DOGARO DA KAI
©Ayeesh Chuchu
August,2016
"I know they say believe in love is a dream that can't be real".
Justin Bieber
I dedicated this chapter to The story character Zee (aunty Sis), Ameenah Meeinerh and my able ladies BEAUTY RUSH (Marwah, Deejah Shariff, Aisha Sheik, Zully Baby, Fatima Baba Isah, Hajja). Thanks for always been there for me. Love you loads 😘.
{18}
"Zee lafiya?,please tell me what happened? Mi Samir ya ma ki?".
"ki kyale ni in ji da abinda ya ke damuna".
Kwanciya ta yi ta cigaba da kuka. Yasmeen ta zuba ma sarautar Allah ido. Sai da ta yi mai isarta sannan ta tashi ta yi wanka ta yi sallah.
SAMIR
Tun da ta tafi ta bar shi, ya dafe kan shi da hannu biyu.
"why all this? Na ɓata ma Zainab rai macen da na fi son a rayuwa ta".
"kar Zainab ta yi tunanin wani abu ni ke nufi".
Haka ya yi ta surutun shi ya tashi ya tafi.
PANAROMA MALL ya wuce shopping,cards ya siya manya ma su kyau guda hudu ma su dauke tsantsar kalaman soyayya, da katuwar rose flower mai dadin kamshi, hade da set ɗin TORY BURCH ULTIMATE mai dadin kamshi.
Bangaren chocolates da sweets ya je ya jido duk abinda ya ga ya ma shi. Ya kashe kudi aka zuba ma shi a shopping bag.
Bakin gate ɗin makarantar su Zee ya tsaya ya kira wayarta ta ki dauka.
Ya rasa inda zai tsoma ran sa, tunowa da ya yi ta kira shi da lambar Yasmeen yasa ya yi saurin dubawa ya ci sa'a ya gan ta.
"Assalamu Alaiki".
"please ki fito bakin gate ɗin ku ina kan hanya ne da taxi, Samir ɗin Zainab ne".
Tsawon mintuna sha biyar (15mins)ta iso, sun gaisa.
"Samir mi ka yi ma Zee sai kuka take?".
"Yasmin ba wani abu bane Zee ce ba ta fahimce ni ba".
Nan ya ba ta labarin abinda ya faru.
Dariya ta yi ta ce "kai ma ai be kamata ka yi ma ta tsawa ba, da ka fahimtar da ita".
"gani nayi daga na ce ta raka ni wani waje, shopping za mu daga nan in rako ta school".
"ba komi zan fahimtar da ita, kai ma ka kiyaye ba'a mace tsawa fa".
Dariya su ka yi, sannan ta amshi kayan da kyar ta ke tafiya saboda nauyin kayan.
Zaune ta iske Zee saman daddumar sallah, ta gama sallar isha'i.
"Yasmin daga ina ki ke ne?".
"Ban sani ba ".
" Ashe kin iya bakar magana ban sani ba".
"kadan kenan, na je mun gaisa da Samir ne".
"Samir???".
"Yes! Samir ɗin ki".
Ji ta yi wani irin tukuki na ta so ma ta, kamar ta kurma ihu.
Yasmin na kula da halin da ta shiga tayi banza da ita.
"mi ki ka je yi wajen Samir?".
"miye haɗin ki da shi da ki ke tambaya?".
"saboda mi ba zan tambaya ba, bayan kin san yanda nike son Samir".
"Yes! Har yanzu ban yi proving son da ki ke ma shi ba".
"ta ya za ki yi bayan ni kadai na san What am going through, Samir is my life".
"stop all this kind of fairy-tale, ba ki son Samir tunda you can't understand his words and actions".
"Ba haka bane, Samir ni ya ma tsawa dan ina faɗin ra'ayi na".
"Ya dau laifin shi na tsawar da ya ma ki, amma kuma kema abinda ki kai ba ki kyauta ba, kin zarge shi akan abinda ba ki tabbatar ba. Ya rantse man da Allah shopping za ku daga restaurant ɗin da ku ka fito ".
" Amma ai sai ya faɗa mun ba wai ya ce wani waje ba".
"so yake ya yi surprising ɗin ki ".
" hmm ba ki san mazan mu bane Yasmeen they're capable of doing anything".
"Duk da haka for the first time you would have given him a chance to prove himself, not all men's are the same".
"Amma ai wannan babban mistake ne sai in bi shi wajen da ban sa ni ba, da dai ya fada ne ".
" shikenan dai kiyi hakuri, ya zo ku yi sallama kin ki picking calls ɗin shi, ga sako nan in ji shi".
*****************
"Yeeeeee Yasmeen fito ki ga rigar da na ɗinka son ta ake sosai".
Yasmeen da ta fito daga bayi tana goge kai ta ce "MashaAllah! Zee kin zama professional fashion designer kawai".
"Ke kam dai an yi azuraka, nagode da zagi na da kike yi".
"ba wani zagi, ni ban ji kina maganar plan ɗin ki ba idan kin koma Nigeria".
"har yanzu tunanin yanda abubuwan za su kasance ni ke, kin ga mu akwai bambancin al'ada yanzu mutane zasu fara magana a kaina dan dai na yi DOGARO DA KAI ".
" mtsww in dai za ki biye maganar mutane ba za ki taɓa yin komi a rayuwa ba ".
" ba za ki gane ba, mu surutun mutane kadai ya isheka sannan ba mu yi maganar wani abu dangane da fashion design ba da Samir".
"ni na san ba ki da matsala da Samir he is a socialized person, kuma ma abu da ke a field ɗin shi ".
"akwai bambanci tsakanin mace da namiji, shi zai iya zuwa ko'ina ne a duniyar nan, ni fa?".
"kina ban mamaki Zee. Just have self confidence on yourself, believe in yourself,and stand for yourself".
"Duk ki ajiye wannan ina son as soon as na Koma gida, a ce na bude shagon da zan dau kwararrun teloli da za su iya duk wani irin dinki da na nuna ma su, kuma nima tunda na iya ɗinki banda matsala, amma babbar matsalar ita ce capital!".
"Tunda har iyayen ki su ka amince da karatun nan, za su taimaka ma ki, ko ba'a taimaka ma ki ba start with the little you've, a hankali fa komi ke samuwa".
"Hakane gaskiya, na ji dadin firar nan. Kin sa na manta ban kira Mon Cheri ba, na ga missed call ɗin shi".
"it's not too late ai, Mrs. Samir".
"wato har na zama Mrs. Samir?".
"Yes! Kadan ya rage kawai, ni dai wannan rose flower ɗin ni ke idan mun gama tunda dai ni na amso kyautar lokacin da ake fushi da Samir". "kin san kuwa kullum sai na karanta cards ɗin nan, komi na Samir daban ne Yasmeen. Ya san yanda zai tafiyar da mace, he is cool and gentle".
"Soyayya kenan! Kuna birge ni Zee".
***************
Kwance ya ke akan kushin three seater dake gefen a tamtsetsen gidan da ya gina a cikin garin Gusau. Ya zura ma Katon hotonta da aka zana kamar ita ido. So da kaunarta na fizgar shi.
A hankali ya furta "I love you so much Zainab!".
Wayar shi da ke kan center table ya kai hannu ya dauka, ya tura ma ta sako kamar haka :
"I really missed your cute smile, your pulchritude face, in fact everything about you. You're unique in your own style. My love for you will forever shine with happiness my honey bunch".
Ta maido ma shi da reply kamar haka:
"No matter the distance between Us. I am as close to U today as I was yesterday.. For as long as U are in my heart we are never truly far apart. I love you with all my heart ".
Sun dade su na musayar kalmomi ma su dadi tare da bayyana asirin zuciyar junan su.
Bacci ɓarawo ya sace su.
*************
A kwana a tashi sauran wata ɗaya su Zainab su kammala karatunsu.
Kaya ne baje a saman gadonsu ita da Yasmeen.
"Zee gaskiya yau na gaji sai ka ce kasuwar za mu siye gaba daya".
"ni fa in dai batun shiga shaguna ne ba ni gajiya yanzu kinga gobe ko jibi mu tura kayan mu ba ni son time ɗin da za mu tafi in kwashi wasu kaya".
"Wai Zee kayan da na ga ki na ta dauka na maza wa ki ka siya ma wa?".
"hoo Yasmeen gulma ba kyau, yayana na yi ma tsaraba".
"ban yadda ba wallahi gara ma ki faɗi gaskiya".
"toh ba zan faɗi gaskiyar ba".
*****************
Tsaye su ke sanye da doguwar riga ta material mai adon flowers a jiki. Dinkin yabi jikinsu kamar dan su aka yi shi. Sun sha daurin turban headwrap, fuskar nan ta sha Makeup.
"MashaAllah! Autar Momi ke ce kuwa?".
"Yaya Habib mi ka gani?".
"naga kin kara kyau da haske, anya ba bilicin (bleaching) ki ka koma yi ba? ".
" Abban Sultan ba ka da dama, Makeup ne kawai yasa ta wannan hasken".
"Wai miya sa su Momi ba su zo ba?".
"Mu kenan ba ki yi murnar ganin mu ba?".
"A'a na so a ce dai Momi da Daddy na kusa su ga Auta a stage ta na karbar gifts".
Sai bayan maghriba taron yaye su Zainab ya watse, Yaya Habib da Aunty J hotel suka wuce. Zee ta ja hannun Yasmeen suka tafi hostel ɗin su.
"Yasmeen kin ga Samir ya karya alkawarin shi da yace zai zo,na kira wayarshi ta ki shiga, jibi ko mun koma gida ba ruwana dashi".
"ki ma shi uzuri mana kila akwai dalilin da ya hana shi zuwa".
"Amma duk da haka ai da ya kira ni ya faɗa mun ba zan damu ba".
"duk da haka dai".
Suna zuwa hostel wanka Zainab ta yi tare da alwala ta rama sallar maghriba da ta wuce ta, sannan ta yi isha'i.
Ta kwanta tana ta neman lambar Samir shiru ba ta shiga.
Washegari da safe misalin karfe goma (10:00am),Zainab tsaye ta na gyara daurin dankwalinta da ta nada shi wani irin crazy style.
Sanye take da doguwar rigar material turquoise color da combination na fari (white) mai high neck da dogon hannu da ya matse daga tsintsiyar hannunta.
Rigar ta bude daga kasa. Ta yi kyau sosai cikin dinkin.
RETAJ DABAB HOTEL ta isa, hotel ɗin da su yaya Habib su ka sauka.
"Inyee! Auta wannan rigar ta mun kyau ina ki ka siya?".
"kai aunty J kin manta da fashion designer ki ke tare ne? Ni na dinka rigata da kaina".
"Lallai Auta abin yar wariya ce sai kiyi ta dinka ma kan ki kaya banda mu".
"ku jira kuga idan ban dinka ma ku ba. Ni ba wannan ba, mun yi da Samir zai zo jiya kin ga throughout jiya wayar shi kashe har yanzu".
"Ummm ashe dai ana son Samir ɗin nan haka?".
"faɗi ma ɓata baki, ai ba namijin da za'a gani a ce ba'a so bane".
Dariya ta yi tace "Eh gaskiya ne, da an koma asa rana kawai tunda na ji Abban Sultan yace ya je har gida gun Daddy neman izini".
"Au ashe har gun Daddy ya je be taɓa faɗa mun ba".
Wayarta ce ta yi kara ta na neman agaji.
"Yasmeen lafiya kuwa? Ok ba ni address ɗin wajen gani nan zuwa".
" Aunty J, bari in je in dawo, Yasmeen ke nema na".
Double double sorry please. In Shaa Allah gobe za ku ji, ku gafarce ni. Thanks for your support, love and care.
ILYSM
Indo Aisharku ce
Please don't forget to drop your comments on chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu
YOU ARE READING
DOGARO DA KAI
RandomIt's a Hausa story, based on self confidence, love, business, Hausa culture and lot more. Zainab yarinya ce da ta Dogara da kan ta, ta dalilin sana'ar da take takama da ita. Hakan yasa 'yan uwanta matasa su ke koyi da ita wajen ganin sun dogara da k...
