SIX 🦋

5 0 0
                                    

💫🥀   HASKE BIYU 🥀💫
                  ( YAR JARIDA )

        







( A heart touching love story & destiny )









STORY & WRITTEN BY : MEERAH 👑❤





Marubuciyar littafin

TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

❤⚘ EXILED PRINCE  ⚘❤
              
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥







TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL

👇👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i





TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP

👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY

                        BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM










               PAGE 6 🥀 ❤










Ta na ci gaba da tukin ta , Ba tare da ta kale ta ba Safa ta ce " wane taimako kuma "

Haoua ce ta karbe zancen da cewa " Haba Safa ki rage wannan rashin yarda da mutanan na ki , yanzu inda momy ba ta karbi account number din su ba  ta turo musu kudin , kin san fa ba za su bar mu mu tafi ba , ko ba komai idan mun ma dattijon nan magana a hankali zai taimaka mana , dan da ga gani ya na da kirki , kin san fa mu ko kashe mu za a yi ba mu kudin biyan ice cream din nan , dan ni ko kudin kati ba ni da "

Yar karamar dariya Safa da Djamila su ka yi kafin Djamila ta riga Safa cewa " ke kudin katin ma ki ke nema , ni yau din nan Always di na su ka kare , ga shi ko dubu daya ba ni da a jiki na , Allah ta ki mai sauki ce , ke pretty da dai kin hakura ya taimaka mana ga shi yanzu kin janyo mana asara "

Dariya sosai Safa ta yi har da bugun steering motar ta
Hararrar ta Haoua da Djamila su ka yi kafin Djamila ta ce " kin ga ko wlh abun da ke gama ni da ke kenan  komi sai ki meda shi abun dariya "

Tsagaita dariyar ta Safa ta yi kafin ta ce " okay na ji Haoua ta ce ba ta da kudi , ba matsala na san ba ta da mashinshi ni amma ke fa ina wanda ki ke kira da baby , ba ya baki komai kenan " ta kai karshen ta na sake bushewa da dariya dai'dai lokacin da ta yi parking motar ta bakin kofar gidan su  Djamila 

Tsaki Djamila ta ja kafin ta bude kofar ta sauko da ga cikin motar
Har ta nufi cikin gidan Safa ta ce ta tsaya , ba musu ta dawo geffen Safa ta tsaya
Ta na tsayuwa Safa ta bude wani locker a cikin motar ta fido bandir din kudi dan dari biya biyar ya kai dubu dari biyu ta bawa Djamila
Cike da murna Djamila ta karba ta na yi mata godiya kafin ta juya ta shiga cikin gidan su ita kuma Safa su ka yi gaba 

Su na tsaka da tafiyar su Haoua ta kali Safa ta ce " yanzu pretty dama ki na da kudi cikin motar ki , shi ne da card din ki ta ki kamawa ba ki zo kin dauke su kin biya ba ? "

Sai da ta dauki lokaci kafin ta ce " ba ni son taba su , sai in ya zama urgent ne na ke daukar su , wannan dan karamin abu ne shi ya sa na kira momy "

Jinjina kan ta Haoua ta yi kafin ta juya ta kali titi , da ga haka ba wanda ya sake cewa wani abu har su ka karaso gidan su Haoua

Ta na shirin sauka Safa ta tsaida ta , sannan ita ma ta ciro kudi ta ba ta dubu dari biyu
Murmushi Haoua ta yi kafin ta karba ta na yi mata godiya

Jinjina kan ta Safa ta yi kafin ta juya da kyau ta na kallon Haoua ta ce " Haoua ba zan miki karya ba , ke da Djami ku kadai ne friends ni a rayu kuma Allah ya sani da zuciya daya na ke zaune da ku "

HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) Où les histoires vivent. Découvrez maintenant