DOGARO DA KAI
©Ayeesh Chuchu
August,2016{8}
Murmushi ta sakar ma sa, ta furta "Thanks", cikin softly spoken voice ɗinta.
List ɗin da ke hannunta ya amsa, ya duba.
"Let me help you (Bari in taimake ki)".
Gyada kai ta yi, ba tare da ta ce uffan ba.
Ta waiwaya ba ta ga aunty J ba. Haka tayi ta bin shi, kamar ya ma ta baki ya dauki basket, yana zabar ma ta drawing pencils,black pens, water color pencils, markers da pencil sharpener & erasers.
Can ta hango aunty J tana daukar sweet da chocolate. Wajen da za su biya su ka wuce, nan ta iske wannan mutumin ta yi saurin mika ATM card ɗinta, ya duba kudin chocolates da su ka siya ya ciri kudin, sai tayi nuni da sketching tools ɗinta da ke a basket.
Ya duba su, sannan ya ciri kuɗinsu. Ta waiwaya ba ta ga mutumin ba. Ta amshi kayanta su ka fito. Nan ma ta duba babu alamarshi.
Aunty J na driving ta ce "wai waye na ganku tare?".
"yanda kika ganshi nima haka, ya dai taimaka mun ya zabar man duk abubuwan da ni ke bukata, na duba ma in ma shi godiya ya bace bat kamar aljani".
"Kila shi ne Mr. Right ɗin na mu".
"A'a babu soyayya a plan ɗina yanzu, duka 17years fa gare ni".
"ai ko dai Momi nasan ganin Auta a gidan mijinta".
"tab kamata a ce a mun aure ai nayi yarinya ta da yawa, ina laifin 20years".
"Mu dai da miji ya fito aurar da ke za mu yi ba ruwanmu, dan na ci ma bikin ki buri sosai".
"Lallai aunty J har kin ma fi Momi zakewa".
Har gida aunty Jamila ta kai Zainab, sannan ta wuce, ta shiga cikin gida.
**************
Yanda ta shigo gidan da gudu, fuskarta yalwace da farin ciki zai tabbatar da cewa akwai abinda ke ma ta daɗi.
"Momi, Yaya Labeeba, Sis Beeba I've got it all".
Da gudu Labeeba ta fito ta kwace takardar da ke hannun Zainab, rungume ta tayi "Congrats my lovely sister, Autarmu sai jami'a".
A falo ta iske Momi zaune da littafin HARVEST OF SHAME by Julie Odimma tana karantawa. Gefen Momi ta zauna, fararen hakoranta a buɗe.
"Momi ga sakamakona".
Ganin yanayin Zainab yasa Momi ta faɗaɗa fara'arta. Tana gama dubawa ta rungume Zainab.
"Hakika kin fitar da ni kunya samun 9 credits da kika yi, Allah yai ma rayuwarki albarka".
Habiba da ta shigo ta ce "Tare da mu Momi".
Nan su ka zauna su na ta taya Zainab murna. Nan ta kira Jidda ta faɗa ma ta da yake ta je Katsina hutu, gidan kawunta.
Da dare Daddy ya dawo, dama shi kawai ta ke jira. Sai da ta bari duk kowa ya je gaida shi, sun dawo sai Hajiya da ke da girki aka bari.
Result ɗinta ta dauka ta yi part ɗin Daddy. Zaune ta iske shi, Hajiya na zuba ma shi dafadukan couscous da ya ji kayan lambu.
Ta yi ma shi sannu da zuwa, ya amsa ba tare da ya kalleta ba. Ta ji zuciyarta na suya, ba ta son irin halayen mahaifinsu dan dai ba ta da yanda za ta yi, kullum sai ta yi ma shi addu'a, sam babu shakuwa a tsakaninsu.
Sanin halinshi idan zai ci abinci ba ya magana har sai ya gama, ya sa ta sami waje ta zauna.
Sabuwar tashar turanci ta Unity TV dake Abuja ce ke haskawa a allon talebijin ɗin,idanunta su ka sauka akan fuskar mutumin da ta yi nema har ta gaji ba dan komi ba sai dan ta goɗe ma shi.
Shirin YOUTH OF TODAY suke, wanda Meenah Musa ke gabatarwa cikin tsararren turancinta kamar wata buturiyar England.
Gaba ɗaya ta tattara hankalinta akan mutumin da ta gani, magana ya ke cikin silvery voice ɗin shi da ya yi bala'in tafiya da ita, ba dan ta ji ya taɓa yin yaren Hausa ba, da sai ta rantse da Allah ba bahaushe ba ne.
Sanye ya ke da bakaken suit kirar J. CREW. Hutun rabin lokaci aka tafi, bayan sun dawo ne Meenah Musa ta ce "Ina fatan ma su kallonmu ba su manta da Samir Ahmad Alkali ba, shugaban SAA Fashion Design da ke a Lagos".
Murmushi ya yi tare daga hannun shi sama, alamar gaisuwa ga ma su kallo.
" Zainab!".
Ta juyo a firgice "Na'am Daddy".
"Ya aka yi ne?". Ya faɗa fuskarshi a daure.
"Ga shi Daddy result ɗina ne na wannan shekarar da na canza".
Ya amsa tare da bin kowanne harafi dan tantance abinda ke jikin takardar.
"Yaushe ki ka yi jarrabawa ban sani ba?".
"tun kwanaki ne, Yaya Habib ya biya man".
"Madalla! Ya yi kokari ai, kin yi JAMB kuwa?".
"Eh duk na yi, admission kadai ni ke jira anan FUG".
"Ba laifi kin yi kokari, sai ki kara dagewa idan kin shiga jami'a, wane Course ki ka cike?".
"BSc Chemistry ne".
"Ok, komi kenan za ki ji duk wani bayani daga bakin Mominku ko Habib".
" Nagode Daddy, Allah shi karo budi na alkhairi ".
" Amin".
Ta tashi tare da kai duba ga TV da ke kunna, ta ga har sun gama shirin.
Ta na tafe tana nanata sunan Samir Ahmad Alkali a ranta.
Dakinta ta wuce ta faɗa bandaki, tayi wanka tare da alwalar bacci,kayan bacci ta sa ma su kauri riga da wando duba da yanayin sanyi da ake ciki. Fashion design sketching box ɗinta ta dauko, study table ɗinta ta hau, tare da zazzage kayan da ke cikin akwatin, ta kare ma su kallo tare da furta "komi na shi mai kyau ne, ya iya zabar abu unique".
Fashion sketch book ɗinta ta fiddo, mai pink cover, ta bude shi ta na kallon shafi-shafi na Design ɗin da ta yi,dangin su Abaya na middle east (kasashen larabawa), ankara style da kuma design na English wears da suka dace da addininmu da al'ada.
Wani irin farin ciki ta ke ji, wanda ba ta taɓa tsintar kanta a ciki ba.
Ta waiwaya ɗakin ba wanda zai taya ta murna. Wayarta da ke caji ta dauko.
"Jidda ki hau WhatsApp in tura ma ki wani abu".
Duk shafin da ta bude sai ta ce dauka, har ta gama ta kunna data ɗinta. Ta iske Jidda na online ta tura ma ta.
Bayan sun bude Jidda ta turo ma ta da sako, "MashaAllah! Am proud of you My Zee, In Shaa Allah sai kin zama shahararriya kamar yadda Donna Koran mai kamfanin Donne Koren New York (DKNY) da kuma Coco Chanel me Chanel brand".
"hahaha, kin ban dariya ma, wacece Zainab Ismail Gumi da har zan kai wadannan fitattun matan da su ka goge a harkar Fashion design".
"Ke ma mutum ce kamar su, har kin fi su ma tunda ke musulma ce, kuma na san kina kishin addininki ba za ki yi abinda zai saba ma shari'a ba, I trust you Zee".
"Hmmm ke dai ke hangen hakan, amma ni ina yi kawai dan jin dadi na, ba ni tunanin ta ka wani matsayi a dalilin Fashion design, ba zan iya gasa da su ba".
"matsalar mutanenmu kenan, suna da talent na kirkiro abubuwa amma tsoro da rashin son DOGARO DA KAI yasa sam ba mu samun cigaba".
"akwai rashin kayan aiki fa".
"duk da haka da kadan-kadan sai ki ga mutum ya zama abu a rayuwa".
"hakane Jidda, you're such a darling".
YouTube ta shiga, ta binciko Unity TV, tabi duk programs daki-daki har ta zo kan wanda take so. Ta danna akan Youth of today episode 5,cikin yan sakwanni ya bude, kan gado ta kwanta ta lumshe idanunta, sannan ta bude su akan screen ɗin wayarta da Samir Ahmad Alkali ke bada takaitaccen tarihinshi.
Ta dau tsayin 45mins tana kallon tattaunawarsu, idan daga karshe ya bada contacts ɗinshi na zaurikan sada zumunta (social media).
Biro da littafi ta dauko akan bedside drawer ɗinta, ta rubuce su tsab.
Ba ta damu irinsu Facebook, Twitter, Instagram, Skype da sauransu ba,WhatsApp kadai take yi shi ma saboda kawayenta.
************
Zainab da Jidda sun fara zuwa makaranta, tare su ke tafiya da Jidda dasu Labeeba. Kullum Danliti zai kai su ya dawo gida da su.
Habeeba na ta samun alkhairi a sana'arta dan ba ta tsawwala kuɗi da yawa, shiyasa ta ke ciniki.
Yau ma kamar kullum sun dawo daga makaranta da yamma, Zainab na zaune a falo ita da Momi, suna kallon tashar Sunna TV suna shirin Domin Iyali, wayar Zainab ta yi kara, ganin sunan aunty Jamila yasa tayi saurin dauka, bayan sun gama magana ne ta ce "Momi kin ji aunty Jamila wai kwangila ta kawo man".
"kwangilar mi Auta?".
"fried rice ce zan yi da pepper chicken na mutum ɗari, makwabciyarta ce za ta yi walimar dawowar ɗiyarta daga UK, shi ne su ke neman in da za su bada ayi masu abincin mutum dari, sai ta faɗa ma su akwai yar uwarta da ke yi".
"yanda ki ka gani Auta, in dai za ki iya ki kwatanta ki yi ai akwai isassun kuɗi a account ɗin ki".
"Eh Momi akwai, zan gwada in gani".
"Allah shi bada sa'a".Tun ana sauran kwana biyu walimar Zainab ta tanadi duk wani abu da take bukata ta siyo, wadanda zasu lalace ta sa a freezer.
Ranar walima tun safe da ta shi ba ta koma bacci ba, da yake ranar Asabar ne.
Dama ta soya kaji, da taimakon Habeeba da Labeeba da su ka taya ta, ta kamalla komi, su ka zuba a farar roba ta takeaway hade da spoon da fork duk na roba.
Daki ta dawo ta zauna ta lissafa duk abinda ta kashe, hatta da kudin motar da za'a kai ma ta gidan sai da ta fidda, sannan ta daura ribarta a sama.
Karfe hudu na yamma za'a yi walimar, tun uku saura ta shirya cikin abaya baka mai faɗi kirar FANCY EMBROIDERED da ta ji ado da duwatsu farare a faffaɗen hannun rigar, wuya da kasan rigar.
Gyale ja ta dauko shi ma da duwatsu a jiki, ta saka dankunne silver da agogonta na hannu kirar NIXON ita ma silver, sai jan sandals mai tudu na MIU MUI.
Saboda yawan girar da take da ita yasa bata damu da zana girar ba, sai dai ta sa brush wand gyara girar. Wadannan SMOKEY EYES ɗin nata da basu bukatar eyeshadow ta zizara ma eye liner, sai su ka kara haske da girma. Ta shafa ma labbanta sirara maroon ɗin jan baki hade da Red lip liner. Fuskar nan sai walwali ta ke.
Ita kanta ta san ta yi kyau, selfie stick (handy camera) ta dauko ta jona da wayarta.
Ta kar kace sai daukar hotuna take, sai da tayi mai isarta sannan ta dau clutch ɗinta ja, ta fito daga ɗakin.
Momi ta fito daga kitchen hannunta dauke da gorar ruwa da glass cup.
"MashaAllah! Auta ke ce kuwa?".
"Haba Momi canzawa na yi ne?"
"Kin yi kyau sosai, ki kula da kan ki banda sakarci".
"In Shaa Allah Momi".
Dakin su Labeeba ta leka nan ma suna ta kuranta irin kyan da ta yi.
Ta na fitowa harabar gidan ta iske mai mota na jiranta, ta bashi kudin shi da address ɗin gidan. Ta wuce ta tari Napep ta kai ta gidan aunty J, su ka shiga gidan Arch. Sulaiman Ibrahim, gida ne na azo a gani daga gani naira ta koka.
Sun shiga part ɗin matar gidan,Zainab sai kalle-kalle ta ke, a falo ta iske matar gidan da ta sha ado cikin leshi mai tsada da gwala-gwalai sai walkiya ta ke.
Zainab ta gaida Hajiyar cikin girmamawa, haka ma aunty J.
"Maman Sultan ba dai wannan ce kanwar ta ki ba?".
"Eh ita ce Hajiya".
"na ganta karama kuma ita tayi wannan girkin da Hafeez ya dau daya sai santi yake, lallai Allah yai ma ki baiwa".
Murmushi Zainab ta yi tare da dukar da kai".
Wani sassayan kamshi ne ya baɗe falon.
"Mum please karin three takeaway su Mahmud ne su ka zo, I Know they'll enjoy the food".
"ka duba kitchen akwai abinci a food flask".
Sam be lura da su Zainab dake falon ba. "please Mum ba dan hali na ba".
Karaf idanuwansu su ka sarke da juna, murmushi Zainab ta yi.
"Hafeez ka ga wadda ta yi girkin nan fa".
"Wannan yar karamar yarinyar?".
Zainab ta wurga ma shi harara dan ta tsani a kirata da karamar yarinya.Nana Aa'ishatu loves you much..
Waiting for your comments.
chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu

DU LIEST GERADE
DOGARO DA KAI
SonstigesIt's a Hausa story, based on self confidence, love, business, Hausa culture and lot more. Zainab yarinya ce da ta Dogara da kan ta, ta dalilin sana'ar da take takama da ita. Hakan yasa 'yan uwanta matasa su ke koyi da ita wajen ganin sun dogara da k...