💫🥀 HASKE BIYU 🥀💫
( YAR JARIDA )
( A heart touching love story & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH 🔥💦
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
P A G E 10 🥀 ❤
Dan karamin murmushi Sami ya yi kafin ya ce " sister wai me ya sa har yanzu ba ki sakin jiki da ni ? "
Daga kafadun ta ta yi allamun ban sani ba , kafin ta juya ta kali Snoopy ta ce " baby tashi ka je "
Ba musu ya diro da ga saman sofar ya girgije sannan ya fice parlourn da gudu
Ya na barin wajen ita ma ta mike ta na shirin barin wajenDa sauri Sami ya riko hannun ta ya janyo ta ta fado a jikin shi
" ki ba ni amsa mana kafin ki tafi , why ki ka tsane ni a yanzu , lokacin da ki ke baby saman cinya ta ki ke wassa ko kin manta , why ki ka daina yanzu " ya fada ya na kallon face din ta" i'm not a baby , so let me , kai da kan ka ka fada ni ba yarinya ba ce " ta fada ta na kokarin kwatar hannun ta
Sakin ta ya yi , dama jira ta ke , ta tashi da sauri ta yi baya ta na hararrar shi ta matse gera ta ce " tashi ka fice mana gida "
Komawa ya yi ya jingina a bayan sofar ya daura kafa daya saman daya cike da isa ya ce " in kin gaji da gani na sai ki bar gidan ga kofa nan "
Tsaki Safa ta yi kafin ta juya ta nufi hanyar stair
Da sauri ya ce mata " idan kin je ki sauya wadanan kayan kin ji ko "Yar karamar kara Safa ta yi ta na bubuga kafafun ta ga kassa kafin ta juyo ta ce " ka san Allah in ka kara yi min magana cikin gidan nan sai na kakarya , ka bari in na je gidan ku sai ka yi min rashin mutuncin da ka saba " ta fada da dan karfi kafin ta juya ta Haye stair da gudu
Shi dai Sami da kallo ya rakata har sai da ta Haye sannan ya yi yar karamar dariya ya ce " you'll be mine very soon " ya kai karshen ya na dan murmushi
▪After two days
FRIDAY : 7pm
▪Safa 💋
Zaune ta ke cikin motar ta , ta na tuki hankali konce , Doctor Badariya Moussa na zaune geffen ta , dan tun wajen karfe 6 su ka baro Garin Kaduna
Kallon Safa Doctor ta yi kafin ta ce " Na tambaye ki , ke ba diyar tsohon Président Abdoul Karim ba ce ? "
Da sauri Safa ta juyo ta na kallon ta , ta ma rasa abun da za ta ce mata
Cen kuma sai ta saki wani cool murmushi ta ce " ta ya zan zama diyar shi , bai fi 4 years ba da mu ka dawo Nigeria da zama , a UK na tasso " ta kai karshen ta na meda kallon ta kan hanyaJinjina kan ta doctor ta yi kafin ta ce " ta yu kin girma ai jini ba wassa ba ne , duk da ba ki kama da haoussawa , amma ki na jinin shi sosai "
" no gaskia ni ba jinin shi ba ce , an sha fada min haka sau dayawa , amma gaskia ba ni da hadi da shi ni ban ma san wanene ba , ko za ki iya fada min , na ji a na maganar shi "
VOUS LISEZ
HASKE BIYU ( YAR JARIDA )
RomanceLABARIN WATA YARINYA MAI SUNAN SAFA KE DA MUGUN SHA'AWAR AIKIN JARIDA , WATA RANA A KA SAKA TA REPORTING A KAN WANI DOCTOR MAI SUNAN DOCTOR AMAR MUSADEEQ , SANNU SANNU BAYAN HADUWAR SU KA FADA SOYAYYAR JUNA AMMA WANI MUGUN ABU YA FARU WANDA YA RABA...