BABI NA BAKWAI

1.7K 116 6
                                    

DOGARO DA KAI
   ©Ayeesh Chuchu
August,2016

      {7}
  "Zee lafiya? In ga print out ɗin".
Jiki a sanyaye Zainab ta mika ma Jidda print out ɗin result ɗinta. Hankalinsu a tashe su ka fito daga cafe ɗin.
  Keke napep su ka tsaida ya kai su Samaru, bakin titi ya ajiye su be shiga da su cikin unguwa ba.
   Jidda ta fara shiga gida, sannan Zainab ta wuce. Zuciyarta na ta harbawa a da karfi, sakamakon fargabar da ta ke ciki na irin hukuncin da Momi, Yaya Habib da Daddy za su yanke ma ta.
Tunda ta shigo gidan take kuka, zuciyar ta na tukuki. Hango motar Daddy a parking shade ya kara daga ma ta hankali.
A hankali ta ke tafiya har ta isa sashen Daddy, da sallamarta ya amsa. Ba ta yi tsammanin ganin Momi ba, ta durkusa har kasa ta gaida shi.
"Auta lafiya kuwa na gan ki sukuku kamar baki da lakka a jiki?".
"Momi, Daddy dan Allah ku yi hakuri ku gafarce ni, wallahi na yi karatu sosai tun kafin mu fara jarrabawa har mu ka gama..."
Daddy ya katse ta "mu ga takardar ban san dogon zance". Ta mika ma shi, tare da dukar da kanta.
  "Zainab yanzu duk kudin da na kashe ma ki na makaranta ya tashi a banza kenan, ki rasa subject ɗin da za ki faɗi sai Math da English, ba ni ki kai ma asara ba illa kan ki, ina ganin kin fi  Labeeba hankali da natsuwa ashe gara ita. Toh ki sani kwandalata ba za ta kara ciwo a kan karatunki ba, ni ba asararre ba ne, ni ma nan da ki ka gan ni, ba wanda ya taimaka mun da kwandalar shi a harkar karatu na, ni nayi duk wani faɗi tashi har na kai matsayin da nike yanzu, dan haka kuma ba zan bari ku lalace saboda kuɗi ba. Duk ranar da ki ka yi hankali ki ka gyara jarabawar ki,sannan kwandalata za ta cigaba da aiki akan ki".
"Daddy dan Allah ka yi hakuri, wallahi ba laifi na bane, ko Jidda ma ba ta samu ba".
  Momi da tayi zuru, zuciyarta na kuna akan maganganun Daddy ta ce "tashi ki tafi Auta".
Ganin ta kasa tantance yanayin da Momi ke ciki yasa ta fita daga falon.
Momi ta kalli Daddy ta ce "Haba Alhaji maganar da ka faɗa na tsame hannunka daga hidimar karatun Auta sam be kamata ba, ai hannunka baya ruɓewa ka yar".
"Dakata! Dakata!! Na riga na gama magana dan haka ban son maimaici, hakan da nayi shi ne horon da na zaɓa ma ta bani son ana saka mun baki a harkokin ya'yana".
     "Amma dai kasan rabi da kwata na karatun Zainab ni da Habibu ne jigo dan abinda ka ke badawa ba isarta yake ba,Haba Alhaji ka tuna fa idan dai kan jarabawar Auta ne be kamata ka yi haka ba, kaddara ce ba inda ba ta fadawa kuma yarinyar nan na iya bakin kokarinta".
"maganar kudin makaranta iya yanda na ga zan iya shi na yi ba ni kure kaina".
  "Shikenan ai Alhaji, amma dai yau tini zan ma ka akan abinda ya zama hakkinmu akan ka da ka manta da yin shi shekaru da dama da suka wuce, har zuwa yau ba ta canza zani ba".
"Ki faɗi duk wani son ranki Fatima".
"Ba son rai na faɗa ba, illa gaskiya idan na ɓata ma ka ka yi hakuri ka gafarce ni".
  Ta sa kai ta fita. Falo ta iske Zainab kwance akan three seater tana ta rizgar kuka, kamar an aiko ma ta da sakon mutuwa. Momi ta dafa ta, "Auta tashi mu yi magana ki bar kukan nan haka. Na yarda da kaddara, kada rashin cin jarabawarki yasa ki butulce ma Allah, shi kadai ya san dalilin haka, ki gode ma Shi akan ni'imomin da ya ma ki wanda idan ki ka duba na kasa da ke za ki ga ba su kai ki ba".
  "Hakane Momi kalaman Daddy ne ke sa ni cikin ruɗani amma In Shaa Allah you'll be proud of me".
  Momi ta shafa kan Zainab tare da rungume ta.
  Koda su Labeeba su ka ji zancen rashin cin jarabawar Zainab, sun tausaya ma ta, tare da ba ta baki akan ta yi hakuri da kaddarar da ta same ta.
Hajiya kuwa ko Allah kyauta ba ta ce ba.
  Yaya Habib ma da ya zo bayan faɗan da ta sha wajen shi daga baya ya koma lallashinta.

                ****************
Kwance ta ke akan gado rike da fensiri (pencil) a hannunta, ga wani katon drawing book da Zainab ke ta zane a ciki.
   Habeeba ce ta shigo ɗakin "Auta kina nan ki na ta sana'ar?".
"Ki bari kawai Sis Beeba, hakanan kawai na ji kwanan nan fashion design kawai na ji ina sha'awar yi, ban fa san zan iya zane ba, zanen ma na fashion design".
" Lallai kam ina da talented sister,mu ga zanen?".
  Zainab ta mika ma ta, Habeeba ta buga tsalle "Wow! Auta ke ki ka zana style ɗin wannan rigar?".
Murmushi ta yi "yayi kyau ne?".
"Sosai ma, kin san idan ki ka dage Allah ka dai ya san inda za ki kai, Auta please kar ki daina ki cigaba da yi why not ki faɗa ma Daddy kila ya tallafa ma ki".
"Sis Daddy fushi yake da ni,kin ga ina son siyen fashion sketching tools kuma fa tsada gare su, amma ina da kuɗi hannun Momi, akwai kuɗin snacks da za'a kawo man na bikin gidan Sagir Waziri da nayi".
"Ai ba ki da matsalar kuɗi ma tunda kina sana'arki, da zan iya nima da nayi, ina son a ce na dogara da kaina".
"ba ki sa ma ranki yi bane Sis shiyasa amma ga sana'oi nan da dama da za ki yi kina gida, ke da ma ke zuwa makaranta kullum ko irin takalma ne, hijabai da cosmetics siye za su yi".
"toh ai kuɗin fara sana'ar ce matsala, Hajiya ba ta da shi ba ta ba wani ajiya ba".
"Bari zan ma Momi magana ko Yaya Habib na san za su taimaka tunda kina so".

DOGARO DA KAI Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang