DOGARO DA KAI
HAKKIN MALLAKA (M) AYEESH CHUCHU
July,2016
{1}
Auta! Auta!!Auta!!! Wai baki ji na ne?", Cewar wata 'yar dattijuwa da ke zaune akan kujera mai cin mutum biyu. Daga can 6angaren ta ce "Momi gani nan zuwa bani son cake din ya k'one ne ya kusa gasuwa".
Murmushi dauke a fuskarta ta ce "Zainab uwar son kudi". Ta ce "La Momi ai ke kika nuna man hanyar neman kudin,I can't live with an empty hand. Hikima ta jarina Momi".
Murmushi ne kwance saman fuskarta, tana jinjina kwazon ɗiyar tata.
Zainab ce ta fito da farin bokiti wanda ana hangen abinda ke ciki, ta isa gaban mahaifiyarta tace "Momi asa man albarka".
Momi ta buɗe bokitin, ta dauko cake ɗaya da fork ta kai baki. Tare da furta "Mmmm My Baby is the best cake maker, Allah shi kawo kasuwa".
Tsalle tayi ta ce "yeeeeee Momi nagode kwarai".
Wani corridor ta bi ta shiga ɗakin baccinsu,blue din mayafi ta dauka da ya dace da kalar duwatsun da ke jikin bakar doguwar rigarta, ta nannada a kanta, ya sakko zuwa kafaɗunta. Takalmi flat blue ta dauko samfurin channel, tasa a santaleliyar kafarta. Turarenta na New white oud da Dalila ta fesa tare da fitowa daga ɗakin.
Bokitin ta dauka tace "Momi zan kai cake ɗin MAINASARA SUPERMARKET, daga nan zan wuce gidansu Jidda".
Momi ta ce "a dawo lafiya, ki dai kula kar ki kai maraice kin dai san halin mahaifinku".
Ta gyada kai cike da gamsarwa, ta fita.Isar ta supermarket ɗin ke da wuya, ta shiga ciki bayan sun gaisa da mai tsaron ta ce "Auwal ga cake dina nan, na dubu uku ne cif". Yace "Angama gimbiya Zainab sai aban alakoro". Ta yamutsa fuska ta ce "Kana daukar daya cikin kudinka". Dariya ta kuɓuce ma shi, yace "yanzu dai ba za ki bani ba". Tace "dauki ɗaya dai ba dan halinka ba".
Ta yi ma shi sallama ta wuce gidansu Jidda. Da sallamarta ta shiga gidan bayan an amsa ma ta, ta ida shigowa. Ta isa har gaban matar dake zaune a baranda kan tabarma ta ce "Mama ina yini?", ta ce "Lafiya lau Zainab, ya su Hajiya?". Ta ce "duk lafiya lau su ke, suna gaida ki".
Ta ce "sai ki ka iske mutuniyar ta ki sun fita yanzun nan ita da babanta siyayyar makaranta".
Zainab tace "kuma bamu haɗu ba ina can wajen shagon Mainasara".
Ta zauna suna fira da mama. Tayi kamar awa guda, ta ji k'arar mashin alamar dawowar su.
Mama ta ce "gasu nan ma sun dawo".
Suna shigowa Zainab ta tashi ta amshi kwalin da ke hannun mahaifin Jidda, ta kawo kan tabarma. Sannan ta gaida shi cikin girmamawa.
Jidda ta ce "Dhosti hala kin dade a gidan nan?", Zainab ta kaɗa kai tace "na dan dade muna fira da mama".
Jidda tace "mun je siyo kayan tafiya school ne, kin gama shirin ki ko? Kin san dai jibi ne zamu koma".
Zainab tace "a'a sai Daddy ya dawo in amshi kuɗin gobe sai ki raka ni muje tare, in kuma Momi ta je shikenan".
Nan suka cigaba da hirar su ta aminan juna.A hanya ta na tafiya ita kadai tana tunanin yanayin rayuwar gidansu Jidda, duk da ba wasu masu kuɗi ba ne, amma suna da rufin asiri, ga shakuwa da kaunar juna a tsakanin su. Ta tuno yanda mahaifin Jidda ke zama suyi hira yana basu shawarwari na rayuwa.
Ta tuno na su gidan da kan su ke a rabe, babu zumunci da shakuwa a tsakanin su. Kowa sabgar gaban shi yake yi. Kudi Allah ya hore ma mahaifinsu dai-dai gwargwado wanda yana cikin sahun masu kuɗi a garin Gusau. Amma hakan be sa ya cika hakkin da ya rataya a wuyan shi na iyalinshi ba.
chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchuVote and comment.
Love 😍 y'all 😘.
YOU ARE READING
DOGARO DA KAI
RandomIt's a Hausa story, based on self confidence, love, business, Hausa culture and lot more. Zainab yarinya ce da ta Dogara da kan ta, ta dalilin sana'ar da take takama da ita. Hakan yasa 'yan uwanta matasa su ke koyi da ita wajen ganin sun dogara da k...