BABI NA SHA HUDU

1.6K 90 10
                                        

DOGAROda DA KAI
©Ayeesh Chuchu
August, 2016
{14}

Wani irin murmushi mai taushi ta saki, farincikin da take ciki ya kasa ɓoyuwa. Ta rasa wanda za ta shaida ma wa, tunowa da ta yi ai sirrin zuciyarta ne.
A hankali ta furta "Samir Alkali".
**************
"Auta shiru kin ki fidda gwani har yanzu".
"Aunty BA LAIFI NA BANE, am still young and I'm looking for my missing rib, Wanda zai so ni ya bani duk wa ta kulawa da ni ke bukata".
"Toh ya nuna mana kin ga dai na gaji da tarin da ni ke".
"Lallai aunty J ko Momi ba ta fara tari ba sai ke, yanda ki ka ci buri a bikina ni uwar gayyar ma ban ci ba".
"Ki bari kawai ganin ba ni da kanne ne ko a gida, shiyasa ki ka ga ina wannan ɗokin kema wata rana za ki ji abinda ni ke ji, ban so na zo a Auta ba".
"Ai ga shi Allah ya ba ki zuri'a damma naga kun tsaya yanga ke da Yaya. Ban yarda da ku ba Family planning ku ke yi idan ba haka ba shekara goma da aure 'ya' ya biyu".
"ki bari idan Abban Sultan din ya dawo sai ki tambaye shi da kan ki".
"ki rufan asiri dan Allah, in ba so ki ke yai ta mun bala'i ba".
"na ji an ce an saka ranar auren Jidda da Hafeez?".
"Ta yiwu da gaske ne mun kwana biyu ba mu hadu ba, tunda su ka dan samu hatsaniya na shirya su".
"Zainab lallai zuciyarki na da karfin imani, har wani shirya su ki ke".
"Eh ba ni son Jidda ta rasa Hafeez, matsalata ɗaya da Jidda har yanzu ta kasa fahimtar halayenshi".
"Sai ki kyale ta idan sun yi aure za su fahimta".
*************
"Momi! Momi!! Momi!!!".
"Kai Auta wannan kira haka".
"Momi mmm.. Mmmm".
"faɗi man mana kin tsaya kina inda-inda".
"wannan gasar ta NABA da na shiga na zo a ta biyu".
"Alhamdulillah! Lallai kam wannan shi ne RABONKA KO YANA A BAKIN KURA".
"Sun ban scholarship na RAFFLES DESIGN INSTITUTE da ke a Riyadh, Saudi Arabia hade da admission letter ta, da takardar da ke nuna sheda na ci gasar zan je a fiddo man su idan sun kammala duk wasu shirye-shiryen su za su tuntuɓe mu da sako mai dauke da ranar da za mu je Milan ɗin daga nan duk wani shirin tafiya makaranta sun gama daga wajen kararrawar za'a wuce damu ".
" Nayi murna Zainab, mu je Alhaji ya ji wannan batu shi da Hajiya".
A farfajiyar gidan su ka iske shi, zaune kasan bishiyar umbrella da ke dauke da kujerun zama yana karantar jaridar AMINIYA.
"Lafiya kuwa? Wannan farin cikin da ke kwance a saman fuskokinku ban taɓa ganinku da irin shi ba".
"Auta je ki kira Hajiya".
"Momin yara ba ki bani amsata ba".
"Dadin yara bari Hajiya ta iso ka ji".
Zuwan Hajiya yasa Momi ta ba su labarin abinda ya faru tiryan-tiryan har ta kammala.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Mamana Ubangiji Allah shi albarkaci rayuwarki, a yau na kara jadadda ke din YAR BAIWA ce, ba zan hana ki fita kasar waje ba, amma da sharaɗi ki rike mutuncinki da martabar iyayenki. Ki ji tsoron Allah a duk in da ki ke, kada ki ga kin je kasar da ba iyayenki ba 'yan uwanki ki yi abinda ki ka ga dama, to ki sa ni Allah na ganinki, kiyi abinda ya kai ki banda shirme".
"In Shaa Allah Daddy".
"ki mun alkawarin da kin dawo za ki fiddo da mijin aure, akalla kin kusa shiga shekara ashirin da uku idan ban manta ba".
"na yi ma ka alkawari Daddy ku cigaba da tayani da addu'a ".
Sun dade suna fira, kafin daga bisani ta koma ɗaki tabar su Momi can. Farincikin da ta ke ciki baya misaltuwa, idan ta tuno hirar da tayi da mahaifinta sai ta ji wani irin sanyi na ratsa ta.
Wayarta ta dauka ta yi ta kiraye-kiraye, duk wanda ya kamata ta faɗa ma wa, sai da ta faɗa.
Washegari sai ga su Labeeba, Habeeba da Aunty J. Gida ya cika da jikoki.
Sai kiriniya Huda (diyar Labeeba) da Amrah (diyar Habeeba) suke da yake sa'annin juna ne.
Sultan dan Shekara tara shi ala dole babba, ya hakimce yana kallo. Amatullah kuwa duk in da Zainab ta sa kafa sai ta bi ta. Jininsu ya haɗu, Zainab na san yarinyar saboda sunan Momi aka sa ma ta.
Zaune suke a ɗakin Zainab hira ta kaure.
"Auta fa za'a hau jirgi duk kurinta ba ta taɓa hawa jirgi ba". Cewa aunty J.
"Maman Sultan ai har mamaki ni ke, ko Abuja zuwanta ɗaya fa, duk kurinta iyakarta Gusau".
"Ka ji yaya Labeeba ina jin ke ma dai auren da ki ka yi yasa kika fara keta hazo".
"Kyale su Auta ai yanzu dai ga dalili ya zo, fita kasar waje har sai kin ce baki so wata rana".
"kai kada Allah ya kawo ranar Sis Beeba".

***********
Duk wani shiri da ya kamata Zainab ta yi, ta yi shi. Yau su ke shirin tashi da misalin karfe uku na rana (3pm),a Abuja su ka kwana ita da Momi, Yaya Habib da Aunty J.
Zainab da bakinta ya kasa rufuwa, ta kagara su bar Nigeria.
Hankalinta be kwanta ba, sai da ta ga sun isa babban filin jirgin sama na Milan.
A hankali su ke sakkowa daga matattakalar jirgin ta na kallon mutanen da ke ta shawagi a sararin filin, da yawansu matafiya ne.
Taxi su ka hau ta kai su adireshin NABA dake a Darwin, 20
20143 Milan. Direban taxi ɗin ya kai su har wajen. Basu sha wa ta wahala ba, bayan Zainab ta nuna ma su duk abinda su ke bukata. Aka kai su masaukin da aka tanadar ma su.
Washegari aka fara taro a cikin babban ɗakin taro na NABA, wajen damkam yake da fararen fata.
Anan ne aka kira wadanda su ka lashe gasar daga sashen Kasar Asia,America, Middle East (yankin labarawa), har dai aka gangaro kan Africa. Inda aka faɗi sunan Suzana Samuel yar kasar Ghana da ta zo ta daya, aka ba ta award ɗinta.
Zainab Isma'il Gumi (Zamfara,Nigeria) ta fito sanye cikin bakar abaya ta yane kanta da shuɗin mayafi. Ita ma aka ba ta award ɗin ta, su Momi su ka fito suka dauki hotuna.
Abdul Hameed Ibrahim (Katsina, Nigeria) ya fito.
An yi shagulgula sosai a ranar. Kafin su koma masaukinsu.
Washegari su Momi su ka koma, in da suka kara ja ma Zainab kunne. Tayi kuka kamar ranta zai fita.
Satin su ɗaya a Milan ana masu shirye-shiryen tafiya Riyadh. Kadaici ya addabi Zainab, ba ta da abokin magana sai dai tayi chatting.

RIYADH
Sun sauka a filin jirgin saman KING KHALID INTERNATIONAL AIRPORT (KKIA). Tare suke da wakilin su. Taxi su ka shiga.
"MashaAllah". Zainab ta furta ganin fitulu tangararan kamar da rana.
Ba su tsaya ko ina ba sai gaban tangamemen BOUDL ALMALAZ HOTEL da ke a Ahsa street, a cikin birnin Riyadh.
An yi ma su booking ɗin dakuna, inda kowannen su ya shiga inda aka tanadar ma shi.
Wanka Zainab ta fara, sannan ta biya bashin sallolin da ake bin ta. Ta na zaune ta ji an kwankwasa kofa, ta je ta bude.
Murmushi ta yi ganin shi bakin kofar.
"Abdul ya aka yi ne?".
"da ma dubawa zan yi inga ko kin shirya ki raka ni wajen Mr. Charles".
"da kyar idan shi ma be yi bacci ba saboda gajiya kasan ya cika raki".
Murmushi ya yi "Ok toh sai da safe".
Ta ɗaga ma shi hannu tare da rufe kofar.
Tun da su ka haɗu a Milan su ke mutunci da Abdul Hameed, kusan tsararrakin juna su ke, dan Funtua a cikin jihar Katsina.

Washegari bayan sun shirya sun fito, nan ma taxi duk suka hau taxi zuwa unguwar AL ORUBA, daura da titin Prince Turki Ibn Abdl Azeez Al Auwal.
Sun tsaya gaban makarantar RAFFLES DESIGN INSTITUTE da aka rubuta da manyan haruffan turanci da kuma larabci.
A hankali suka fito suna kare ma ginin kallo.

Ku dakace ni zuwa anjima.
Ga breakfast nan.
chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu

Nana Aa'ishah love you wijiga-wijiga

DOGARO DA KAI Where stories live. Discover now