , a lokacin har ta zauna a nan RUSSIA ta ci gaba da kula da Puppy saboda yanayin shekaru ga ta kuma ya mace kar ta taso ba uwa a kusa da ita , bayan na Kamala karatu na , sai momy ta ce za mu koma UK , ba yin da ba mu yi da ita ba a kan ta hakura mu zauna a RUSSIA mu zama family guda , Dad har rokon ta ya yi ta yarda ta aure shi dan su ci gaba da kula da yaran su tunda ai ita ma na ta ne , amma fir ta ki , ba yadda na iya dole na hakura mu ka koma UK , amma duk holiday din mu a RUSSIA mu ke yin shi ni da ita , kuma har izuwa yanzu ba ta taba yin aure ba , ni kadai ne yaron ta kuma ni kadai na rage mata dan duk ahalin ta sun rasu har sister din ta da ke nan Nigeria duk sun rasu shi ya sa ba ta son ina yin nesa da ita ko tafiyar nan da zan yi sai da Assad ya kire ta kan shi ya fada mata sannan ta hakura , wannan shi ne labari na , kin ji dalilin da ya sa na ce miki uncle di na bai san da zaman Assad ba "
VOUS LISEZ
HASKE BIYU ( YAR JARIDA )
RomanceLABARIN WATA YARINYA MAI SUNAN SAFA KE DA MUGUN SHA'AWAR AIKIN JARIDA , WATA RANA A KA SAKA TA REPORTING A KAN WANI DOCTOR MAI SUNAN DOCTOR AMAR MUSADEEQ , SANNU SANNU BAYAN HADUWAR SU KA FADA SOYAYYAR JUNA AMMA WANI MUGUN ABU YA FARU WANDA YA RABA...