DOGARO DA KAI
©Ayeesh Chuchu
August, 2016{20}
Abubuwan motsa ta kawo ma shi, jere suke a cikin tray.
Mikewa ya yi ya karbi tray ɗin.
"daga yanzu zan fara aikina".
Ta zuba ma shi Macaroni casserole hade da coleslaw, ga pepper chicken a karamin bowl, sai kunun aya da zobo drink,gefe kuma samosa da springrolls ne naɗe cikin foilpaper.
Kallonta ya ke yanda ta ke komi na ta a nutse.
"Cheri Bismillah".
"za ki shagwaba ni Babe".
"ba dole na ba".
Yana ci su na firar su gwanin ban sha'awa. Ya na ta santin abincin.
Da zai tafi har bakin mota ta raka shi, hannunta dauke da samosa da springrolls da ke cikin foilpaper. Ta zagaya dayan gefen motar ta ajiye.
Hannu ya sa bayan motar ya fiddo leda da aka rubuta "You're my happiness".
Ya mika ma ta, ta girgiza kai.
"ya yi kadan ko?".
Murmushi ta yi ta ce "ka daina faɗin haka hidimar ta yi yawa".
"in dai akan ki ne ba zai taɓa yin yawa ba".
Ta amsa tare da yin godiya.
Da kyar su ka rabu da juna.
Kan gadonta ta zazzage kayan, kwalin cakulet (chocolate), set ɗin turaren DAISY MARC JACOBS cikin pack ɗin su mai kyau haɗe da flower a jiki sai dankareriyar agogo kirar TISSOT kalar baki da ruwan kasa guda biyu cikin ma'adanarsu.
Murmushi ta yi ganin yanda Samir ya gama sanin kyautar da ke birge ta. Jin son shi take yana bin ko wane sashe na jikinta.
************
BAYAN WATA BIYAR
Shago ne makeke akan titin premier road da aka rubuta ZG FASHION DESIGN da kyalkyalin golden a jiki. Shagon ɗinki ne da ya dace da tsarin zamani da kuma shagunan ɗinki irin na kasashen da su ka cigaba.
Daga an shiga shagon kujeru ne na karfe ma su kalar pink da purple kalar fenti da wallpaper da ke manne a bango. Gefe guda wani matashi ne zaune akan kujera irin ta office da takardu a gaban shi.
Daga an shiga ciki anbi wani dogon corridor symbols ne mai dauke da Manager's office daga hannun hagu, cashier's office na bin shi, sai Media Department. Daga hannun dama CEO ZG aka rubuta daga sama,Gallery, Store.
Sai can gefe makeken fili ne dauke da kekunan ɗinki na zamani. Ma'aikata na ta aikin dinkin su, maza da mata.
Sanye ta ke da doguwar rigar abaya baka, da ta sha adon duwatsuna. Ta boye idanunta cikin bakin gilashin RAY BAN.
Murmushi ne dauke a fuskarta ta yi ma su sallama.
"Ranki shi dade barka da isowa".
"Saifu ba dai za ka dai na kirana haka ba, hope ba wa ta matsala?".
"A'a babu, ga records ɗin jiya nan zan kawo ma ki office".
"Ok! Sannu da kokari".
Ofishin manager ta shiga su ka gaisa ta fito.
Wajen da aka tanaɗa dan ɗinki ta shiga nan ma'aikatan ta ke ta kawo gaisuwa. Ta bi ɗinkunan da aka yi tana dubawa.
"Gaskiya na yaba da kokarin ku, sai a kara bada himma".
Media department ta shiga,ofishi ne mai dauke da komfutoci guda hudu, printer da scanner.
"Aminatu sannu da kokari".
"yauwa Madam! Na gama tura pictures ɗin jiya".
"Mukhtar mi ake ci game da hotunan da Aminatu ta tura kafafen social media".
"an sami cigaba sosai Ranki shi dade, dan akwai wadanda ke son bada order ma duk na ba su reply din da ya dace, in sun zo za su ga manager".
"Yauwa to a cigaba da kokartawa ana kyakkyawan mu'amala da su dan samun karin customers".
"In Allah ya yarda".
Ofishinta ta wuce, fridge da ke gefe ta bude ta fiddo da ruwa a gora ta tuttula ta sha,sannan ta samu wajen zama.
Ba tayi minti biyar ba wa ta matashiyar ma ce ta shigo ba za ta wuce shekara ashirin da daya ba.
"Miss Zee morning".
"Morning Miss Cashier,akwai labari ne?".
"Miss Hafsat dai Madam,gaskiya jiya an samu income fiye da kullum ga bayanin kudin da aka samu na lissafa ".
" good! Haka ake so, in zan fita lunch na tafi da su bank".
"Ok Ma!".
"Nagode Hafsat ba tare da ku ba ba za a samu irin wannan cigaban ba".
"Mune da godiya da ki ka ba mu amana ki ka kuma daura mu hanyar cin abincinmu. Idan ba dan haka da yanzu ina gida zaune banda aikin yi certificate ɗina ya zama na banza".
"ba komi haka Allah ya so, idan kin fita Please ki kira mun Saifu".
Tun da ta zauna ta ke samun mutane ma su shige da fice, ba ta samu kanta ba sai karfe daya da minti goma (01:10pm).
Wayarta ta dauko da ke a silent ta duba taga missed call. A fili ta furta "I Miss him so much".
Wayar ta kara a kunne ta ce "Bibi nah ina aiki ina tunanin ka, wayar na a silent mode. Gaskiya kuna kokari bare ku da ke Lagos garin cinkoso yanzu na kara jinjina kwazonka".
"Ok this week kenan za ka shigo Gusau tunda za ka je Sokoto? Alright will talk later. Love you hun".
Bandakin da ke office ɗin ta shiga ta yi alwala ta fito ta tada sallah, sai da ta gabatar da nafila raka'a hudu (wadanda su ka zo a matsayin sunanu arrawatib) sannan ta yi sallar azuhur, bayan ta sallame ta sake guda biyu.
Fita ta yi tana sake duba ma'aikatanta.
"Yusuf bude mota ka dauko man leda a seat ɗin baya".
"Lokacin sallah da cin abinci ya yi na ga ba wanda ya motsa".
"Hajiya yanzu za mu tashi".
"ba ni son kuna wasa da sallah ne, idan lokacin sallah ya yi sai a ajiye komi aje ayi".
Yana kawo ma ta ledar ta koma office ɗinta.
Doughnut ne ta fiddo da ya ji chocolate crepes da coconut a sama. Fridge ta bude ta ciro pineapple drink ta zauna ta na sha tana haɗawa da doughnut.
Rufe office ɗin ta yi, ta shiga media Department. Gaban wata computer ta zauna ta bude ta, bayan ta gama booting ta shiga COREL DRAW in da ta natsu ta maida hankalinta akan abinda take yi.
Ko motsi ba ta son yi, ta fi awa guda tana aiki da na'ura mai kwakwalwa kafin daga bisani ta tashi ta jona komfutar da printer.
Takardu ne ta yi printing ma su dauke da zanen doguwar rigar wedding gown Har guda biyar.
"Mukhtar dauko flash ka tura design ɗin nan sai kayi uploading a instagram, twitter, Facebook da sauransu".
"Ok Ma".
"Aminatu duba man ki ga sun yi kyau".
"Wow Ma! Sun matukar yin kyau duk shige-shige na ban taɓa ganin irinsu ba".
"Yauwa! Dama I promise her something unique, diyar yayar Dr. Yabi za'a ma wedding gown na dinner bikinta".
"Eh gaskiya dole ayi ma ta dinki na kece raini".
**********
"Wash! Momi na gaji".
"Allah sarki sannu Auta Allah ya sa nema rabo ne".
"Amin Momina".
"dazu magabatan Samir sun zo, an kawo kayan na gani ina so,da na sa rana".
"Amma Samir be faɗi man ba".
"anjima Daddyn ku zai kira ki ya ma ki bayani".
"toh Momi bari in je in yi watsa ruwa Momi".Ku dakace ni!
A'ee Sholynku ce mai kaunar ku.chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu
Waiting for your comments, likes and suggestions about Zainab's lifestyle.
Miye na ku burin a rayuwa? Mi yafi burge ku a rayuwa Zainab.
Instagram @ayeesh_chuchu
Twitter @ayeesh_chuchu
Facebook Ayeesh Chuchu
Ina jiran sakonninkuLove you wujiga-wujiga lodi-lodi... Lmao
YOU ARE READING
DOGARO DA KAI
RandomIt's a Hausa story, based on self confidence, love, business, Hausa culture and lot more. Zainab yarinya ce da ta Dogara da kan ta, ta dalilin sana'ar da take takama da ita. Hakan yasa 'yan uwanta matasa su ke koyi da ita wajen ganin sun dogara da k...