🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄
©️Salma Ahmad Isah
SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah @WattpadPage-10
ARMAN.
A rana ta gaba ma haka suka ci gaba da tafiya a cikin dajin, kasancewar suna duba taswirar da tsoho ya basu yasa ba su ɓata hanya ba ko sau ɗaya. Har rana ta biyu a tafiyar tasu ta ƙare babu wata matsala da ta samesu, ko wani baƙon abu da ya ziyarce su, sai a rana ta uku, ranar da suke hasashen iske ƙauyen Askar wani baƙon lamari ya riskesu a hanya.
Tun cikin daren ranar ake iska me ƙarfi, wadda take tafe da ƙura da kuma sanyi me shiga jiki, kuma tun a safiyar ranar iska ta ɗauke tentunan da suka kafa, lokacin da suka tafi naiman ruwan wanke jikunansu, sanda suka dawo suka iske babu tentin iska ta ɗauke.
Sa'arsu ɗaya, jakukkunansu ba su cikin tent ɗin lokacin da iska ta yi gaba da su, cike da salallamin rashin tent ɗin suka haɗa kayansu suka ci gaba da tafiya, dan yanzu abin ma ya fara zame musu jiki, har sun fara sabawa da yanayin tafiyar.
Suna tsaka da tafiya a tsakanin wasu bishiyoyi suka fara jin kuwwar wasu mutane, Adam ne ya fara jiyo kuwwar, hakan yasa ya ankarar da sauran, sai suka tsaya suna duba kewayen da suke, wai ko za su ga ta inda masu kuwwar za su ɓullo. Amma har bayan shuɗewar daƙiƙu biyu babu alamar komai. Sai da suka sakankance sannan suka ji faɗowar abu daga sama tim!.
Hakan ya sa suka ƙara razana, Arman ya turasu bayansa domin basu kariya, yayin da yake kallon ta inda abin ya faɗo, girman idonsa ya rage yana kallon mutumin dake tsaye a gabansu, alamun dai shi ne ya faɗo daga saman. Tun daga kan kwarjallen dake ƙugunsa zuwa rigar dake sanye a jikinsa duka na fata ne, kuma fuskarsa a rufe take, shi yasa ba su iya banbance kamarsa.
Kafin su yi wani yunƙuri wasu mutum uku dake sanye da kaya irin nasa suka sake dirowa daga saman bishiya, Arman ya sake kare Ivana da Adam da suke a matuƙar tsorace, shi ma kansa a tsorace yake, amma dole ya ɓoye tsoronsa domin kare abokansa.
Kallon-kallo aka tsaya yi, su suna karantar kama da kuma nau'in tufafin dake jikin mutanen huɗu, yayin da su ma suke kallonsu, dan za su iya cewa tun da suke fashi a hanyar, tsawon shekaru tara, ba su taɓa ganin mutane masu kama da waɗannan ba, bawai dan sun banbanta da mutane ba ne, a'a su ma kamar mutane suke, amma kalar tufafin jikinsu shi ne abin mamaki... Sai dai mamakin son sanin su wasu nau'in mutane ne ba shi zai hana su ƙwace duk wani abu da suke tafe da shi ba, dan haka wanda ya kasance shugansu ya miƙa musu hannunsa, cikin larabcinsa me kyau yace.
“Ku bamu kayanku!”
“Kaya?”
Adam ya maimata.
“Ku bamu kaya ko kuɗi, idan ba haka ba ku yi ta ranku!”
Dariya ta so kama Adam, dan shi ne ya fara fahimtar wasu irin mutane ne. Camera ɗinsa ya fitar ya shiga ɗaukansu a hoto. Yayin da su kuma suka shiga kare fuskokinsu saboda hasken flasher da Adam ke haskasu da ita.
“Adam me suke buƙata ne?”
Ivana ta tambaya tana kallonsa lokacin da ya gama ɗaukansu a hoto yana dariya.
“Wai 'yan fashi ne”
Ita kanta sai da abin ya so bata dariya. Ganin suna dariya ya harzuƙa 'yan fashin, ai rainin hankali ne ma, ya za'ayi su tambayesu kudi ko kayan kuɗi su zauna suna musu dariya. Hakan yasa suka fitar da makamansu masu firgita bil adama, suka yi kansu da shi. Amma Arman bai bari sun kai ga cutar da su ba, dan cikin azama shi ma ya fitar da nasa takobin ya nunasu da shi.
“Kada ku sake ko da taku ɗaya zuwa garemu, duk wanda ya sake kuma zan raba kansa da gangar jikinsa”
Ya faɗi a dake yana dubansu, juna suka kalla, dan ba sosai suka gane abin da yace ba. Ɗaya daga cikinsu ya sake yin wani takun zuwa gaba. Cikin ƙwarewa da iya sarrafa takobi, Arman ya juya takobin a hannunsa, sannan shi ma ya nufe shi, yana zuwa dab da shi ya kare farmakin da ɗan fashin ya kawo masa, sannan ya jujjuya takobin da hannunsa ɗaya, ya kai masa suka a gefen ciki, shi kansa bai ɗauka cewa zai iya samun wurin da ya hara ba. Domin bai taɓa amfani da takobin gaskiya ba, amma sai ga shi ya samu gefen cikin ɗan fashin.
YOU ARE READING
JUYIN KWAƊO
AventuraShin kun taɓa tunanin cewa wata rana rayuwa za ta muku juyi, irin juyin waina a tanda?. Tamkar yanda rayuwar kwaɗo kan yi juyi daga ruwa zuwa ruwan zafi?. Wani hali za ka tsinci kanka a sanda ƙofofin mafita suka kulle gareka, yayin da kake tsaka da...